Ba Ka San Inda Zai Yi Albarka Ba!
“Da safe sai ka shuka irinka, da yamma kuma kada ka ja hannunka; gama ba ka san wanda za ya yi albarka ba.”—M. WA. 11:6.
1. Me ya sa ganin yadda tsiro ke girma yake da ban mamaki da kuma sa mu kasance masu tawali’u?
MANOMI yana bukatar ya yi haƙuri. (Yaƙ. 5:7) Bayan ya shuka iri, yana bukatar ya jira don ya tsira kuma ya yi girma. A hankali, idan yanayin yana da kyau, tsiron zai fashe ƙasar ya soma fitowa. Sai ya yi girma ya zama tsiro da ke fitowa. A ƙarshe manomin zai yi girbi. Abin mamaki ne a ga yadda tsiro yake girma! Mu masu tawali’u ne idan muka fahimci Tushen wannan girmar. Za mu iya kula da iri. Za mu iya ba da taimako wajen ba da ruwa. Amma Allah ne kaɗai zai sa ya yi girma.—Ka gwada 1 Korinthiyawa 3:6.
2. Waɗanne darussa ne Yesu ya koyar game da girma ta ruhaniya a kwatanci da aka tattauna a talifin da ya gabata?
2 Kamar yadda aka ambata a talifin da ya gabata, Yesu ya kwatanta aikin wa’azin Mulki da manomi mai shuka iri. A kwatanci na ƙasa dabam dabam, Yesu ya nanata cewa idan manomi ya shuka iri mai kyau, yanayin zuciyar mutumin ne yake nuna ko irin yana girma ko ba ya yi. (Mar. 4:3-9) A kwatancin mai shuki da ya yi barci, Yesu ya nanata cewa manomin bai fahimci yadda mutum yake zama almajiri ba. Saboda da ikon Allah ne mutum yake girma ba don ƙoƙarin ɗan adam ba. (Mar. 4:26-29) Bari yanzu mu ƙara bincika kwatancin Yesu guda uku na ƙwayar mastad, na yisti, da kuma taru.a
Kwatanci na Ƙwayar Mastad
3, 4. Waɗanne fannoni game da saƙon Mulki ne kwatancin ƙwayar mastad yake taƙaita?
3 Kwatanci na ƙwayar mastad da ke rubuce kuma a Markus sura 4, ya nanata abubuwa biyu: na farko, girma na ban mamaki na saƙon Mulki; na biyu, yadda aka kāre waɗanda suka amince da saƙon. Yesu ya ce: “Ƙaƙa za mu kwatanta mulkin Allah? da wane misali kuma za mu misalta shi? Yana kama da ƙwayar mustard; ita kuwa sa’anda aka shibka ta a cikin ƙasa, ko da ta fi kowane irin da ke cikin ƙasa ƙanƙanta, duk da haka sa’anda aka shibka ta ta kan yi girma, ta kan fi dukan ganyaye girma, ta kan miƙa ressa masu-girma; har tsuntsayen sama sun iya sabka ƙalƙashin inuwatata.”—Mar. 4:30-32.
4 A nan an nuna cewa “mulkin Allah” tana girma domin yadda ake yaɗa saƙon Mulki da kuma yadda ikilisiyar Kirista tun daga Fentakos na shekara ta 33 A.Z., take ƙaruwa har yanzu. Ƙwayar mastad wata iri ce ’yar ƙarama da za ta iya wakiltar abu ƙarami sosai. (Ka gwada Luka 17:6.) Amma daga baya, tsiron mastad tana iya kai tsawon ƙafa 10 zuwa 15 kuma ta sami rassa masu ƙwari, har ta zama itace.—Mat. 13:31, 32.
5. Wane girma ne ikilisiyar Kirista na ƙarni na farko ta shaida?
5 Girman ikilisiyar Kirista ya soma da mutane kaɗan a shekara ta 33 K.Z., sa’ad da aka shafa almajirai kusan 120 da ruhu mai tsarki. Amma cikin ɗan lokaci, almajiran da suke cikin wannan ƙaramar ikilisiyar suka zama dubbai. (Ka karanta A. M. 2:41; 4:4; 5:28; 6:7; 12:24; 19:20.) Adadin masu girbi ya ƙaru sosai a cikin shekaru talatin, shi ya sa manzo Bulus ya gaya wa ikilisiya da ke Kolosi cewa an riga an yi wa’azi “cikin dukan halitta da ke ƙarƙashin sama.” (Kol. 1:23) Wannan girma ne sosai!
6, 7. (a) Wace ƙaruwa ce ta faru tun shekara ta 1914? (b) Wace ƙaruwa ce za ta faru?
6 Tun lokacin da aka kafa Mulkin Allah a sama a shekara ta 1914, rassan “itacen” mastad sun faɗaɗa fiye da yadda aka yi tsammani. Mutanen Allah sun ga cikawa ta zahiri na annabcin da Ishaya ya rubuta: “Ƙaramin za ya zama dubu, ƙanƙanin kuma za ya zama al’umma mai-ƙarfi.” (Isha. 60:22) Ƙaramin rukuni na shafaffu da suke aikin Mulki a farkon ƙarni na 20 ba su taɓa tsammani ba cewa a shekara ta 2008 Shaidu kusan miliyan bakwai za su riƙa yin wannan aikin a fiye da ƙasashe 230 ba. Hakika wannan ƙaruwa ce mai ban mamaki, daidai da ƙwayar mastad na kwatancin Yesu!
7 Amma wannan ƙaruwar ta daina ci gaba ne? A’a. Da shigewar lokaci kowane mutum da ke zama a duniya zai zama talakawan Mulkin Allah. Za a cire dukan masu hamayya. Ba ’yan adam ne za su yi wannan ba amma Ubangiji Jehobah Mai Ikon Mallaka ne zai sa hannu a harkokin duniya. (Ka karanta Daniel 2:34, 35.) Sa’annan za mu ga cikawa ta ƙarshe na wani annabci da Ishaya ya rubuta: “Duniya za ta cika da sanin Ubangiji, kamar yadda ruwaye su ke rufe teku.”—Isha. 11:9.
8. (a) Su waye ne tsuntsaye na cikin kwatancin Yesu suke wakilta? (b) Daga menene ake kāre mu a yau?
8 Yesu ya ce tsuntsaye na sama za su sami masauki a ƙarƙashin wannan Mulkin. Waɗannan tsuntsaye ba sa wakiltar magabtan Mulki waɗanda suka yi ƙoƙari su cinye iri masu kyau, kamar yadda tsuntsaye da ke kwatancin mutum wanda ya yafa iri a ƙasa dabam dabam suka yi. (Mar. 4:4) Maimakon haka, a wannan kwatancin tsuntsaye suna wakiltar masu zuciyar kirki da suke neman mafaka a cikin ikilisiyar Kirista. Har yanzu, ana kāre waɗannan daga halaye masu ƙazantarwa a ruhaniya da ayyuka marasa kyau na wannan muguwar duniya. (Gwada da Isha. 32:1, 2.) Hakanan ma, Jehobah ya kwatanta Mulkin Almasihu da itace kuma a cikin annabci ya ce: “A cikin maɗaukakin dutse na Isra’ila zan dasa shi: za ya yi ressa, ya bada ’ya’ya, ya zama kyakyawan cedar: ƙalƙashinsa tsuntsaye na kowane irin fiffike za su zauna; a cikin inuwar ressansa za su zauna.”—Ezek. 17:23.
Kwatancin Yisti
9, 10. (a) Wane darassi ne Yesu ya nanata a kwatanci na yisti? (b) A cikin Littafi Mai Tsarki, sau da yawa menene yisti yake wakilta, amma wace tambaya ce game da yadda Yesu ya yi maganar yisti za mu bincika?
9 Ba koyaushe ba ne ’yan adam suke sanin yadda girma take kasancewa ba. A kwatancin Yesu na gaba, ya nanata wannan batun. Ya ce: “Mulkin sama yana kama da yeast wanda mace ta ɗauka, ta ɓoye cikin mudu uku na gari, har duka ya game da yeast.” (Mat. 13:33) Menene wannan yisti yake wakilta, kuma yaya yake da nasaba da ƙaruwa ta Mulkin?
10 Sau da yawa yisti a cikin Littafi Mai Tsarki yana wakiltan zunubi. Manzo Bulus ya yi nuni ga yisti a wannan hanyar sa’ad da yake maganar tasiri marar kyau na wani mai zunubi a ikilisiyar da ke Koranti na dā. (1 Kor. 5:6-8) Yesu yana amfani da yisti don ya wakilta girman abu marar kyau ne?
11. Ta yaya Isra’ila ta dā take amfani da yisti?
11 Kafin mu amsa wannan tambayar, muna bukatar mu lura da abubuwa uku masu muhimmanci. Na farko ko da Jehobah ya hana amfani da yisti a lokacin Idin Ƙetarewa, a sauran lokatai ya karɓa hadayu masu yisti. Ana amfani da yisti a lokacin yin godiya a hadaya ta salama, mai yin hadayar zai yi hakan da son rai don ya gode wa Jehobah don albarkarsa masu yawa. Wannan abincin zai sa masu cin sa farin ciki.—Lev. 7:11-15.
12. Menene za mu koya daga yadda Littafi Mai Tsarki ya yi amfani da alamu?
12 Na biyu, ko da yake wata alama a wani lokaci tana da ma’ana marar kyau a Nassosi, a wani lokaci ana iya yin amfani da wannan alamar wajen kwatanta abu mai kyau. Alal misali a 1 Bitrus 5:8 an kwatanta Shaiɗan da zaki, don a nuna mugun halinsa na cin zali. Amma a Ru’ya ta Yohanna 5:5 an kwatanta Yesu da zaki, wato, “zaki wanda shi ke na asalin kabilar Yahuda.” Akwai inda aka yi amfani da zaki a matsayin alamar gaba gaɗi.
13. Menene kwatancin Yesu na yisti ya nuna game da girma na ruhaniya?
13 Na uku, a kwatancinsa Yesu bai faɗi cewa yisti ya lalata dukan curin ba, har da ya sa ba za a iya yin amfani da shi ba. Yana maganar yadda ake yin burodi ne kawai. Da gangan ne uwargidan ta daɗa yisti, kuma sakamakon hakan ya yi kyau. An kwaɓa Yisti ɗin da fulawa. Da haka, uwargidan ba ta ga yadda yisti ɗin ya ruɓe ba. Wannan ya tuna mana da mutumin da ya shuka iri kuma ya yi barci daddare. Yesu ya ce “iri kuma ya tsira ya yi girma, shi kuwa [mutumin] ba ya san yadda ya ke yi ba.” (Mar. 4:27) Wannan hanya ce mai sauƙi na kwatanta yadda ba a ganin girma ta ruhaniya! Ba za mu ga girman da farko ba, amma daga baya za mu ga sakamakon.
14. Wane fanni na aikin wa’azi ne yisti da ya sa dukan curin suka ruɓa yake kwatanta?
14 ’Yan adam ba sa ganin wannan girmar kuma hakan na faruwa a dukan duniya. Wannan wani fanni ne da aka nanata a kwatanci na yisti. Yisti ɗin ya ruɓar da dukan curin, dukan “mudu uku na gari.” (Luka 13:21) Kamar yisti, aikin wa’azin Mulki da ya kawo wannan girma na ruhaniya ya yaɗu sosai har yanzu ana wa’azin Mulki “har . . . iyakan duniya.” (A. M. 1:8; Mat. 24:14) Gata ne sosai da yake muna sa hannu a wannan faɗaɗawa na aikin Mulki mai ban mamaki!
Tarun
15, 16. (a) Ka taƙaita kwatancin taru. (b) Menene tarun yake wakilta, kuma wane fanni ne na girman Mulki ne wannan kwatancin yake nuni?
15 Ingancin waɗannan almajiran ya fi muhimmanci da yawan adadin waɗanda suke da’awa su almajiran Yesu Kristi ne. Yesu ya yi maganar wannan fanni na girman Mulkin sa’ad da ya ba da wani kwatanci game da taru. Ya ce: “Kuma, mulkin sama yana kama da tarun da aka jefa cikin teku, ya tattara waɗansu daga kowane irin kifi.”—Mat. 13:47.
16 Taru wanda yake wakilta aikin wa’azin Mulki yana tattara kowane irin kifi. Yesu ya ci gaba da cewa: “Sa’anda [tarun] ya cika kuma suka jawo shi bisa gefe; suka zamna, suka tattara masu-kyau, suka zuba cikin kurtuna, munana kuwa suka yas. Hakanan kuma za ya zama cikin matuƙar zamani: mala’iku za su fito, su rarraba miyagu daga cikin masu adalci. Su jefa su cikin buyar wuta: can za a yi kuka da cizon haƙora.”—Mat. 13:48-50.
17. Wane lokaci ne warewa da aka ambata a kwatancin taru yake nuni?
17 Wannan warewa yana nuni ne ga hukunci na ƙarshe na tumaki da awaki da Yesu ya faɗa za a yi sa’ad da ya dawo cikin ɗaukakarsa? (Mat. 25:31-33) A’a. Za a yi wannan hukunci na ƙarshe sa’ad da Yesu ya bayyana a lokacin ƙunci mai girma. Akasin haka, warewa da aka yi nuninsa a kwatanci na taru zai faru a “matuƙar zamani.”b Wannan lokacin ne da muke ciki yanzu, wato, kwanaki da za su kai ga ƙunci mai girma. Saboda haka, ta yaya ake aikin warewa a yanzu?
18, 19. (a) Ta yaya ake aikin warewa a yanzu? (b) Wane mataki ne dole mutane masu zuciyar kirki su ɗauka? (Ka duba hasiya a shafi na 21.)
18 A zahiri an jawo miliyoyin kifaye na alama daga teku na ’yan adam zuwa ikilisiyar Jehobah a zamanin nan. Wasu sun halarci Tuna Mutuwar Kristi, wasu sun halarci taronmu, kuma har ila wasu suna farin cikin yin nazarin Littafi Mai Tsarki. Amma dukan waɗannan tabbatattun Kiristoci ne kuwa? Ana iya jawo su ‘bisa gefen’ teku amma Yesu ya gaya mana cewa “masu-kyau” ne ake tattara cikin kurtuna, wanda ke wakiltar ikilisiyoyin Kirista. Ana fitar da waɗanda ba su da kyau, daga baya a jefa su cikin tanderun wuta na alama da ke wakiltar halaka a nan gaba.
19 Kamar yadda yake da kifaye da ba su dace ba, mutane da yawa da a dā suna yin nazarin Littafi Mai Tsarki da mutanen Jehobah sun daina yin nazari. Wasu da iyayensu Kiristoci ne ba sa son su zama mabiyan Yesu. Ba sa son su tsai da shawara su bauta wa Jehobah ko kuma idan sun yi hakan na ɗan lokaci sai su daina bauta masa.c (Ezek. 33:32, 33) Amma wajibi ne cewa duk mutane masu zuciyar kirki su yarda a tara su cikin ikilisiyoyi masu kama da kurtuna kafin ranar hukunci na ƙarshe kuma su kasance a wurin mafakan nan.
20, 21. (a) Menene muka koya daga maimaitawar kwatancin Yesu game da girma? (b) Menene ka ƙudurta za ka yi?
20 To, menene muka koya ta wajen maimaita kwatancin Yesu game da girma? Na farko, kamar girman ƙwayar mastad, an samu ƙaruwa sosai ta yin aikin Mulki a nan duniya. Babu abin da zai hana a yaɗa aikin Jehobah! (Isha. 54:17) Ƙari ga haka, an ba wa waɗanda suka nemi mafaka “a ƙarƙashin inuwar [itacen],” kāriya ta ruhaniya. Na biyu, Allah ne ke sa ya yi girma. Kamar yadda aka kwaɓa yisti da fulawa, ba a cika ganin wannan girman, amma hakan yana faruwa! Na uku, ba dukan waɗanda suke saurara ba ne suke nuna sun cancanta. Wasu sun zama kamar kifi da bai dace ba a kwatancin Yesu.
21 Amma, abin ƙarfafa ne a ga mutane da yawa da suka cancanta da Jehobah yake jawowa! (Yoh. 6:44) Hakan ya kawo ƙaruwa mai ban mamaki a ƙasashe da yawa. Jehobah Allah ne za a yaba wa don wannan ƙaruwa. Da ganin haka, ya kamata kowanenmu ya yi biyayya da wannan umurni da aka rubuta ƙarnuka da suka shige: “Da safe sai ka shuka irinka, . . . gama ba ka san wanda za ya yi albarka ba, ko wannan ko wancan, ko kuwa duk za su yi kyau baki ɗaya.”—M. Wa. 11:6.
[Hasiya]
a Bayani da aka yi a gaba gyara ne da aka yi ga abin da aka bayyana a Hasumiyar Tsaro na 15 ga Yuni, 1992, shafuffuka 17-22, da kuma fitowar 1 ga Oktoba, shekara ta 1975, shafuffuka na 589-608 a Turanci.
b Ko da yake Matta 13:39-43 na nuni ga fanni dabam na aikin wa’azin Mulki, lokacin cikawar ya yi daidai da lokacin cikawar kwatancin taru, wato, a “matuƙar zamani.” Warewar kifi na alama yana ci gaba, yadda aikin shuki da girbi yake ci gaba a dukan wannan lokacin.—Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Oktoba, 2000, shafuffuka 25-26 na Turanci; Ka Bauta wa Allah Makaɗaici na Gaskiya, shafuffuka 178-181, sakin layi 8-11.
c Wannan yana nufi ne cewa mala’iku suna ganin kowane mutum da ya daina yin nazari ko kuma tarayya da mutanen Jehobah bai cancanta ba? A’a! Idan mutum da gaske yana so ya dawo wurin Jehobah, za a marabce shi.—Mal. 3:7.
Yaya Za Ka Amsa?
• Menene kwatancin Yesu game da ƙwayar mastad ya koya mana game da girma na Mulkin da kuma kāriya ta ruhaniya?
• Menene yisti na kwatancin Yesu yake wakilta, kuma wace gaskiya ce game da girman Mulki Yesu ya nanata?
• Wane fanni ne na girman Mulki aka nuna a kwatanci na taru?
• Ta yaya za mu tabbata cewa mun kasance cikin waɗanda aka ‘tara cikin kurtuna’?
[Hotuna a shafi na 18]
Menene kwatancin ƙwayar mastad ya koya mana game da yadda aikin Mulki yake ƙaruwa?
[Hoto a shafi na 19]
Menene muka koya daga kwatancin yisti?
[Hoto a shafi na 21]
Menene ake kwatantawa game da warware kifi mai kyau daga marar kyau?