Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w08 4/15 pp. 25-27
  • Suna Ware Amma Ba A Mance Da Su Ba

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Suna Ware Amma Ba A Mance Da Su Ba
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Ƙalubale da Ake Fuskanta a Gidan Tsofaffi
  • Taimako Daga Ikilisiya
  • Mu Ci Gaba da Ziyararsu
  • Ziyararka Yana da Muhimmanci
  • Amfanin Ziyarar
  • Kula Da Tsofaffi Hakki Ne Na Kirista
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
  • Ku Tuna da Waɗanda Suke Gidajen Kula da Tsofaffi
    Hidimarmu Ta Mulki—2014
  • Allah Yana Kula da Tsofaffi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Jehobah Yana Kula Da Bayinsa Tsofaffi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
w08 4/15 pp. 25-27

Suna Ware Amma Ba A Mance Da Su Ba

MANZO Bulus ya aririce mabiyansa Kiristoci: “Bari mu aika nagarta zuwa ga dukan mutane, tun ba waɗanda su ke cikin iyalin imani.” (Gal. 6:10) A yau, muna bin wannan hurarriyar shawara kuma muna neman hanyoyin da za mu yi wa ’yan’uwanmu masu bi alheri. A cikin waɗanda suke bukatar kulawa a cikin ikilisiyar Kirista sune tsofaffin ’yan’uwa maza da mata da suke zama a gidan tsofaffi.

Hakika, a wasu ƙasashe, al’ada ce iyalai su kula da iyayensu tsofaffi a gida. Amma, a wasu ƙasashe kuma, ana ajiye tsofaffi a gidan tsofaffi ne inda ake kula da su. Kiristoci tsofaffi da suke zama a gidan tsofaffi kuma fa? Wane ƙalubale ne suke fuskanta? Yaya za su iya jimrewa idan ba sa samun taimako daga iyalinsu? Yaya ne ikilisiyar Kirista za ta iya taimaka musu? Kuma ta yaya za mu amfana idan muka ziyarce su a kai a kai?

Ƙalubale da Ake Fuskanta a Gidan Tsofaffi

Sa’ad da tsofaffi Kirista suka ƙaura zuwa gidan tsofaffi, sai su kasance a yankin wata ikilisiya dabam. A sakamakon haka, Shaidu da suke yankin ba za su yi tunanin ziyartar su kai a kai ba. Ƙari ga haka, a gidan tsofaffi, mai yiwuwa za su kasance a tsakanin mutane masu imani dabam dabam. Wataƙila hakan zai saka Shaidu tsofaffi cikin yanayi mai wuya.

Alal misali, a wasu wurare, gidan tsofaffi sukan shirya a yi sujada ta addinai. Wani mai kula da tsofaffi ya ce: “An kai wasu Shaidu tsofaffi da ba su iya magana ba sosai zuwa sujada a coci, ba tare da an tambaye su ko sun amince ba.” Bugu da ƙari, ma’aikatan gidan tsofaffi suna canja yanayin daƙin a ranar bikin haihuwarsu, ranar Kirsimati, ko kuma ranar Easter. Ana kuma ba wa wasu Shaidu abincin da lamirinsu ya hana su ci. (A. M. 15:29) Idan muka ziyarci ’yan’uwanmu tsofaffi maza da mata a kai a kai, za mu iya taimakonsu su magance waɗannan ƙalubalan.

Taimako Daga Ikilisiya

Kiristoci na farko suna sane da hakkinsu na kula da tsofaffi da ba su da iyalan da za su kula da su. (1 Tim. 5:9) Hakazalika, dattawa a yau suna ƙoƙari su ga cewa ba a ƙyale tsofaffi da suke zama a gidan tsofaffi a yankinsu ba.a Robert Wani dattijo ya ce: “Zai yi kyau idan dattawa Kiristoci suka ziyarci tsofaffi don su ga lafiyarsu kuma su yi addu’a tare da su. Ikilisiyar ta yi ƙoƙari a wajen kula da bukatunsu.” Idan muka keɓe lokaci don mu ziyarci tsofaffi, za mu nuna cewa mun fahimci yadda kula da waɗanda suke neman taimako yake da muhimmancin a wurin Jehobah.—Yaƙ. 1:27.

Idan ya wajaba, dattawan su taimaki ’yan’uwansu da suke gidan tsofaffi da ke yankinsu. Robert ya faɗi abin da ya kamata mu yi: “Ya kamata mu ƙarfafa tsofaffi ’yan’uwa maza da mata su halarci taron Kirista idan za su iya.” Amma, dattawa su yi wasu shirye-shirye don waɗanda ba za su iya zuwa Majami’ar Mulki ba. Jacqueline, wata ’yar’uwa ’yar shekara 85 mai ciwon osteoarthritis, tana saurarar jawabi a taro ta wayar tarho. Ta ce: “Ina amfana sosai idan na saurari taro a lokacin da ake yin ta. Ina son in saurari jawabi a taro ko da menene ya faro.”

Idan wani tsoho Kirista ba zai iya saurarar taro ta wayar tarho ba, dattawa za su iya shirya a yi masa tanadinsa a kaset. Ɗan’uwan da zai kai wa ɗan’uwan ko ’yar’uwar kaset ɗin a gidan tsofaffi ya yi amfani da wannan zarafin ya ƙarfafa shi ko ita. Wani dattijo ya ce: “Idan aka gaya musu abubuwa game da ’yan’uwa na cikin ikilisiya zai sa tsofaffin sun san cewa suna cikin iyalin ’yan’uwan na cikin ikilisiya.”

Mu Ci Gaba da Ziyararsu

Babu shakka, tsofaffin da yawa ba sa farin ciki idan suka koma gidan tsofaffi. A sakamakon haka, wasu ba za su so yin magana da mutane ba. Amma, idan muka ziyarci ’yan’uwanmu tsofaffi maza da mata bayan sun koma gidan tsofaffi kuma muka ci gaba da ƙarfafa su, hakan zai sa su yi farin ciki.—Mis. 17:22.

Idan ’yan’uwa tsofaffi maza ko mata suka fita a hankalinsu ko kuma ba sa iya ji sosai ko kuma suna da wasu matsaloli da suka sa sadawa da su yake da wuya, wasu za su iya kammala cewa ziyararsu ba shi da amfani. Amma, ƙoƙarin da muke yi na ziyararsu, duk da cewa sadawa da su yana da wuya, zai nuna cewa muna ci gaba da ‘gabatarda ’yan’uwanmu cikin bangirma.’ (Rom. 12:10) Idan ɗan’uwa tsoho ya soma yawan mantuwa, za mu iya ƙarfafa shi ya gaya mana wasu abubuwa da suka faru a dā ko kuma ya gaya mana yadda ya koyi gaskiyar Littafi Mai Tsarki. Me za mu iya yi idan yana ƙoƙari ya tuna wata kalma? Ya kamata ka saurara da kyau, kuma idan zai yiwu ka ambata kalamai guda biyu ko uku da wataƙila yake so ya tuna, ko kuma ka sake faɗin abubuwan da ya faɗa sannan ka ƙarfafa shi ya ci gaba. Idan ya ɗimauce kuma yana da wuya mu fahimci abin da yake faɗi, za mu yi ƙoƙari mu fahimci abin da yake nufi idan muka saurari muryarsa.

Idan magana ba za ta yiwu ba, za a iya amfani da wasu hanyoyin sadarwa. Laurence, wata majagaba, a kai a kai tana ziyartar Madeleine, wata tsohuwa Kirista mai shekara 80 wadda ba ta iya magana kuma. Laurence ta bayana yadda take sadawa da ita: “Ina riƙe hannun Madeleine sa’ad da muke addu’a tare. Sai ta matse hannu na kuma ta ƙibta idanunta don ta nuna godiyarta ga wannan lokaci mai tamani.” Riƙe hannun tsofaffi ko kuma rungumar su zai sa su farin ciki.

Ziyararka Yana da Muhimmanci

Ziyararka a kai a kai zuwa wajen tsofaffi zai iya sa a rika kula da su da kyau. Danièle, wadda take ziyartar ’yan’uwa Shaidu a gidan tsofaffi na shekaru 20 ta ce: “Idan ma’aikatan gidan tsofaffin suka ga cewa ana ziyartar ɗaya daga cikin tsofaffin a kai a kai, za su kula da shi ko ita sosai.” Robert, da aka ambata a gaba, ya ce: “Ma’aikatan gidan tsofaffin suna saurarar wanda yake ziyartar wurin a kai a kai. Wataƙila ba za su nuna irin wannan daraja ga wanda ba ya zuwa a kai a kai ba.” Tun da ma’aikan gidan tsofaffin suna sha’ani da wasu iyalai masu matsi, suna jin daɗi idan baƙi suka nuna godiyarsu. Bugu da ƙari, idan muka ƙafa dangantaka mai kyau da ma’aikatan gidan tsofaffin zai sa su daraja imanin Shaidu tsofaffi da suke kula da su.

Za mu iya ƙafa dangantaka da ma’aikatan gidan tsofaffi ta wajen taimaka musu a wasu ƙanana ayyuka. A wasu wurare saboda karancin ma’aikatan gidan tsofaffi, ba sa samun kulawa sosai. Rébecca, wata ma’aikaciyar asibiti ta ce: “Lokacin ba wa tsofaffi abinci yana da wuya. Wannan zai iya kasancewa lokaci ne mai kyau na ziyartar aboki kuma a taimake shi ya ci abinci.” Ka da mu yi jinkirin tambayar ma’aikatan yadda za mu iya taimaka musu.

Sa’ad da muka ziyarci gidan tsofaffin a kai a kai, za mu ga wuraren da ’yan’uwanmu maza da mata suke bukatar taimako kuma da izinin ma’aikatan za mu iya taimaka musu. Alal misali, za mu iya gyara ɗakin tsofaffin da hotunan waɗanda suke ƙauna ko kuma zane-zane da yara suka yi. Idan muka san bukatunsu, za mu iya kawo musu rigar barci ko kuma man shafawa da sabulu. Idan gidan tsofaffin yana da wajen shan iska, muna iya kai abokanmu waje su sha iska. Laurence, wadda aka ambata a gaba ta ce: “Madeleine tana jirar ranar da zan zo ziyara. Sa’ad da na zo da yaro, sai ta yi murmushi kuma fuskanta ya yi haske.” Yin irin waɗannan abubuwa yana da muhimmanci ga tsofaffi da suke zama a gidan tsofaffi.—Mis. 3:27.

Amfanin Ziyarar

Ziyartar tsoho a kai a kai zai iya gwada ‘sahihancin ƙaunarmu.’ (2 Kor. 8:8) A wace hanya? Abin baƙin ciki ne mu ga abokinmu yana raunana. Laurence ta ce: “Da farko, yanayin madeleine ya dame ni sosai har ya sa bayan kowane ziyarar da na yi sai na yi kuka. Amma na fahimci cewa addu’a za ta iya taimakonmu mu kame zuciyarmu kuma mu ƙarfafa waɗanda muke ziyara.” Robert ya yi shekaru da yawa yana ziyartar wani ɗan’uwa Kirista mai suna Larry wanda yake fama da ciwon Parkinson. Robert ya ce: “Cutar ta ci Larry sosai har ta sa ba na iya fahimtar abin da yake faɗi. Amma sa’ad da muka yi addu’a tare, ina ganin bangaskiyarsa.”

Sa’ad da muka ziyarci tsofaffi masu bi, za mu taimake su kuma mu amfana. Ƙudurinsu na yin kusa da Jehobah sa’ad da suke zama a tsakanin mutane masu imani dabam ya koya mana mu kasance da bangaskiya kuma mu nuna ƙarfin zuciya. Yadda suke ɗokin saurarar abinci na ruhaniya duk da irin matsalar da suke ciki ya nuna cewa “Ba da abinci kaɗai ba mutum za ya rayu, amma da kowace magana da ke fitowa daga bakin Allah.” (Mat. 4:4) Yadda tsofaffi suke farin cikin da abubuwa kalilan, kamar murmushin yara, da kuma cin abinci tare da su yana koya mana cewa ya kamata mu gamsu da abin da muke da shi. Ƙaunar da suke nuna wa abubuwa na ruhaniya zai iya taimakonmu mu riƙe makasudai masu kyau.

Hakika, dukan ikilisiya suna amfana daga taimako da muke yi wa tsofaffi. A wace hanya ce ikilisiya take amfana? Tun da yake waɗanda ba su da ƙarfin jiki suna dogara ga ’yan’uwa, hakan yana ba wa ikilisiyar zarafi na ci gaba da nuna ƙauna. Saboda haka, ya kamata kowannenmu ya ɗauki kula da tsofaffi, har na dogon lokaci, sashen hidimarmu ce ga juna. (1 Bit. 4:10, 11) Idan dattawa suka kasance na farko a wannan aikin, za su taimaki ’yan ikilisiyar su fahimci cewa ya kamata mu ɗauki wannan irin aiki na Kirista da muhimmanci. (Ezek. 34:15, 16) Idan muka ba da goyon baya ga wannan aiki, za mu nuna wa ’yan’uwanmu tsofaffi cewa ba mu mance da su ba.

[Hasiya]

a Sa’ad da sakatare na ikilisiya ya ji cewa wani ɗan’uwa ko ’yar’uwa ya ko ta koma gidan tsofaffi a wani yankin, zai dace nan da nan ya sanar da dattawan ikilisiyar da ke yankin.

[Bayanin da ke shafi na 27]

“Sa’ad da ma’aikatan gidan tsofaffi suka ga cewa ana ziyartar ɗaya daga cikin tsofaffin a kai a kai, za su kula da shi ko ita sosai”

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba