Magidanta Ku Yi Koyi Da Shugabancin Kristi
“Kan kowane namiji Kristi ne.”—1 KORINTHIYAWA 11:3.
1, 2. (a) Ta yaya ne za a gwada nasarar maigida? (b) Me ya sa yake da muhimmanci a fahimci cewa Allah ne ya ƙafa aure?
TA YAYA za ka gwada nasarar maigida? Ta iliminsa ko kuwa ta iyawarsa? Ko ta yadda yake samun kuɗi ne? Ko kuwa musamman ta yadda yake bi da matarsa da ’ya’yansa? Idan muka lura da yadda magidanta suke bi da iyalansu za mu ga cewa yawancinsu ba sa yin abin da ya kamata su yi, domin sun ƙyale mizanan ’yan adam da ruhun duniya su rinjaye su. Me ya sa? Musamman saboda sun kasa yin koyi kuma ba sa yin amfani da umurnin wanda ya ƙafa aure wato wanda ya ‘ɗauki haƙarƙari daga cikin mutumin, ya maishe shi mace, ya kawo ta wurin mutumin.’—Farawa 2:21-24.
2 Yesu Kristi ya tabbatar da abin da littafi Mai Tsarki ya ce game da yadda Allah ya ƙafa aure, sa’ad da ya gaya wa ’yan sūka na zamaninsa cewa: “Ba ku karanta ba, shi wanda ya yi su tun farko, namiji da tamata ya yi su, har ya ce, Saboda wannan namiji za ya bar ubansa da uwatasa shi manne ma matatasa; su biyu kuwa za su zama nama ɗaya? Ya zama fa daga nan gaba su ba biyu ba ne, amma nama ɗaya ne. Abin da Allah ya gama fa [a aure], kada mutum shi raba.” (Matta 19:4-6) Hakika, ainihin dalilin yin nasara a aure shi ne idan aka fahimci cewa Allah ne ya ƙafa aure kuma aka bi umurnin da ke cikin Kalmarsa, Littafi Mai Tsarki.
Abin da Zai Sa Maigida Ya Yi Nasara
3, 4. (a) Menene ya sa Yesu yake da fahimi game da aure? (b) Wacece matar Yesu na alama, kuma ta yaya ne ya kamata magidanta su bi da matansu?
3 Ainihi abin da zai sa maigida ya yi nasara shi ne yin nazarin abin da Yesu ya ce kuma ya bi gurbinsa. Yesu yana da ilimi sosai game da aure, saboda yana wurin sa’ad da aka halicci mutane biyu na fari da kuma sa’ad da aka ɗaura masu aure. Jehobah Allah ya ce masa: ‘Bari mu yi mutum a cikin surarmu, bisa ga kamaninmu.’ (Farawa 1:26) Hakika, Allah yana magana ne da wanda ya halitta kafin kowa da kuma komi wanda yake “wurinsa gwanin mai-aiki.” (Misalai 8:22-30) Wannan shi ne ‘ɗan fari gaban dukan halitta.’ Shi ne “farkon halittar Allah,” wanda ya kasance kafin halittar sararin samaniya.—Kolossiyawa 1:15; Ru’ya ta Yohanna 3:14.
4 Ana kiran Yesu “Ɗan rago na Allah,” kuma a alamance ana kiransa maigida. Wani mala’ika ya taɓa cewa: “Ka zo daganan, ni nuna maka amarya, matar Ɗan Ragon.” (Yohanna 1:29; Ru’ya ta Yohanna 21:9) Wacece wannan amaryar, ko kuma matar? “Matar Ɗan Ragon” su ne mabiyan Yesu amintattu shafaffu na ruhu, waɗanda za su yi sarauta ta samaniya tare da shi. (Ru’ya ta Yohanna 14:1, 3) Saboda haka, yadda Yesu ya bi da almajiransa sa’ad da yake duniya ya koya wa magidanta yadda za su bi da matansu.
5. Yesu zai zama gurbi ga su wanene?
5 Hakika, Littafi Mai Tsarki ya faɗi cewa Yesu abin koyi ne ga mabiyansa, ya ce: “Kristi kuma ya sha azaba dominku, yana bar maku gurbi, domin ku bi sawunsa.” (1 Bitrus 2:21) Amma, shi gurbi ne musamman ga maza. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kan kowane namiji Kristi ne; kan mace kuma namiji ne; kan Kristi kuma Allah ne.” (1 Korinthiyawa 11:3) Tun da Yesu ne kan namiji, ya kamata magidanta su yi koyi da misalinsa. Kuma dole ne a yi amfani da ƙa’ida game da shugabanci idan iyalin za ta yi nasara kuma ta yi farin ciki. Saboda haka, ya kamata magidanta su bi da matansu cikin ƙauna kamar yadda Yesu ya bi da matarsa na alama, wato almajiransa shafaffu.
Yadda Za a Bi da Matsaloli na Aure
6. Ta yaya ya kamata magidanta su bi da matansa?
6 A duniya yau ta wahala, magidanta suna bukatar su yi koyi da misalin Yesu game da haƙuri, ƙauna da kuma ɗaukaka ƙa’idodi masu adalci. (2 Timothawus 3:1-5) Game da gurbin da Yesu ya bari, Littafi Mai Tsarki ya ce: “Hakanan kuma ku mazaje, ku zauna da matayenku bisa ga sani.” (1 Bitrus 3:7) Hakika, magidanta suna bukatar su bi da matsaloli na aure da fahimi, kamar yadda Yesu ya bi da matsaloli. Ya fuskanci gwaji mai tsanani fiye da kowane ɗan adam, amma ya fahimci cewa Shaiɗan da aljanunsa da kuma muguwar duniyar nan ne suka sa yake fuskantar wannan gwaji. (Yohanna 14:30; Afisawa 6:12) Yesu bai taɓa yin mamakin gwajin da yake fuskanta ba, saboda haka, bai kamata ma’aurata su yi mamaki ba sa’ad da suke fuskantar “wahala a cikin jiki.” Littafi Mai Tsarki ya yi gargaɗi cewa waɗanda suka yi aure za su fuskanci irin wannan wahala.—1 Korinthiyawa 7:28.
7, 8. (a) Menene zama da mata cikin sani ya ƙunsa? (b) Me ya sa ya kamata a girmama mata?
7 Littafi Mai Tsarki ya ce magidanta su bi da matansu ‘bisa ga sani, suna bada girma ga mace, kamar ga wadda ta fi rashin ƙarfi.’ (1 Bitrus 3:7) Maimakon ya mallaki matarsa, kamar yadda Littafi Mai Tsarki ya annabta cewa maza za su yi, mijin da yake son Allah ya amince da shi zai girmama matarsa. (Farawa 3:16) Zai bi da ita kamar dukiya mai tamani, ba zai so ya buge ta ba. Maimakon haka, zai yi la’akari da yadda take ji, zai bi da ita cikin daraja.
8 Me ya sa ya kamata maza su girmama matansu? Littafi Mai Tsarki ya amsa: Tun da ku “masu-tarayyan gado na alherin rai [ne da su]: domin kada addu’o’inku su hanu.” (1 Bitrus 3:7) Ya kamata magidanta su fahimci cewa Jehobah ba ya ɗaukan cewa maza da suke bauta masa sun fi mata daraja. Matan da Allah ya amince da su za su samu ladan rai madawwami daidai da maza, yawancin mata za su mori rayuwa a sama, inda “ba na miji ko ta mata.” (Galatiyawa 3:28) Saboda haka, ya kamata maza su riƙa tunawa cewa amincin mutum ne zai sa ya kasance da tamani a wurin Allah. Ba lallai sai mutum namiji ne, ko tamace, ko maigida ko mata ko kuwa yaro ba.— 1 Korinthiyawa 4:2.
9. (a) In ji Bitrus wane dalili ne ya sa ya kamata maza su girmama matansu? (b) Ta yaya ne Yesu ya girmama mata?
9 Manzo Bitrus ya nanata muhimmancin maza su girmama matansu a ƙarshen kalmominsa, ya ce, “domin kada addu’oinku su hanu.” Irin wannan hani zai iya kasancewa da haɗari! Hakan kuma zai iya sa kada a saurari addu’o’in maigida, kamar yadda ya faru da bayin Allah a dā waɗanda suka ƙi bin sa. (Makoki 3:43, 44) Ya kamata Kiristoci masu aure da waɗanda suke shirin aure su yi la’akari da yadda Yesu ya bi da mata cikin mutunci. Suna cikin waɗanda suke zuwa hidima tare da shi, kuma ya bi da su cikin alheri da kuma daraja. A wani lokaci, Yesu ya bayyana wa mata ne da farko gaskiya mai muhimmanci, ya ce su gaya wa maza.—Matta 28:1, 8-10; Luka 8:1-3.
Fitaccen Misali ga Magidanta
10, 11. (a) Me ya sa magidanta musamman suke bukatar su yi la’akari da misalin Yesu? (b) Ta yaya ne magidanta za su nuna wa matansu ƙauna?
10 Kamar yadda muka lura da farko, Littafi Mai Tsarki ya kwatanta dangantakar maigida da matarsa da ta Yesu da ‘amaryarsa,’ wadda ita ce ikilisiya ta mabiyansa shafaffu. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Miji kan mata ya ke, kamar yadda Kristi kuma kan ikilisiya ne.” (Afisawa 5:23) Ya kamata waɗannan kalmomi su ƙarfafa maigida ya bincika irin shugabanci da Yesu ya koya wa mabiyansa. Ta wurin yin irin wannan binciken ne kawai magidanta za su iya bin misalin Yesu kuma su yi wa matansu ja-gora, su ƙaunace su, kuma su kula da su kamar yadda Yesu ya bi da ikilisiyarsa.
11 Littafi Mai Tsarki ya aririce Kiristoci, “Ku mazaje, ku ƙaunaci matanku, kamar yadda Kristi kuma ya ƙaunaci ikilisiya, ya bada kansa dominta.” (Afisawa 5:25) A littafin Afisawa, an kira ‘ikilisiyar’ “jikin Kristi.” Wannan jiki na alama ya ƙunshi maza da mata, waɗanda suke sa jikin ya yi aiki da kyau. Hakika, Yesu “shi ne kai na jiki, watau ikilisiya.”—Afisawa 4:12; Kolossiyawa 1:18; 1 Korinthiyawa 12:12, 13, 27.
12. Ta yaya ne Yesu ya nuna yana ƙaunar jikinsa na alama?
12 Yesu ya nuna wa jikinsa na alama ƙauna, wato “ikilisiya,” musamman yadda ya kula da waɗanda za su kasance a cikin ikilisiyar. Alal misali sa’ad da almajiransa suka gaji, ya ce masu: “Ku zo . . . waje ɗaya inda ba kowa, ku huta kaɗan.” (Markus 6:31) Da yake kwatanta ayyukan Yesu kafin a kashe shi, ɗaya daga cikin almajiransa ya ce: ‘Yesu ya yi ƙaunar nasa [wato waɗanda suke cikin jikinsa na alama] . . . , ya ƙaunace su har matuƙa.’ (Yohanna 13:1) Wannan misali ne mai kyau da Yesu ya nuna game da yadda magidanta za su bi da matansu!
13. Ta yaya ne aka aririce magidanta su ƙaunaci matansu?
13 Manzo Bulus ya ci gaba da yin amfani da misalin da Yesu ya kafa wa magidanta, ya aririce magidanta: “Ya kamata mazaje kuma su yi ƙaunar matayensu kamar jikunansu. Wanda ya ke ƙaunar matatasa kansa ya ke ƙauna: gama babu mutum wanda ya taɓa ƙin jiki nasa; amma ya kan ciyadda shi ya kan kiyaye shi, kamar yadda Kristi kuma ya kan yi da ikilisiya.” Ya kuma daɗa: “Duk da haka sai ku kuma kowane ɗayanku shi yi ƙaunar matatasa kamar kansa; matan kuma ta ga kwarjinin mijinta.”—Afisawa 5:28, 29, 33.
14. Ta yaya ne maigida yake bi da jikinsa na zahiri, kuma menene wannan ya koya masa game da yadda ya kamata ya bi da matarsa?
14 Ka yi tunanin kalmomin Bulus. Mutum wanda yake da hankali zai yi wa kansa rauni da gangan ne? Idan mutum ya yi tuntuɓe, zai bugi yatsunsa ne domin sun sa ya yi tuntuɓe? A’a! Maigida yana wulakanta kansa a gaban abokansa ko kuma ya faɗi kasawarsa ne? A’a! To me ya sa zai yi wa matarsa baƙar magana ko kuwa ya buge ta idan ta yi kuskure? Ya kamata magidanta su kula da bukatunsu da kuma na matansu.—1 Korinthiyawa 10:24; 13:5.
15. (a) Menene Yesu ya yi sa’ad da almajiransa suka nuna kasawa? (b) Waɗanne darussa ne za a iya koya daga wannan misali?
15 Ka yi la’akari da yadda Yesu ya kula da almajiransa a daren da zai mutu, sa’ad da suka nuna kasawa. Ko da yake ya ci gaba da gaya musu su yi addu’a, sun yi barci sau uku a lambun Jathsaimani. Farat ɗaya, sojoji suka kewaye su. Yesu ya tambayi mutanen: “Wa kuke nema?” Suka ce: “Yesu na Nazarat,” ya amsa: “Ni ne.” Domin ya san cewa ‘lokacin mutuwarsa ya yi,’ ya ce: “Idan fa ni kuke neman ku bar waɗannan su tafi.” A koyaushe, Yesu yana kula da lafiyar almajiransa, wato jikinsa na alama kuma ya yi masu hanya su gudu. Idan magidanta suka yi la’akari da yadda Yesu ya bi da almajiransa, za su sami ƙa’idodi da yawa da za su iya amfani da su game da yadda za su bi da matansu.—Yohanna 18:1-9; Markus 14:34-37, 41.
Ƙauna Ta Yesu ba Sha’awa ba Ce
16. Yaya ne Yesu ya ji game da Martha, kuma ta yaya ne ya yi mata gyara?
16 Littafi Mai Tsarki ya ce: “Yesu dai yana ƙaunar Martha da ’yar’uwatta, da kuma Li’azaru,” waɗanda sau da yawa suna karɓansa a gidansu. (Yohanna 11:5) Duk da haka, Yesu ya gargaɗi Martha sa’ad da ta mai da hankali ainun ga shirya abinci, wanda haka ya sa ba ta samu isashen lokacin sauraransa ba. Ya ce: “Martha, Martha, kin damu, kina wahala kuma a kan abu dayawa. Amma bukata ɗaya ce.” (Luka 10:41, 42) Babu shakka, saboda irin ƙaunar da yake wa Martha ne ya sa ta karɓi shawararsa da sauƙi. Hakazalika, ya kamata magidanta su bi da matansu cikin ƙauna, su yi musu kirki, kuma kada su yi musu baƙar magana. Duk da haka, sa’ad da ake bukatar gyara, yana da kyau a yi shi kamar yadda Yesu ya yi.
17, 18. (a) Yaya ne Bitrus ya tsauta wa Yesu, kuma me ya sa ya dace a yi wa Bitrus gyara? (b) Wane hakki ne magidanta suke da shi?
17 A wani lokaci, Yesu ya bayyana wa almajiransa cewa dole ne ya tafi Urushalima, inda zai sha wahala daga hannun “datibai da manyan malamai da marubuta, a kashe shi, rana ta uku kuma ya tashi.” Sai Bitrus ya keɓe Yesu waje ɗaya ya fara tsauta masa yana cewa: “Allah shi sawaƙa maka, Ubangiji, wannan ba za ya same ka ba daɗai.” Babu shakka, Bitrus ya aikata bisa ga motsin rai. Hakika yana bukatar gyara. Sai Yesu ya ce masa: “Ka koma bayana, Shaiɗan: abin tuntuɓe ka ke a gareni; gama ba ka yi tattalin abin da ke na Allah ba, sai na mutane.”—Matta 16:21-23.
18 Yesu ya ambata abin da Allah yake so ya yi, wato zai sha wahala sosai kuma a kashe shi. (Zabura 16:10; Ishaya 53:12) Saboda haka, Bitrus ya yi kuskure da ya tsauta wa Yesu. Hakika, Bitrus yana bukatar gyara sosai, kamar yadda muke bukata a yi mana gyara wani lokaci. Da yake shi ne shugaban iyali, maigida yana da iko da kuma hakkin gyara iyalinsa tare da matarsa. Ko da yake ana bukatar a yi gyara sosai, ya kamata a yi hakan da ƙauna. Kamar yadda Yesu ya taimaki Bitrus ya gyara tunaninsa, a wani lokaci ya kamata magidanta su taimaki matansu su gyara ra’ayinsu. Alal misali, ya kamata maigida ya yi wa matarsa gyara a hankali idan kwalliyarta bai yi daidai ba da abin da Nassosi suka ce.—1 Bitrus 3:3-5.
Yana da Muhimmanci Magidanta Su Kasance Masu Haƙuri
19, 20. (a) Wace matsala ce ta taso tsakanin manzannin Yesu, kuma yaya ne Yesu ya yi gyara? (b) Yesu ya yi nasara ne?
19 Idan akwai wani kasawa da ya kamata a gyara, bai kamata magidanta su yi tsammanin cewa ƙoƙarin da suke yi don gyara zai yi nasara nan da nan ba. Yesu ya ci gaba da ƙoƙari sosai kafin ya gyara halin manzaninsa. Alal misali, sun yi jayayya kuma a tsakaninsu a ƙarshen hidimar Yesu. Sun yi gardama a tsakaninsu a kan wanene babba. (Markus 9:33-37; 10:35-45) Ba da daɗewa ba bayan da suka yi gardama na biyu, Yesu ya shirya ya yi bikinsa na Ƙetare tare da su kawai. A wannan lokacin, ba wani cikinsu da ya tashi ya yi aiki mafi ƙanƙanta na wanke ƙurar da ke ƙafafun sauran kamar yadda ake yi a zamaninsu. Amma Yesu ya yi hakan. Sai ya ce: “Na yi muku kwatanci.”—Yohanna 13:2-15.
20 Magidanta da suke da tawali’u kamar Yesu za su samu haɗin kai da kuma taimako daga matansu. Amma wannan yana bukatar su zama masu haƙuri. Daga baya a daren Ƙetarewa, manzannin sun yi gardama kuma a kan ko wanene babba a cikinsu. (Luka 22:24) Yakan ɗauki lokaci kafin mutum ya canja halinsa. Duk da haka, abin farin ciki ne idan aka yi nasara kamar yadda ya kasance a tsakanin manzannin Yesu!
21. Sa’ad da suka fuskanci kalubale a yau, menene ya kamata magidanta su tuna kuma su yi?
21 A yau, aure yana fuskantar kalubale fiye da dā. Mutane da yawa ba sa ɗaukan alkawarin aure da muhimmanci. Saboda haka, ya kamata magidanta su yi bimbini game da tushen aure. Su tuna cewa aure daga Allah ne, kuma shi ne ya kafa ta. Ya ba da Ɗansa, Yesu, ya zama Mai Fansarmu, da Mai Cetonmu, kuma ya zama misali ga magidanta.—Matta 20:28; Yohanna 3:29;1 Bitrus 2:21.
Yaya Za Ka Amsa?
• Me ya sa yake da muhimmanci mu fahimci tushen aure?
• Ta yaya ne aka ƙarfafa magidanta su yi ƙaunar matansu?
• Waɗanne misalai ne game da yadda Yesu ya bi da almajiransa ya nuna yadda ya kamata magidanta su bi shugabanci na Kristi?
[Hoto a shafi na 8]
Me ya sa ya kamata magidanta su bi misalin Yesu a yadda ya bi da mata?
[Hoto a shafi na 9]
Yesu ya nuna yana kula da almajiransa sa’ad da suka gaji
[Hoto a shafi na 10]
Magidanta su yi wa matansu gargaɗi cikin ƙauna, da kuma kalamai da suka dace