DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | MATTA 18-19
Ka Guji Sa Kanka da Kuma Wasu Yin Tuntuɓe
Yesu ya ba da misalai da yawa don ya nuna cewa sa kanmu ko kuma wasu tuntuɓe ba ƙaramin abu ba ne.
Sa mutum “tuntuɓe” yana nufin yin wasu abubuwan da za su sa shi ya yi abin da bai kamata ba ko kuma ya yi zunubi
Gwamma a rataye wa mutum babban dutse a wuyansa kuma a jefa shi cikin teku da ya sa wani tuntuɓe
Babban dutse
Yesu ya gaya wa mabiyansa su yanke hannunsu ko kuma cire idanunsu idan suna sa su tuntuɓe
Gwamma mutum ya rabu da waɗannan abubuwan kuma ya shiga Mulkin Allah, da ya zama da su kuma a halaka shi gabaki ɗaya
Mene ne nake yi da zai iya sa wasu tuntuɓe, kuma ta yaya zan guji sa kaina da kuma wasu yin tuntuɓe?