WAƘA TA 94
Muna Godiya Jehobah Don Kalmarka
Hoto
(Filibiyawa 2:16)
1. Jehobah Ubanmu, mun zo gabanka,
Mu yi maka godiya don Kalmarka!
Nassosin da ka ba mu
ne sun ’yantar da mu,
Sun haska hanyarmu, sun wayar da mu.
2. Maganar Jehobah tana da iko,
Tana gyara tunanin zuciyarmu.
Duk ƙa’idodin Allah
masu adalci ne,
Suna amfanar mu a ayyukanmu.
3. Maganarka Allah na ratsa zuci.
Annabawanka sun nuna aminci.
Ka taimake mu Allah,
mu yi koyi da su.
Mun gode ma sosai domin Kalmarka!
(Ka kuma duba Zab. 19:9; 119:16, 162; 2 Tim. 3:16; Yaƙ. 5:17; 2 Bit. 1:21.)