WAƘA TA 94
Muna Godiya Jehobah Don Kalmarka
Hoto
	(Filibiyawa 2:16)
- 1. Jehobah Ubanmu, mun zo gabanka, - Mu yi maka godiya don Kalmarka! - Nassosin da ka ba mu - ne sun ’yantar da mu, - Sun haska hanyarmu, sun wayar da mu. 
- 2. Maganar Jehobah tana da iko, - Tana gyara tunanin zuciyarmu. - Duk ƙa’idodin Allah - masu adalci ne, - Suna amfanar mu a ayyukanmu. 
- 3. Maganarka Allah na ratsa zuci. - Annabawanka sun nuna aminci. - Ka taimake mu Allah, - mu yi koyi da su. - Mun gode ma sosai domin Kalmarka! 
(Ka kuma duba Zab. 19:9; 119:16, 162; 2 Tim. 3:16; Yaƙ. 5:17; 2 Bit. 1:21.)