ABIN DA KE SHAFIN FARKO: ZA KA IYA YIN RAYUWA MAI MA’ANA
Zai Yiwu A Yi Rayuwa Mai Ma’ana Kuwa?
‘Tsawon kwanakin ranmu duka aƙalla shekara saba’in ne, in kuwa muna da ƙarfi, shekara tamanin ne. Duk da haka iyakar abin da waɗannan shekaru suke kawo mana, damuwa ce da wahala.’—Zabura 90:10, Littafi Mai Tsarki.
WANNAN maganar gaskiya ce, ko ba haka ba? Rayuwa a duniyar nan tana cike da ‘damuwa da wahala.’ Wataƙila ka taɓa yin tunani, ‘Zai yiwu a yi rayuwa mai ma’ana kuwa yanzu?’
Ka yi la’akari da misalin Maria. A dā ita mai ƙwazo ce sosai, amma yanzu da shekarunta suka kai 84, ta naƙasa kuma ba ta fita daga cikin gida. Ko da yake tana cikin hankalinta, amma ba ta da ƙarfi kamar dā. Ta yaya za ta yarda cewa rayuwa tana da ma’ana?
Kai kuma fa? Wataƙila ka taɓa yin tunani ko rayuwarka tana da ma’ana. Yana yiwuwa cewa aikin da kake yi kullum mai gundura ne kuma mai gajiyarwa. Wataƙila mutane ba sa gani ko kula da ƙoƙarin da kake yi. Ko da kana jin daɗin rayuwa yanzu, wataƙila kana damuwa a kan abin da zai faru a nan gaba. A wasu lokatai kana iya jin kaɗaici ko kuma ka yi baƙin ciki. Wataƙila babu kwanciyar hankali a cikin gidanku. Ko kuma ka taɓa yin rashin wani da kake ƙauna. Wani mutum mai suna André ya shaƙu da mahaifinsa sosai, amma farat ɗaya sai mahaifin ya kamu da wata muguwar cuta kuma ya mutu. André ya yi baƙin ciki sosai kuma yana ganin ba abin da zai iya magance wannan baƙin cikin da yake ji.
Ko da wace irin matsala ce muke ciki, tambayar da za mu so mu san amsarta ita ce: Za a iya yin rayuwa mai ma’ana kuwa? Za mu sami amsar wannan tambayar idan muka bincika rayuwar wani mutum da ya wanzu wajen shekaru 2,000 da suka shige, wato, Yesu Kristi. Duk da matsalolin da ya fuskanta, Yesu ya yi rayuwa mai ma’ana sosai. Mu ma za mu iya yin rayuwa mai ma’ana idan muka bi misalinsa.