Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w12 10/1 p. 27
  • Jehobah Ya Ƙi Jinin Rashin Adalci

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Jehobah Ya Ƙi Jinin Rashin Adalci
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Makamantan Littattafai
  • Darussa Daga Littafin Ezekiel Na Ɗaya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • Yadda Jehobah Yake Taimaka Mana Mu Yi Nasara a Hidimarmu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2022
  • ‘Al’ummai Za Su Sakankance Ni Ne Jehobah’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Darussa Daga Littafin Ezekiel na Biyu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
w12 10/1 p. 27

Ka Kusaci Allah

Jehobah Ya Ƙi Jinin Rashin Adalci

“WAƊANSU sukan sami mulki, waɗansu kuwa su sha wuya a ƙarƙashinsu.” (Mai-Wa’azi 8:9, Littafi Mai Tsarki) Wannan kalamin da aka rubuta shekaru 3,000 da suka shige, sun kwatanta sak yadda rayuwa take a zamaninmu. ’Yan Adam suna amfani da ikon da suka samu a hanyar da ba ta dace ba. Sau da yawa suna cin zalin marasa ƙarfi da kuma talaka. Yaya Jehobah yake ji game da irin wannan rashin adalci? Za mu samu amsar a Ezekiyel 22:6, 7, 31.—Ka karanta.

Jehobah ya bayyana dalla-dalla a Dokar da ya ba wa Isra’ila cewa kada masu iko su wulaƙanta waɗanda suke ƙarƙashin su. Ya ce zai albarkaci al’ummar ne idan shugabanninta sun nuna alheri da kuma adalci wa matalauta da gajiyayyu. (Kubawar Shari’a 27:19; 28:15, 45) Amma, a zamanin Ezekiyel, hakiman Urushalima da Yahuda sun zalunci mutane sosai. Ta yaya suka yi hakan?

Hakiman suna ‘zub da jini, kowa . . . iyakacin [ikonsa, LMT].’ (Aya ta 6) Wani juyin Littafi Mai Tsarki ya bayyana cewa: “Shugabannin Isra’ila . . . sun yi amfani da ikonsu don zub da jini.” Yaya za a samu adalci tun da shugabanni masu iko, waɗanda ya kamata su nuna adalci, suna wulaƙanta mutane har ma suna kisan talakawa?

Bayan Ezekiyel ya furta wannan, sai ya tuhume shugabannin da suka karya Dokar Jehobah da kuma waɗanda suke koyi da su. Ya ce: “An maida uba da uwa ba wani abu ba.” (Aya ta 7) Ta wajen rena iyayensu, mutanen sun gurɓata iyali wanda yake shi ne tushen al’umma.—Fitowa 20:12.

Azzaluman sun cuci matalautan da ke cikinsu. Duk lokacin da suka yi rashin biyayya, suna nuna cewa sun rena kyakkyawan dalilin da ya sa Allah ya ba su Dokar. Alal misali, Dokar da Allah ya ba wa Isra’ilawa ta umurce su su riƙa nuna alheri wa bare da ke zama a ƙasarsu. (Fitowa 22:21; 23:9; Levitikus 19:33, 34) Amma sai mutanen suka riƙa yi wa ‘baƙi wulakanci.’—Aya ta 7.

Ƙari ga haka, mutanen sun wulaƙanta gajiyayyu da ke cikinsu, wato, “marayu da gwamraye.” (Aya ta 7) Jehobah ya damu sosai da waɗanda suka yi rashin iyayensu ko matarsu ko kuma mijinsu. Allah ya yi alkawari cewa zai hukunta waɗanda suka wulaƙanta maraya ko kuwa gwauruwa.—Fitowa 22:22-24.

Sa’ad da Isra’ilawan zamanin Ezekiyel suka aikata waɗannan abubuwan, sun nuna cewa sun rena Dokar da Allah ya ba su saboda ƙaunar da yake yi musu. Shin mene ne Jehobah zai yi? Ya ƙudura: “Na zuba musu hushina.” (Aya ta 31) Jehobah ya ƙyale Babiloniyawa su halaka Urushalima kuma su kai mutanen da ke cikinta bauta a shekara ta 607 kafin zamanin Kristi.

Daga waɗannan kalmomin Ezekiyel, mun koyi darussa guda biyu a kan yadda Jehobah yake ji game da rashin adalci: Na farko, Jehobah ya ƙi jinin rashin adalci; na biyu, yana tausaya wa waɗanda aka nuna musu rashin adalci. Allah bai canja ba. (Malakai 3:6) Ya yi alkawari cewa zai kawar da rashin adalci da kuma waɗanda suke hadassa shi. (Misalai 2:21, 22) Ya kamata ka ƙara sanin wannan Allah mai “son shari’a” kuma ka fahimci abin da za ka yi don ka kusace shi, ko ba haka ba?—Zabura 37:28.

[Bayanin da ke shafi na 27]

Jehobah ya bayyana dalla-dalla cewa kada masu iko su wulaƙanta waɗanda suke ƙarƙashin su

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba