Abin da Na Koya Daga Littafi Mai Tsarki
’YAN SHEKARA 3 ZUWA ƘASA
Kaleb ya ji labari cewa abokinsa bai da lafiya.
Sai ya ce: “Na san matakin da Zan ɗauka.
Zan rubuta masa wasiƙa don ya samu ƙarfafa, sa’an nan zan kai masa ziyara!”
Ka yi alheri, sa’an nan kai da abokinka za ku yi farin ciki! 1 Bitrus 3:8
UMURNI GA IYAYE
Ka sa yaronka ya nuna hoton:
Gida Teburi Kaleb
Rana Tsuntsu Itace
Ka ambaci sunan wani da yake rashin lafiya, kuma ka gaya wa yaronka abin da za ku iya yi don ku ƙarfafa shi.