Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w12 10/1 pp. 30-31
  • Haɗama Ta Sa Gehazi Ya Ɓata Dangantakarsa da Allah

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Haɗama Ta Sa Gehazi Ya Ɓata Dangantakarsa da Allah
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Makamantan Littattafai
  • Yarinya Ta Taimaki Jarumi
    Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki
  • Ta So Ta Yi Taimako
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Ya Yi Taurin Kai Amma Daga Baya Ya Yi Biyayya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Dawaki da Karusan Wuta na Jehobah
    Darussa daga Littafi Mai Tsarki
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
w12 10/1 pp. 30-31

Ku Koyar Da Yaranku

Haɗama Ta Sa Gehazi Ya Ɓata Dangantakarsa da Allah

KA TAƁA yin sha’awar wani abu sosai?—a Idan ka taɓa yi, to ba laifi ba ne. Amma ya kamata ka yi ƙarya don ka samu abin da kake so?— A’a bai kamata ba. Duk wanda ya yi hakan mai haɗama ne. Akwai wani mutum mai suna Gehazi da ya yi haɗama. Bari mu ga yadda wannan halin ya ɓata shi. Gehazi yana yi wa annabin Jehobah mai suna Elisha hidima.

Elisha da Gehazi sun yi zamaninsu wajen shekara dubu kafin a haifi Yesu Ɗan Allah a duniya. Jehobah ya sa Elisha ya yi abubuwa masu ban al’ajabi. Alal misali, Littafi Mai Tsarki ya ba da labarin wani shugaban sojoji a ƙasar Suriya mai ciwon kuturta. Ba wanda ya iya ya warkar da shi, amma Elisha ya warkar da shi.

Allah ya ba Elisha iko saboda ya warkar da mutane kuma sa’ad da ya yi hakan, ba ya karɓan kuɗi. Ka san abin da ya sa?— Domin Elisha ya san cewa waɗannan abubuwan al’ajabin da yake yi ba da ikonsa ba amma daga Allah ne. Na’aman ya yi farin ciki sosai sa’ad da aka warkar da shi kuma ya so ya ba wa Elisha kyautar azurfa da zinariya da tufafi masu kyau. Elisha ya ƙi ya karɓa waɗannan abubuwan amma Gehazi yana so a ba shi waɗannan kayan.

Bayan Na’aman ya kama hanyar koma gida, Gehazi ya soma bin sa ba tare da ya gaya wa Elisha ba. Sa’ad da ya sami Na’aman, ka san abin da ya gaya masa?— ‘Elisha ya aiko ni in gaya maka cewa ya yi baƙi guda biyu. Yana son ka ba shi riguna biyu ya ba wa baƙin.’

Labarin nan cewa maigidansa Elisha ya yi baƙi ba gaskiya ba ne! Yana so a ba shi rigunan nan da Elisha ya ƙi karɓa ne. Amma Na’aman bai san cewa ƙarya yake yi ba. Saboda haka, ya ba shi waɗannan kayan da farin ciki. Kuma ya ba shi fiye da yadda yake bukata. Ka san abin da ya faru bayan haka?—

Sa’ad da Gehazi ya koma gida, sai Elisha ya tambaye shi: “Daga ina ka fito Gehazi?”

Gehazi ya amsa: ‘Ai ban je ko’ina ba.’ Amma Jehobah ya bayyana wa Elisha abin da Gehazi ya yi. Saboda haka, Elisha ya gaya masa: ‘Yanzu ba lokacin karɓan kuɗi da riguna ba ne.’

Bai kamata Gehazi ya karɓi kuɗi da rigunan nan ba don ba a yi niyyar ba shi ba. Don wannan abin da ya yi, sai Allah ya sa kuturta da ta kama Na’aman ta koma kan Gehazi. Wane darasi ne kana gani za mu koya daga wannan labarin?— Wani abu da muka koya shi ne bai kamata mu riƙa yin ƙarya ba.

Me ya sa Gehazi ya yi ƙarya?— Don shi mai haɗama ne. Kwaɗayi ya sa shi ya yi ƙarya don ya samu abubuwan da yake so. Saboda haka, ya kamu ta mugun cuta har ya mutu.

Ƙari ga haka, Gehazi ya rasa wani abu mai muhimmanci sosai. Ka san ko mene ne abin?— Dangantakarsa da Allah. Kada mu taɓa yin wani abu ya ɓata dangantakarmu da Jehobah! A maimakon haka, mu kasance masu alheri kuma mu riƙa yi wa mutane kyauta.

Ka karanta wuraren nan a cikin naka Littafi Mai Tsarki

2 Sarakuna 5:5, 20-27; Yahuda 21

Yohanna 15:10

[Hasiya]

a Idan kana karatun da yaro ne, wannan alamar fid da ma’ana (—) tana nufin ka ba wa yaron dama don ya faɗi ra’ayinsa.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba