Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • km 3/10 p. 4
  • Abin da Za a Ce Game da Mujallun

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Abin da Za a Ce Game da Mujallun
  • Hidimarmu Ta Mulki—2010
  • Makamantan Littattafai
  • Abin da Za a Ce Game da Mujallun
    Hidimarmu Ta Mulki—2011
  • Abin da Za a Ce Game da Mujallun
    Hidimarmu Ta Mulki—2010
  • Abin da Za a Ce Game da Mujallun
    Hidimarmu Ta Mulki—2010
  • Abin da Za a Ce Game da Mujallun
    Hidimarmu Ta Mulki—2010
Dubi Ƙari
Hidimarmu Ta Mulki—2010
km 3/10 p. 4

Abin da Za a Ce Game da Mujallun

Janairu-Maris

“Mutane da yawa sun gaskata cewa dukan masu adalci suna zuwa sama. Kana tsammanin cewa nufin Allah kenan? [Ka bari ya ba da amsa. Sai ka karanta Zabura 37:29.] Wannan mujallar za ta taimaka maka ka fahimci cewa ba dukan adalai ba ne suke zuwa sama.” Ka gabatar da talifin da ya soma daga shafi na 12.

Maris

“Mutane da yawa suna daraja Littafi Mai Tsarki amma suna tunanin cewa ba shi da wani amfani sosai a zamaninmu. Menene ra’ayinka? [Ka bari ya ba da amsa. Sai ka karanta Romawa 15:4.] Wannan talifin ya bayyana dalilin da ya sa har sashen da suka daɗe a cikin Littafi Mai Tsarki har ila suke da amfani.” Ka gabatar da talifin da ya soma a shafi na 28.

Afrilu-Yuni

“Idan an gaya wa mutane su ambata mutum da ya fi shafan tarihi, mutane da yawa suna zaɓar Yesu. Shi kai ma ka zaɓa? [Ka bari ya ba da amsa.] Ka lura da dalilin da ya sa ya kamata mu yi bincike sosai game da labarai da yawa game da shi kuma mu san gaskiya. [Karanta Yohanna 17:3.] Wannan talifi na musamman na Hasumiyar Tsaro ya nuna ainihi abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da Yesu da koyarwarsa.”

Afrilu

“Kamar dai ba mu da isashen lokaci na cim ma dukan abubuwan da muke so mu yi. Ko ba haka ba ne? [Ka bari ya ba da amsa.] Mutane da yawa sun ga cewa wannan shawarar tana da amfani. [Ka karanta Filibiyawa 1:10.] Wannan mujallar ta ba da wasu shawarwari masu amfani da za su taimaka mana mu yi amfani da lokacinmu yadda ya kamata.”

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba