Za a Soma Kamfen na Gayyatar Mutane Zuwa Taron Tuna Rasuwar Yesu a Ranar 17 ga Maris
1. Wane kamfen ne za a soma a ranar 17 ga Maris?
1 Ta wurin Tuna Rasuwar Yesu a kowacce shekara, muna shelar rasuwarsa. (1 Kor. 11:26) Saboda haka, muna son mutane su halarci taron tuna rasuwar tare da mu don su saurari jawabi game da kyauta ta fansa da Jehobah ya ba da don ƙaunar da yake yi mana. (Yoh. 3:16) Za a soma kamfen na gayyatar mutane zuwa taron Tuna Rasuwar Yesu a ranar Asabar, 17 ga Maris na wannan shekara. Shin kana ɗokin yin iya ƙoƙarinka a lokacin kamfen ɗin?
2. Mene ne za mu iya faɗa sa’ad da muke gayyatar mutane?
2 Abin da Za Mu Faɗa: Zai fi kyau mu taƙaita abin da za mu ce. Muna iya cewa: “Barka dai. Muna gayyatar kai da iyalinka zuwa wani taro mai muhimmanci da ake yi shekara-shekara da za a yi a dukan duniya a ranar 5 ga Afrilu. Za a ba da jawabi daga Littafi Mai Tsarki da zai bayyana abin da rasuwar Yesu ta cim ma da kuma abin da Yesu yake yi a yanzu. Wannan takardar gayyata tana ɗauke da adireshi da kuma lokacin da za a yi taron a yankinmu.” Sa’ad da muke rarraba takardar gayyatar a ƙarshen mako, za mu iya ba da mujallu a lokacin da ya dace.
3. Ta yaya za mu iya gayyatar mutane da yawa?
3 Ka Gayyaci Mutane da Yawa: Muna son mu gayyaci mutane da yawa. Saboda haka, ku tabbata cewa kun gayyaci waɗanda kuke nazarin Littafi Mai Tsarki da su da waɗanda kuke koma ziyara wurinsu da danginku da abokan aikinku da abokan makarantarku da maƙwabtanku da kuma sauran mutane. Dattawan ikilisiyarku za su ba da ja-gora ga yadda za ku gayyaci mutane a dukan yankinku. Ana samun sakamako mai kyau daga kamfen na gayyatar mutane zuwa taron Tuna Rasuwar Yesu da muke yi a kowacce shekara. A shekarar da ta shige, sa’ad da wata mata ta shigo inda ake taron, sai wani ɗan atenda ya ce bari ya je ya kira mai shelar da ya gayyace ta. Amma matar ta ce wani ne da yake wa’azi gida zuwa gida ne ya ba ta takardar gayyatar, kuma ba ta san kowa a wajen ba.
4. Waɗanne dalilai ne muke da su na nuna ƙwazo a lokacin kamfen na rarrabar takardar gayyata?
4 Wataƙila wani zai zo taron Tuna Rasuwar Yesu don takardar gayyata da ka ba shi. Ko wani ya saurare ka ko a’a, har ila ƙoƙarce-ƙoƙarcenka ya zama shaida a gare shi. Takardar gayyata da ka ba da za ta sanar cewa Yesu Sarki ne da ke sarauta yanzu. Ƙwazonka a lokacin wannan kamfen zai nuna wa waɗanda suke yankinku da ’yan’uwa da kuma musamman Jehobah cewa kana godiya don kyauta ta fansa da ya yi mana.—Kol. 3:15.