Gabatarwa
Don Soma Nazarin Littafi Mai Tsarki a Asabar ta Farko a Watan Yuli
“Baftisma wani abu ne da yawancin Kiristoci suke yi. Kana ganin yin baftisma yana da muhimmanci ne? [Ka bari ya amsa.] Wannan talifin ya tattauna wasu muhimman batutuwa game da hakan.” Ka ba wa mai-gidan Hasumiyar Tsaro na Yuli-Satumba, bayan haka sai ku tattauna ƙaramin jigon da ke shafi na 14 tare kuma ka karanta aƙalla nassi guda. Ka ba shi mujallun kuma ka gaya masa za ka dawo don ku tattauna tambayar da ke gaba.
Hasumiyar Tsaro Yuli-Satumba
Akwai coci da ɗarikoki masu yawa da suka yi imani da abubuwa dabam-dabam. Kana ganin cewa su duka ne Kiristoci na gaskiya? [Ka bari ya amsa.] In ji Yesu, ga alama guda da za ta sa a san Kiristoci na gaskiya. [Karanta Yohanna 13:34, 35.] Wannan mujallar ta tattauna furuci guda biyar da Yesu ya yi waɗanda za su taimaka mana mu san mabiyansa na gaskiya.
Awake! Yuli
“Idan kana da ikon canja wani abu a duniya, wanne ne za ka canja? [Ka bari ya amsa.] Littafi Mai Tsarki ya nuna dalilin da ya sa ’yan Adam suke da iyaƙa a abubuwan da za su iya cim ma. [Karanta Irmiya 10:23.] Wannan mujallar ta bayyana abubuwan da Allah zai canja.”