Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • mwb17 Disamba p. 7
  • Mece ce Kauna ta Gaskiya?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Mece ce Kauna ta Gaskiya?
  • Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2017
  • Makamantan Littattafai
  • Ku Kāre Aurenku
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2021
  • Abin da Littafi Mai Tsarki Ya Ce Game da Aure da Rashin Aure.
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Kuna Bincika JW.ORG/HA don Samun Shawarwari na Yau da Kullum?
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2022
  • Aure Dangantaka Ce da Ake Yi Muddin Rai
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2022
Dubi Ƙari
Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2017
mwb17 Disamba p. 7

RAYUWAR KIRISTA

Mece ce Ƙauna ta Gaskiya?

Jehobah ya shirya aure ne don mata da miji su kasance tare har abada. (Fa 2:​22-24) Zina ce kaɗai za ta iya sa ma’aurata su kashe aurensu. (Mal 2:16; Mt 19:9) Tun da Jehobah yana so ma’aurata su riƙa jin daɗin aurensu, shi ya sa ya yi tanadin ƙa’idodin da za su taimaka wa Kiristoci su zaɓi aboki ko abokiyar aure nagari kuma su ji daɗin aurensu.​—M. Wa 5:​4-6.

KU KALLI BIDIYON NAN MECE CE ƘAUNA TA GASKIYA?, SAI KU AMSA TAMBAYOYIN NAN:

  • Frank yana magana da ’yarsa Liz

    Ta yaya shawarar da Frank da Bonnie suka ba ʼyarsu ta nuna cewa suna da hikima kuma suna ƙaunarta?

  • Me ya sa bai dace mu yi tunanin cewa za mu iya canja halin mutumin da muke so mu aura ba?

  • Wace shawara mai kyau ce Paul da Priscilla suka ba Liz?

  • Zach da Megan a taro

    Me ya sa Zach da Megan suka sami matsala a aurensu?

  • Liz da John a taro

    Waɗanne maƙasudai ne John da Liz suke da shi?

  • Me ya sa ya kamata ka san “ɓoyayyen mutum na zuciya,” wato halin mutum kafin ka yi wa’adin aure? (1Bi 3:4)

  • Mece ce ƙauna ta gaskiya? (1Ko 13:​4-8)

A ina ne Kiristoci za su iya samun ƙarin bayanai game da fita zance?

  • Bidiyon da ke Tashar JW mai jigo Preparing for Marriage

  • Bidiyon JW.ORG mai jigo Soyayya ta Gaskiya Ce ko ta Ƙarya?

  • Questions Young People Ask​—Answers That Work Littafi Na 1 da 2

  • Littafin Bincike Don Shaidun Jehobah (Ka duba “Rayuwar Iyali,” sai ka duba “Fita Zance da Neman Aure.”)

A ina ne ma’aurata za su iya samun shawara mai kyau?

  • Talifofin JW.ORG (Ka duba ƙarƙashin KOYARWAR LITTAFI MAI TSARKI > TAIMAKO DON IYALI.)

  • Ƙasidar Yadda Iyalinku Za Ta Zauna Lafiya

  • Littafin Asirin Farinciki Na Iyali

  • Littafin Bincike Don Shaidun Jehobah (Ka shiga “Rayuwar Iyali,” sai ka duba “Aure.”)

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba