25 ga Yuni–1 ga Yuli
LUKA 4-5
Waƙa ta 37 da Addu’a
Gabatarwar Taro (minti 3 ko ƙasa da hakan)
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
“Kamar Yesu, Ka Guji Faɗawa Cikin Jarraba”: (minti 10)
Lu 4:1-4—Yesu bai bar sha’awar jiki ta fi ƙarfinsa ba (w13 8/15 25 sakin layi na 8)
Lu 4:5-8—Yesu bai bar abin da ya gani da idonsa ya janye hankalinsa ba (w13 8/15 25 sakin layi na 10)
Lu 4:9-12—Yesu bai yi amfani da ikonsa don ya burge mutane ba [Ka saka bidiyon nan Saman Haikali.] (nwtsty hotuna da bidiyo; w13 8/15 26 sakin layi na 12)
Neman Abubuwa Masu Tamani: (minti 8)
Lu 4:17—Me ya nuna cewa Yesu ya san Kalmar Allah sosai? (nwtsty na nazari)
Lu 4:25—A zamanin Iliya, shekara nawa ne aka yi babu ruwan sama? (nwtsty na nanzari)
Mene ne karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon ya koya maka game da Jehobah?
Waɗanne darussa ne kuma ka koya a karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon?
Karatun Littafi Mai Tsarki: (minti 4 ko ƙasa da hakan) Lu 4:31-44
KA YI WA’AZI DA ƘWAZO
Komawa Ziyara ta Biyu: (minti 3 ko ƙasa da hakan) Ka fara da bin bayanin da ke yadda za mu yi wa’azi. Bayan haka, ka ba wa maigidan katin JW.
Komawa Ziyara ta Uku: (minti 3 ko ƙasa da hakan) Ka zaɓi nassin da za ka yi amfani da shi kuma ka ba shi ɗaya daga cikin littattafan da muke amfani da su don nazari.
Nazarin Littafi Mai Tsarki: (minti 6 ko ƙasa da hakan) jl darasi na 28
RAYUWAR KIRISTA
“Ka Guji Haɗarin da Ke Dandalin Sada Zumunta Na Intane”: (minti 15) Tattaunawa. Ka saka bidiyon nan Ka Zama Mai Hikima a Dandalin Zumunta na Intane.
Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya: (minti 30) lv babi na 9 sakin layi na 13-21 da akwatin da ke shafi na 104
Bita da Abin da Za A Tattauna Mako Mai Zuwa (minti 3)
Waƙa ta 105 da Addu’a