Asabar
“Ku yi zamanku . . . ba tare da wani abin zargi ko tabo ba. Ku yi zama a gabansa da salama”—2 Bitrus 3:14
Da Safe
9:20 Sauti da Bidiyo
9:30 Waƙa ta 58 da Addu’a
9:40 JERIN JAWABAI: Ku Yi “Shirin Kai Labari Mai Daɗi na Salama”
• Ku Ci Gaba da Yin Ƙwazo (Romawa 1:14, 15)
• Ku Shirya Abin da Za Ku Faɗa (2 Timoti 2:15)
• Ku Yi Amfani da Kowane Zarafi (Yohanna 4:6, 7, 9, 25, 26)
• Ku Koma Wurin Masu Son Saƙon (1 Korintiyawa 3:6)
• Ku Taimaki Ɗalibanku Su Manyanta (Ibraniyawa 6:1)
10:40 Matasa—Ku Zaɓi Rayuwar da Za Ta Ba Ku Kwanciyar Hankali! (Matiyu 6:33; Luka 7:35; Yakub 1:4)
11:00 Waƙa ta 135 da Sanarwa
11:10 BIDIYO: Yadda ꞌYanꞌuwanmu Suke More Salama Duk da . . .
• Tsanantawa
• Rashin Lafiya
• Talauci
• Balaꞌi
11:45 JAWABIN BAFTISMA: Ku Ci Gaba da Bin “Hanyar Salama” (Luka 1:79; 2 Korintiyawa 4:16-18; 13:11)
12:15 Waƙa ta 54 da Shaƙatawa
Da Rana
1:35 Sauti da Bidiyo
1:45 Waƙa ta 29
1:50 JERIN JAWABAI: “Ku Yar da” Duk Abin da Ke Ɓata Zaman Salama
• Yawan Takama (Afisawa 4:22; 1 Korintiyawa 4:7)
• Kishi (Filibiyawa 2:3, 4)
• Rashin Gaskiya (Afisawa 4:25)
• Gulma (Karin Magana 15:28)
• Yawan Fushi (Yakub 1:19)
2:45 WASAN KWAIKWAYO DAGA LITTAFI MAI TSARKI: Jehobah Yana Bi da Mu ta Hanyar Salama—Kashi na 1 (Ishaya 48:17, 18)
3:15 Waƙa ta 130 da Sanarwa
3:25 JERIN JAWABAI: Ku ‘Nemi Salama da Dukan Zuciyarku’ . . .
• Ta Wurin Guje wa Saurin Fushi (Karin Magana 19:11; Mai-Wa’azi 7:9; 1 Bitrus 3:11)
• Ta Wurin Neman Gafara (Matiyu 5:23, 24; Ayyukan Manzanni 23:3-5)
• Ta Wurin Saurin Gafartawa (Kolosiyawa 3:13)
• Ta Wurin Faɗan Alheri (Karin Magana 12:18; 18:21)
4:15 Ku Kiyaye Haɗin Kanmu da Salamarmu! (Afisawa 4:1-6)
4:50 Waƙa ta 113 da Addu’ar Rufewa