Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w01 11/1 pp. 25-30
  • ‘Ku Yafa Wa Kanku Tsawon Jimrewa’

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • ‘Ku Yafa Wa Kanku Tsawon Jimrewa’
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Misalin Kristi na Tsawon Jimrewa
  • ’Yar Ruhu
  • “Ƙauna Tana da Yawan Haƙuri”
  • Tsawon Jimrewa Yana Taimakonmu Mu Jimre
  • Ku Yafa Tsawon Jimrewa
  • “Ku Yi Haƙuri da Kowa”
  • Jehovah Allah Ne Mai Tsawon Jimrewa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Za Ka Ci Gaba Da Yin “Tafiya Bisa Ga Ruhu”?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • Kana Barin Ruhun Allah Ya Yi Maka Ja-gora Kuwa?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Abin da Muka Koya Daga Ƙyale Mugunta da Allah Ya Yi
    Ka Bauta wa Allah Maƙadaici na Gaskiya
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
w01 11/1 pp. 25-30

‘Ku Yafa Wa Kanku Tsawon Jimrewa’

“Ku yafa zuciya ta tausayi . . . jimrewa.”—KOLOSSIYAWA 3:12.

1. Ka faɗi nagarin misali na tsawon jimrewa.

RÉGIS, wanda yake da zama a kudu maso yamma na Faransa, ya zama Mashaidin Jehovah da ya yi baftisma a shekara ta 1952. Shekaru da yawa, matarsa ta yi iyakacin ƙoƙarinta ta hana shi bauta wa Jehovah. Ta yi ƙoƙari ta huɗa tayar motarsa don ta hana shi halartan taro, har a wani lokaci ta bi shi ƙofa ƙofa tana masa gwalo yayin da yake wa mutane wa’azin saƙon Littafi Mai Tsarki na bisharar Mulkin. Duk da wannan hamayya ta kullum, Régis ya ci gaba da tsawon jimrewa. Saboda haka, Régis nagarin misali ne ga dukan Kiristoci, tun da yake Jehovah yana bukatar dukan masu bauta masa su kasance da tsawon jimrewa a sha’aninsu da wasu.

2. Menene ma’ana ta zahiri ta kalmar Helenanci na “tsawon jimrewa,” kuma menene kalmar take nufi?

2 Kalmar Helenanci ta “tsawon jimrewa” a zahiri tana nufin “dogon ruhu.” New World Translation na Turanci ya yi amfani da kalmar nan “tsawon jimrewa” sau goma, “haƙuri” sau uku, “yin haƙuri” kuma sau ɗaya. Furcin Ibrananci da na Helenanci da aka fassara “tsawon jimrewa” ya haɗa da ra’ayin haƙuri, daurewa, jinkirin fushi.

3. Yaya ra’ayin Kirista game da tsawon jimrewa ya bambanta daga na Helenanci na ƙarni na farko?

3 Helenawa na ƙarni na farko ba sa ɗaukan tsawon jimrewa cewa kirki ne. ’Yan falsafa Stoic kansu ba su taɓa amfani da kalmar ba. In ji manazarin Littafi Mai Tsarki William Barclay, tsawon jimrewa “akasin kirki ne na Helenanci,” wanda ke “ƙin yarda da wani cin mutunci ko lahani.” Ya ce: “Ga Helenawa mutum mai girma, mutum ne da ya fita neman ramako ko da menene ne. Ga Kirista kuma mutum mai girma shi ne mutumin da ko idan ya iya ma, zai ƙi yin haka.” Ƙila Helenawa suna ɗaukar tsawon jimrewa cewa alamar kumamanci ce, amma a nan yadda yake a wasu fasaloli, “wautar Allah ta fi mutane hikima; rashin ƙarfin Allah kuma ya fi mutane ƙarfi.”—1 Korinthiyawa 1:25.

Misalin Kristi na Tsawon Jimrewa

4, 5. Wane misali na ban mamaki na tsawon jimrewa ne Yesu ya yi tanadinsa?

4 Bayan Jehovah sai shi, Kristi Yesu ya bar misali mai kyau na tsawon jimrewa. Yayin da yake cikin matsi mai tsanani, Yesu ya nuna kame kai na ban mamaki. An annabta game da shi: “Aka wulakance shi, duk da haka ya yi tawali’u, ba ya buɗe bakinsa ba; kamar ɗan rago da a ke kai wurin yanka, kamar yadda tunkiya wurin masu-sosayanta tana shuru; hakanan ba ya buɗe bakinsa ba.”—Ishaya 53:7.

5 Lalle Yesu ya nuna tsawon jimrewa ne mai girma a duk hidimarsa a duniya! Ya jimre ga miyagun tambayoyin magabtansa da kuma ashar daga waɗanda suke hamayya da shi. (Matta 22:15-46; 1 Bitrus 2:23) Ya yi haƙuri da almajiransa, har ma yayin da suke jayayya sau da yawa game da ko wa zai zama babba. (Markus 9:33-37; 10:35-45; Luka 22:24-27) Lalle kuwa kamewa ce ta ban sha’awa Yesu ya nuna a daren da aka tsare shi, sa’ad da barci ya kwashi Bitrus da Yohanna bayan da ya gaya musu su “yi tsaro”!—Matta 26:36-41.

6. Yaya ne Bulus ya amfana daga tsawon jimrewa na Yesu, kuma me muka koya daga wannan?

6 Bayan mutuwarsa da tashiwa, Yesu ya ci gaba da tsawon jimrewa. Manzo Bulus ya yi la’akari da wannan musamman, tun da yake dā shi mai tsananta wa Kiristoci ne. Bulus ya rubuta: “Batun nan amintace ne, ya isa kowa shi karɓa, cewa, Kristi Yesu ya zo cikin duniya domin ceton masu-zunubi; cikinsu kuwa ni ne babba: duk da haka na sami jinƙai dalilin wannan domin ta wurina, ni da ke babba, Yesu Kristi shi bayyana tsawon haƙurinsa duka, domin gurbi ga waɗannan da za su bada gaskiya gareshi gaban nan zuwa rai na har abada.” (1 Timothawus 1:15, 16) Ko menene muka yi dā, idan muka sa bangaskiyarmu cikin Yesu, zai kasance da tsawon jimrewa da mu—yayin nan kuma, ya tsammanci mu yi “ayyuka da sun cancanta tuba.” (Ayukan Manzanni 26:20; Romawa 2:4) Saƙonni da Kristi ya aika wa ikilisiyoyi bakwai a Asiya Ƙarama ya nuna cewa ko da yana tsawon jimrewa, ya bukaci a yi gyara.—Ru’ya ta Yohanna, surori 2 da 3.

’Yar Ruhu

7. Menene dangantaka tsakanin tsawon jimrewa da ruhu mai tsarki?

7 A cikin sura ta biyar ta wasiƙarsa ga Galatiyawa, Bulus ya saɓa ayyukan jiki da ’ya’yan ruhu. (Galatiyawa 5:19-23) Tun da yake tsawon jimrewa ɗaya ne cikin halayen Jehovah, wannan halin ya fito daga wurinsa kuma ’yar ruhunsa ne. (Fitowa 34:6, 7) Hakika, an jera tsawon jimrewa na huɗu cikin kwatancin Bulus game da ’ya’yan ruhu tare da “ƙauna . . . farinciki, salama, . . . nasiha, nagarta, aminci, tawali’u, kamewa.” (Galatiyawa 5:22, 23) Saboda haka, idan bayin Allah suka nuna haƙuri na ibada, ko tsawon jimrewa, suna yin haka ne a ƙarƙashin ikon ruhu mai tsarki.

8. Menene zai taimake mu kasancewa da ’ya’yan ruhu, haɗe da tsawon jimrewa?

8 Amma, wannan ba ya nufin cewa Jehovah yana tilasta wa mutum ruhunsa ba. Dole ne mu bi ikon ruhun da yardan rai. (2 Korinthiyawa 3:17; Afisawa 4:30) Muna yarda wa ruhun ya yi aiki cikin rayukanmu ta kasancewa da ’ya’yansa a dukan abin da muke yi. Bayan ya jera dukan ayyukan jiki da kuma ’ya’yan ruhu, Bulus ya daɗa: “Idan muna rayuwa bisa ga Ruhu, bisa ga Ruhu kuma mu yi tafiya. Kada ka ɓata; ba a yi ma Allah ba’a ba: gama iyakar abin da mutum ya shuka, shi za ya girbe. Gama wanda ya shuka ga jiki nasa, daga wurin jiki za ya girbe ruɓa; amma wanda ya shuka ga Ruhu, daga wurin Ruhu za ya girbe rai na har abada.” (Galatiyawa 5:25; 6:7, 8) Idan za mu yi nasara a kasancewa da tsawon jimrewa, dole ne mu ma mu kasance da sauran ’ya’yan da ruhu mai tsarki ke sakawa cikin Kiristoci.

“Ƙauna Tana da Yawan Haƙuri”

9. Wataƙila, me ya sa Bulus ya gaya wa Korinthiyawa cewa “ƙauna tana da yawan haƙuri”?

9 Bulus ya nuna cewa da akwai dangantaka ta musamman tsakanin ƙauna da tsawon jimrewa da ya ce: “Ƙauna tana da yawan haƙuri.” (1 Korinthiyawa 13:4) Wani ɗalibin Littafi Mai Tsarki, Albert Barnes, ya ce Bulus ya nanata wannan ne domin tsaguwa da jayayya da sun wanzu cikin ikilisiyar Kirista a Koranti. (1 Korinthiyawa 1:11, 12) Barnes ya ce: “Kalmar nan da aka yi amfani da ita a nan [domin tsawon jimrewa] gaba take da garaje: cika da fushi da tunani, da kuma ɓacin rai. Yana nuna yanayin azanci da ke iya JIMREWA DA DAƊEWA yayin da aka zalunci ko aka sa ya fusata.” Ƙauna da tsawon jimrewa har ila na daɗa ga salamar ikilisiyar Kirista sosai.

10. (a) A wace hanya ce ƙauna take taimakonmu mu kasance da tsawon jimrewa, kuma wane gargaɗi manzo Bulus ya bayar game da haka? (b) Wane furci ne wani ɗalibin Littafi Mai Tsarki ya yi a kan tsawon jimrewa na Allah da kuma alheri? (Duba hasiya.)

10 “Ƙauna tana da yawan haƙuri tana da nasiha; ƙauna . . . ba ta sa sonkai, ba ta jin tsokana.” Shi ya sa, a hanyoyi da yawa, ƙauna tana taimaka mana mu kasance da tsawon jimrewa.a (1 Korinthiyawa 13:4, 5) Ƙauna tana sa mu bi da juna cikin haƙuri kuma mu tuna cewa dukanmu ajizai ne kuma muna da laifi da kasawa. Tana taimaka mana mu kasance da alheri kuma mu riƙa gafartawa. Manzo Bulus ya ƙarfafa mu mu yi tafiya “da dukan tawali’u da ladabi, da jimrewa, kuna haƙuri da junanku cikin ƙauna; kuna ƙwazo ku kiyaye ɗayantuwar Ruhu cikin ɗaurin salama.”—Afisawa 4:1-3.

11. Me ya sa yake da muhimmanci musamman a kasance da tsawon jimrewa a tsakanin rukunin Kirista?

11 Kasancewa da tsawon jimrewa na waɗanda suke tsakaninsu yana kawo salama da farin ciki cikin rukunin Kirista, ko a ikilisiyoyi, gidajen Bethel, gidajen ’yan wa’azi na ƙasar waje, ko rukunin magina ko kuma a wasu makarantu na Kirista. Saboda haka, a wasu lokatai bambanci a halaye, yadda son mutum yake, yadda aka yi renonsa, kirkinsa, har ma tsabtarsa ta jiki, sukan jawo damuwa. Haka ma wannan yake cikin iyalai. Ana bukatar jinkirin fushi. (Misalai 14:29; 15:18; 19:11) Dukanmu na bukatar tsawon jimrewa—haƙurin jimrewa, da fatan samun gyara don kyautatawa.—Romawa 15:1-6.

Tsawon Jimrewa Yana Taimakonmu Mu Jimre

12. Me ya sa tsawon jimrewa ke da muhimmanci a lokatai masu wuya?

12 Tsawon jimrewa yana taimakonmu mu jimre da yanayi masu wuya da kamar babu ƙarshe ko maganinsa. Haka wannan yake ga Régis, da aka ambata da farko. Shekaru da yawa, matarsa ta yi hamayya ga ƙoƙarinsa na bauta wa Jehovah. Amma, wata rana ta zo wajensa da hawaye tana cewa: “Na san wannan ce gaskiya. Ka taimake ni. Ina son in yi nazari na Littafi Mai Tsarki.” A ƙarshe aka yi mata baftisma ta zama Mashaidiya. Régis ya ce: “Wannan ya tabbatar da cewa Jehovah ya albarkaci waɗancan shekaru na kokawa, haƙuri, da kuma jimiri.” Ya sami ladar tsawon jimrewarsa.

13. Menene ya taimaki Bulus ya jimre, kuma ta yaya misalinsa zai iya taimaka mana mu jimre?

13 Can baya a ƙarni na farko A.Z., manzo Bulus misali ne mai kyau na tsawon jimrewa. (2 Korinthiyawa 6:3-10; 1 Timothawus 1:16) Kusa da ƙarshen rayuwarsa, lokacin da yake ba da gargaɗi ga abokinsa ƙarami Timothawus, Bulus ya faɗakar da shi cewa dukan Kiristoci za su fuskanci gwadawa. Bulus ya ambata nasa misalin kuma ya faɗa wasu halayen Kirista da sun cancanta don a yi jimiri. Ya rubuta: “Kai ka bi koyarwata, da tasarrufina, da nufina, da bangaskiyata, da tsawon jimrewata, da ƙaunata, da haƙurina, da shan tsanani nawa, da wahalaina; irin al’amuran da suka same ni cikin Antakiya, da Ikoniya, da Listra: irin tsanani da na jimre: daga cikinsu duka fa Ubangiji ya cece ni. I, kuma, dukan waɗanda su ke so su yi rai mai-ibada cikin Kristi Yesu za su sha tsanani.” (2 Timothawus 3:10-12; Ayukan Manzanni 13:49-51; 14:19-22) Domin mu jimre, dukanmu na bukatar bangaskiya, ƙauna, da kuma tsawon jimrewa.

Ku Yafa Tsawon Jimrewa

14. Ga menene Bulus ya kamanta halin ibada irinsu tsawon jimrewa, kuma wane gargaɗi ya ba wa Kiristoci a Kolossiya?

14 Manzo Bulus ya kamanta tsawon jimrewa da wasu halaye na ibada da tufafi da Kirista zai yafa bayan ya tuɓe na ayyuka da ke na ‘tsohon hali.’ (Kolossiyawa 3:5-10) Ya rubuta: “Domin ku zaɓaɓu na Allah ne, masu-tsarki, ƙaunatattu kuma, ku yafa zuciya ta tausayi, nasiha, tawali’u, ladabi, jimrewa; kuna haƙuri da juna, kuna gafarta ma juna, idan kowanne mutum yana da maganar ƙara game da wani; kamar yadda Ubangiji ya gafarta muku, hakanan kuma sai ku yi: gaba da dukan waɗannan kuma ku yafa ƙauna, gama ita ce magamin kamalta.”—Kolossiyawa 3:12-14.

15. Me ke faruwa yayin da Kiristoci sun ‘yafa wa kansu’ tsawon jimrewa da kuma wasu halaye na ibada?

15 Idan waɗanda suke cikin ikilisiya suka ‘yafa wa kansu’ zuciya ta tausayi, alheri, tawali’u, ladabi, tsawon jimrewa, da kuma ƙauna, za su iya warware matsaloli kuma su ci gaba cikin haɗin kai cikin hidimar Jehovah. Masu kula Kirista musamman suna bukatar kasancewa da tsawon jimrewa. Akwai lokatai da suke bukatar yi wa wani Kirista horo, amma ana iya yin horo a hanyoyi dabam dabam. Bulus ya kwatanta hali mafi kyau na yin haka lokacin da ya rubuta wa Timothawus: “Ka tsautar, ka kwaɓa, ka gargaɗar, da iyakacin jimrewa da koyarwa.” (2 Timothawus 4:2) Hakika, ya kamata koyaushe a bi da tumakin Jehovah da tsawon jimrewa, daraja, da tausayi.—Matta 7:12; 11:28; Ayukan Manzanni 20:28, 29; Romawa 12:10.

“Ku Yi Haƙuri da Kowa”

16. Me zai iya zama sakamakonsa idan muka kasance da “haƙuri da kowa”?

16 Tsawon jimrewa na Jehovah ga mutane ya sa mu kasance da hakki na mu “yi haƙuri da kowa.” (1 Tassalunikawa 5:14) Wannan yana nufin kasancewa da haƙuri da waɗanda suke cikin iyali da ba Shaidu ba, maƙwabta, abokan aiki, da kuma abokan aji. Shaidu da yawa sun sha kan matsaloli da yawa, waɗanda cikin shekaru da yawa, suna shan ashar ko hamayya kai tsaye wajen mutane da suke aiki tare ko kuma makaranta. (Kolossiyawa 4:5, 6) Manzo Bitrus ya rubuta: “Kuna al’amura na dacewa wurin Al’ummai; domin, yayinda su ke kushenku kamar ma’aikatan mugunta, ta wurin nagargarun ayyukanku da su ke dubawa su ɗaukaka Allah cikin ranar ziyara.”—1 Bitrus 2:12.

17. Ta yaya za mu iya yin koyi da ƙaunar Jehovah da tsawon jimrewarsa, kuma me ya sa ya kamata mu yi haka?

17 Tsawon jimrewa na Jehovah zai zama ceto ga miliyoyi. (2 Bitrus 3:9, 15) Idan muka yi koyi da ƙaunar Jehovah da tsawon jimrewarsa, za mu ci gaba da wa’azin bisharar Mulkin Allah da haƙuri da koyar da wasu su ba da kai ga Sarautar Kristi. (Matta 28:18-20; Markus 13:10) Idan muka daina wa’azi, zai zama muna neman yanke tsawon jimrewa na Jehovah ke nan kuma muna ƙin fahimtar manufarsa, wadda domin kawo mutane ne zuwa tuba.—Romawa 2:4.

18. Wace addu’a Bulus ya yi wa Kolossiyawa?

18 A cikin wasiƙarsa zuwa ga Kiristoci a Kolossiya, Asiya Ƙarama, Bulus ya rubuta: “Saboda wannan mu kuma, tun ran da muka ji wannan, ba mu fasa yin addu’a da roƙo dominku ba, ku cika da sanin nufinsa cikin dukan hikima mai-ruhaniya da fahimi kuma, da za ku yi tafiya wadda ta cancanta ga Ubangiji, kuna gamshe shi sarai, kuna bada ’ya’ya cikin kowane kyakkyawan aiki, kuna ƙaruwa kuma cikin sanin Allah; ƙarfafaffu da dukan iko, bisa ga ikon ɗaukakarsa, zuwa dukan haƙuri da jimrewa tare da farinciki.”—Kolossiyawa 1:9-11.

19, 20. (a) Ta yaya za mu guji ɗaukar tsawon jimrewa na Jehovah cewa gwaji ne? (b) Waɗanne fa’idodi ke zuwa daga tsawon jimrewarmu?

19 Ci gaba na tsawon jimrewa na Jehovah, ko haƙuri, ba zai zama wani gwaji gare mu ba idan mun “cika da sanin nufinsa,” wanda ke nufin cewa “dukan [iri-irin] mutane su tsira, kuma su kawo ga sanin gaskiya.” (1 Timothawus 2:4) Za mu ci gaba da “bada ’ya’ya cikin kowane kyakkyawan aiki,” musamman na wa’azin “bishara kuwa ta mulki.” (Matta 24:14) Idan mun ci gaba da yin haka cikin aminci, Jehovah zai sa mu zama “ƙarfafaffu da dukan iko,” yana sa mu iya “haƙuri da jimrewa tare da farinciki.” Ta haka, za mu ‘yi tafiya da ya cancanci na Jehovah,’ kuma za mu samu salama da ke zuwa da sanin cewa muna “gamshe shi sarai.”

20 Bari mu tabbata sosai game da tsawon jimrewa na Jehovah. Domin cetonmu ne kuma da ceton waɗanda suke saurara ga wa’azinmu da koyarwa. (1 Timothawus 4:16) Koyon ’ya’yan ruhu—ƙauna, nasiha, nagarta, tawali’u, da kuma kamewa—zai sa mu yi tsawon jimrewa da farin ciki. Za mu fi zama ta salama tare da waɗanda suke cikin iyalinmu da kuma ’yan’uwanmu maza da mata cikin ikilisiya. Tsawon jimrewa kuma zai taimake mu mu yi haƙuri da abokan aikinmu ko na makaranta. Tsawon jimrewarmu kuma zai kasance da ma’ana, na ceton masu laifi da kuma na ɗaukaka Allah mai tsawon jimrewa, Jehovah.

[Hasiya]

a Da yake magana a kan zancen Bulus cewa “ƙauna tana da yawan haƙuri,” manazarin Littafi Mai Tsarki Gordon D. Fee ya rubuta: “A cikin koyarwar Bulus [tsawon jimrewa da alheri] suna wakiltar gefe biyu na halin Allah wajen bil Adam (Gwada da Rom. 2:4). A wata sassa, ƙaunar Allah ta jimiri tana bayyana ta wurin riƙe fushinsa wajen tawayen bil Adam ne; a wata sassa kuma, ana ganin alherinsa cikin nuna jinƙai nasa mai yawa. Saboda haka, kwatancin Bulus na ƙauna ya soma da kwatanci kashi biyu game da Allah, wanda ta wurin Kristi ya nuna kansa mai jimiri mai alheri ga waɗanda suka cancanci hukuncinsa.”

Za Ka Iya Bayyanawa?

• A waɗanne hanyoyi ne Kristi misali mai girma na tsawon jimrewa?

• Menene zai taimake mu mu koyi tsawon jimrewa?

• Ta yaya ne tsawon jimrewa ke taimakon iyalai, rukunin Kirista, da kuma dattawa?

• Ta yaya kasancewa da tsawon jimrewa ke kawo mana da kuma wasu fa’idodi?

[Hoto a shafi na 27]

Har lokacin da yake cikin matsi mai tsanani, Yesu ya yi haƙuri da almajiransa

[Hoto a shafi na 28]

An aririci Kiristoci masu kula su nuna misali mai kyau na tsawon jimrewa a bi da ’yan’uwansu

[Hoto a shafi na 29]

Idan muka yi koyi da ƙaunar Jehovah da kuma tsawon jimrewarsa, za mu ci gaba da yin wa’azin bishara

[Hoto a shafi na 30]

Bulus ya yi addu’a cewa Kiristoci su ‘yi haƙuri da farin ciki’

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba