MATALAUTA Suna Daɗa Talauci
“Babu wata jam’iyya da za ta yi nasara kuma ta yi farin ciki, da yawancin waɗanda ke cikinta matalauta ne kuma tsiyayyu.”
MASANIN tattalin arziki Adam Smith ne ya yi maganar nan can baya a ƙarni na 18. Mutane da yawa sun tabbata da cewa gaskiyar abin da ya ce ta ma fi dacewa da yau. An fi ganin bambanci da ke tsakanin mawadata da matalauta. A ƙasar Philippines, kashi uku na jama’a kowacce rana suna rayuwa bisa kuɗi da bai kai dala guda ba ta Amirka, kuɗin da ake samu a ’yan mintoci a ƙasashe masu arziki. Human Development Report 2002 na Majalisar Ɗinkin Duniya ya ce “kashi 5 bisa ɗari na waɗanda suka fi arziki a duniya suna daɗa samun kuɗi sau 114 fiye da wanda matalauta kashi 5 bisa ɗari suke samu.”
Ko da yake wasu mutane suna morar rayuwa, miliyoyi suna zaman gidan wasu ne, suna gina rumfa duk inda suka samu. Wasu ba su da sa’a sam; suna kwanciya a titi a kan shimfiɗar kwali ko leda da zai kāre su daga ƙasa. Yawancinsu suna faman samun na ci yadda za su iya—suna kwasan kayan bola, suna dako, ko kuma kwasan kwalaben bola a amalanke don su sayar.
Ba a ƙasashe masu bunƙasa kaɗai ake ganin bambanci tsakanin masu arziki da matalauta ba amma, kamar yadda Bankin Duniya ya ce, “ ‘akwai matalauta a dukan ƙasashe.” Daga Bangladesh zuwa Amirka, ko da yaya yawan arzikin wasu yake, da akwai waɗanda suke faman samun na ci ko su sami wurin kwanciya. The New York Times ya ɗauko wani rahoton Ƙungiyar Kirge na Amirka na shekara ta 2001 da ke nuna cewa bambanci tsakanin masu arziki da matalauta a Amirka ya ci gaba da ƙaruwa. Ya ce: “Kashi biyar bisa ɗari na waɗanda suka fi arziki a Amirka an biya su kuɗin kayayyakin cikin gida kashi hamsin bisa ɗari a shekarar da ta shige . . . Kuma kashi biyar bisa ɗari na matalauta an biya su kashi uku da rabi kawai bisa ɗari na kayayyakin cikin gida.” Yanayin ɗaya ne ko ma ya fi wannan muni a ƙasashe da yawa. Rahoton Bankin Duniya ya nuna cewa kashi 57 na jama’ar duniya suna rayuwa kowacce rana da kuɗin da bai kai dala biyu ba.
Mafi muni ma, a shekara ta 2002, mutane miliyoyi sun damu da rahoton cewa wasu manya sun samu arziki ta wasu hanyoyin maguɗi. Ko idan ba a yi wani abu da ake gani na karya doka ba, mutane da yawa suna jin yadda waɗannan manyan, in ji jaridar Fortune, “suke samun mugun arziki, mai yawan gaske.” Idan aka bi abin da yake faruwa cikin duniya, wasu suna damuwa yadda mutane za su iya samun kuɗi masu yawa hakan, ɗarurruwan miliyoyi da ba a iya kirgensu, kuma a ce hakan daidai ne sa’i nan kuma wasu suna talauci.
Talauci Zai Kasance Har Abada Ne?
Wannan ba ya nufin cewa babu wanda yake ƙoƙarin yin wani abu game da matsalar matalauta ba. Manya cikin gwamnati da kuma ƙungiyoyin taimako suna ƙoƙarce-ƙoƙarce domin su kawo canji. Duk da haka, babu abin ƙarfafa. Duk da ƙoƙarce-ƙoƙarcen a yi gyara, Human Development Report 2002 ta ce “ƙasashe da yawa suna talauci yanzu na shekaru 10, 20, wasu ma shekaru 30 da suka shige.”
Wannan ya sa ya zama cewa matalauta ba su da bege ne? Muna gayyatarka ka karanta talifi na gaba, ka yi la’akari da abubuwan da za su taimaka a yanzu, kuma da yadda za a yi maganinsa da ba ka yi tunaninsa ba.