Za Ka Iya Fahimtar Littafi Mai Tsarki
LITTAFI MAI TSARKI na ɗauke da gaskiya mai tamani daga Allah. Ya gaya mana manufar rayuwa, sanadin wahalar ’yan adam, da kuma yadda rayuwar ’yan adam za ta kasance a nan gaba. Yana koya mana yadda za mu sami farin ciki, yadda za mu yi abokai, da kuma yadda za mu magance matsaloli. Mafi muhimmanci, yana koya mana game da Mahaliccinmu kuma Ubanmu na samaniya. Irin wannan sanin na kawo mana farin ciki kuma yana sa rayuwarmu ta kasance da ma’ana.
Littafi Mai Tsarki ya kwatanta fahimtar sanin Allah da cin abinci. Yesu ya ce: “Ba da abinci kaɗai ba mutum za ya rayu, amma da kowace magana da ke fitowa daga bakin Allah.” (Matta 4:4; Ibraniyawa 5:12-14) Kamar yadda muke bukatar mu ci abinci mai kyau kowace rana don mu kasance a raye, hakazalika, muna bukatar mu karanta Kalmar Allah a kai a kai idan muna son mu kasance cikin waɗanda Allah ya yi wa alkawarin rai madawwami.
Muna jin daɗin cin abinci domin yadda aka halicce mu, kuma domin cin abinci na biyan wata bukata a jikinmu. Amma, muna da wata bukata mai muhimmanci da muke bukatar mu kula da ita idan muna so mu yi farin ciki. Yesu ya ce: “Masu-albarka ne masu-ladabi a ruhu.” (Matta 5:3) Za mu iya samun farin ciki domin za a iya biyan wannan bukatar ta wajen fahimtar Kalmar Allah.
Hakika, yana yi wa wasu wuya su fahimci Littafi Mai Tsarki. Alal misali, wataƙila za ka bukaci taimako don ka fahimci kalaman da suka yi magana a kan al’adun da ba ka sani ba, ko kuwa waɗanda suka yi amfani da kalamai na alama. Bayan haka, akwai annabce-annabcen da aka rubuta su a yare ta alama, waɗanda za a iya fahimtarsu ne kawai ta wajen duba wasu kalamai a cikin Littafi Mai Tsarki da suka yi magana game da irin wannan batun. (Daniel 7:1-7; Ru’ya ta Yohanna 13:1, 2) Duk da haka, za ka iya fahimtar Littafi Mai Tsarki. Ta yaya za ka iya tabbatar da haka?
Kowa Zai iya Fahimta
Littafi Mai Tsarki Kalmar Allah ce. Allah ya bayyana mana nufinsa a cikinta. Kana ganin cewa Allah zai yi tanadin littafin da zai yi wuyar fahimta ko kuwa wanda mutane masu ilimi ne kawai za su iya fahimtarsa? A’a, domin Jehobah mai alheri ne. Yesu Kristi ya ce: “Wanene daga cikinku da shi ke uba, ɗansa za ya roƙi dunƙulen gurasa, shi kuwa ya ba shi dutse? Ko kuwa kifi, ya ba shi kuma maciji maimakon kifi? Ko kuwa idan ya roƙi ƙwai, ya ba shi kunama? Idan ku fa da ku ke miyagu, kun san yadda za ku ba ’ya’yanku alherai, balle fa Ubanku na sama za ya bada Ruhu Mai-tsarki ga waɗanda su ke roƙonsa?” (Luka 11:11-13) Da haka, ka ga cewa za ka iya fahimtar Littafi Mai Tsarki, kuma idan ka roƙi Allah da zuciya ɗaya, zai yi maka tanadin taimakon da kake bukata don ka fahimci Kalmarsa. Har ƙananan yara ma za su iya fahimtar koyarwar Littafi Mai Tsarki.—2 Timothawus 3:15.
Ko da yake ana bukatar yin ƙoƙari sosai don a fahimci Littafi Mai Tsarki, amma hakan zai ƙarfafa mu sosai. Bayan da aka ta da shi daga matattu, Yesu ya bayyana ga manzaninsa su biyu kuma ya tattauna annabce-annabcen Littafi Mai Tsarki da su. Labarin ya ce: “Ya soma kuwa tun daga Musa da dukan annabawa, cikin dukan littattafai yana fasalta musu al’amura na bisa kansa.” Menene sakamakon? Da yamma, sa’ad da suke tunani game da abin da suka koya, manzannin sun ce ma junansu: “Zuciyarmu ba ta ƙuna daga cikinmu ba, sa’anda yana yi mamu zance a kan hanya, yana bayyana mamu littattafai?” (Luka 24:13-32) Fahimtar Kalmar Allah ya sa su farin ciki, domin ya ƙarfafa bangaskiyarsu a alkawuran Allah kuma ya sa su kasance da ra’ayi mai kyau game da nan gaba.
Maimakon kasancewa abu mai wuya, fahimtar Kalmar Allah abu ne mai kyau kuma mai amfani, kamar yadda mutum zai ji daɗin cin abinci mai daɗi. Menene kake bukatar ka yi idan kana so ka sami irin wannan fahimin? Talifi na gaba zai nuna yadda za ka iya moran “sanin Allah.”—Misalai 2:1-5.
[Hoto a shafi na 4]
Kamar Uba mai ƙauna, Jehobah yana ba mu ruhunsa mai tsarki don ya taimaka mana mu fahimci Littafi Mai Tsarki