Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w08 5/15 pp. 17-21
  • Ka Bauta Wa Jehobah Sa’ad Da Kake Matashi

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Bauta Wa Jehobah Sa’ad Da Kake Matashi
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Bauta wa Jehobah Ita Ce Abin da ya Dace da za Mu Yi
  • Sa’ad da Wasu Suka Tuhume Ka Ko Suka Yi Maka Hamayya
  • An Buɗe Maka “Kofa Mai-Faɗi”
  • “Ku Ɗanɗana Ku Duba, Ubangiji Nagari Ne”
  • Maganar Jehobah Tana Cika A Kullayaumi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • Matasa, Ku Zaɓi Ku Bauta Wa Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Yana Son Mu Yi Nasara
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Mai Cika Alkawura
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
w08 5/15 pp. 17-21

Ka Bauta Wa Jehobah Sa’ad Da Kake Matashi

“Ka lizima kai a cikin al’amuran da ka koyo, waɗanda ka tabbata da su kuma.”—2 Tim. 3:14.

1. Ta yaya ne Jehobah yake ɗaukan hidimar Shaidunsa matasa?

HIDIMA mai tsarki na matasa yana da muhimmanci ga Jehobah wanda hakan ya sa ya hura annabci game da su. “Mutanenka suna bada kansu hadaya da yardan rai cikin ranar ikonka” in ji mai zabura. “Cikin jamalin tsarki, daga cikin cikin safiya, Kana riƙe da raɓar ƙuruciyarka.” (Zab. 110:3) Hakika, Jehobah yana daraja matasan da suke son su bauta masa sosai.

2. Waɗanne tasiri na abin duniya game da rayuwarsu ta nan gaba ce matasa suke fuskanta?

2 Ku matasa da ke cikin ikilisiyar Kirista, kun keɓe kanku ga Jehobah kuwa? Yana iya yi wa matasa masu yawa wuya su yanke shawarar bauta wa Allah na gaskiya. Manyan ’yan kasuwa, malamai, kuma a wasu lokatai ’yan’uwa da kuma abokai sukan mai da hankalin matasa wajen biɗar abin duniya. Sa’ad da matasa suka biɗi makasudai na ruhaniya, mutane sukan yi musu dariya. Amma gaskiyar ita ce, bauta wa Allah na gaskiya ita ce hanyar rayuwa mafi kyau da za ka iya biɗa. (Zab. 27:4) Game da wannan, yi la’akari da waɗannan tambayoyin guda uku: Me ya sa ya kamata ka bauta wa Allah? Ta yaya za ka iya yin nasara a matsayin mutumin da ya keɓe kansa ga Allah duk da abin da wasu za su iya cewa ko su yi? Waɗanne dama masu kyau na hidima mai tsarki ne za ka iya samu?

Bauta wa Jehobah Ita Ce Abin da ya Dace da za Mu Yi

3. Ta yaya ya kamata halittar Jehobah ta shafe mu?

3 Me ya sa ya kamata ka bauta wa Allah na gaskiya? Ru’ya ta Yohanna 4:11 ta ambata dalilin: “Kai ne mai-isa ka karɓi ɗaukaka da daraja da iko, ya Ubangijinmu da Allahnmu: gama kai ka halicci dukan abu, saboda nufinka kuma suka kasance, saboda nufinka aka halicce su.” Jehobah ne Mahaliccin dukan abubuwa. Duniya tana da kyau sosai! Jehobah ne ya halicci itatuwa, furanni, dabbobi, teku, manyan duwatsu, da kuma gangarowan ruwa. Zabura 104:24 ta ce: “Duniya cike ta ke da wadatarka.” Ya kamata mu yi godiya sosai domin Jehobah cikin ƙauna ya ba mu jiki da kuma hankali da zai sa mu more duniya da kuma abubuwa masu kyau da ke cikinta! Ya kamata nuna godiya domin halittunsa masu ban al’ajabi sun motsa mu mu bauta masa. Ko ba haka ba?

4, 5. Waɗanne ayyuka ne na Jehobah suka sa Joshuwa ya kusanci Jehobah?

4 Wani dalilin kuma da zai sa mu bauta wa Jehobah yana cikin kalaman Joshuwa shugaban Isra’ila. A kusan ƙarshen rayuwarsa, Joshuwa ya gaya wa mutanen Allah: “Ku kuma kun sani cikin zukatanku duka da cikin rayukanku duka, babu wani abu ɗaya ya sare daga cikin dukan alherai waɗanda Ubangiji Allahnku ya ambace su a kanku: dukansu sun tabbata a gareku, babu wani abu ɗaya ya sare daga ciki.” Me ya sa Joshuwa ya faɗi haka?—Josh. 23:14.

5 A matsayin yaro da ke tasowa a ƙasar Masar, Joshuwa ya san alkawarin da Jehobah ya yi na ba Isra’ilawa ƙasar da za ta zama ta su. (Far. 12:7; 50:24, 25; Fit. 3:8) Bayan haka, Joshuwa ya ga yadda Jehobah ya soma cika wannan alkawarin sa’ad da ya kawo Annoba Goma a kan Masar kuma ya tilasta wa Fir’auna mai taurin kai ya ƙyale ’ya’yan Isra’ila. Joshuwa yana cikin waɗanda aka cece su a cikin Jar Teku, kuma ya ga yadda wannan tekun ta cinye Fir’auna da sojojinsa. A lokacin doguwar tafiyar da suka yi a cikin “babban jeji, mai-ban tsoron” da ke Hamadar Sinai, Joshuwa ya ga yadda Jehobah ya yi wa Isra’ilawa tanadin dukan abubuwan da suke bukata. Babu wani a cikinsu da ya mutu domin ƙishirwa ko yunwa. (K. Sha 8:3-5, 14-16; Josh. 24:5-7) Sa’ad da lokaci ya yi da Isra’ilawa za su kame manyan ƙasashen Ka’aniyawa kuma su soma zama a cikin Ƙasar Alkawari, Joshuwa ya ga yadda Allah wanda shi da sauran Isra’ilawa suke bauta wa ya taimaka musu a wannan aikin.—Josh. 10:14, 42.

6. Menene zai taimaka maka ka so bauta wa Allah?

6 Joshuwa ya san cewa Jehobah ya cika alkawuransa. Hakan ya sa Joshuwa ya ce: “Amma da ni da gidana, Ubangiji za mu bauta ma.” (Josh. 24:15) Kai kuma fa? Sa’ad da ka yi tunanin alkawuran da Allah na gaskiya ya riga ya cika da kuma waɗanda yake gab da cikawa, hakan na motsa ka ka so bauta masa kamar Joshuwa?

7. Me ya sa baftisma mataki ne mai muhimmanci da ya kamata a ɗauka?

7 Yin tunani a kan abubuwan da Jehobah ya halitta da kuma yin bimbini a kan alkawuransa masu ban al’ajabi da kuma tabbatattu, ya kamata su motsa ka ka keɓe kanka ga Jehobah kuma ka tabbatar da haka ta wajen yin baftisma. Baftisma mataki ne mai muhimmanci da waɗanda suke son su bauta wa Allah za su ɗauka. Yesu, wanda shi ne Misalin da muke bi, ya tabbatar da hakan. Sa’ad da yake gab da soma aikinsa a matsayin Almasihu, ya miƙa kansa ga Yohanna Mai Baftisma don ya yi masa baftisma. Me ya sa Yesu ya ɗauki wannan matakin? “Na sabko daga sama, ba domin in yi nufin kaina ba,” sai ya daɗa cewa, “amma nufin wanda ya aiko ni.” (Yoh. 6:38) Yesu ya yi baftisma ne don ya nuna cewa ya ba da kansa ga yin nufin Ubansa.—Mat. 3:13-17.

8. Me ya sa Timothawus ya zaɓi ya bauta wa Allah, kuma me ka ke bukatar ka yi?

8 Yi la’akari da Timothawus, wani matashi Kirista wanda Jehobah ya ba aiki da gata mai yawa. Me ya sa Timothawus ya yanke shawarar bauta wa Allah na gaskiya? Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa ‘ya koyi al’amura, waɗanda ya tabbata da su.’ (2 Tim. 3:14) Idan ka riga ka yi nazarin Kalmar Allah kuma an rinjaye ka ka gaskata cewa koyarwarta gaskiya ce, to, yanayinka ɗaya ne da na Timothawus. A yanzu, kana bukatar ka yanke shawara. Me ya sa ba za ka gaya wa iyayenka abubuwan da ka ke son ka yi ba? Tare da dattawan ikilisiya, iyayenka suna iya taimaka maka ka fahimci abubuwan da ake bukata daga gareka da ke rubuce a cikin Nassi kafin ka yi baftisma.—Ka karanta Ayukan Manzanni 8:12.

9. Sa’ad da ka yi baftisma, ta yaya hakan zai shafi mutane?

9 Idan ka yi baftisma, hakan zai zama mataki mai kyau na soma bauta wa Allah na gaskiya. Ta wajen ɗaukan wannan matakin, ka shiga dogon tsere wanda sakamakon su ne rai na har abada da kuma farin cikin da ake samu na yin nufin Allah. (Ibran. 12:2, 3) Kuma za ka sa waɗanda suke cikin iyalinka da suka riga suka soma wannan tseren har da abokanka da suke cikin ikilisiyar Kirista farin ciki. Mafi muhimmanci, za ka faranta wa Jehobah zuciya. (Ka karanta Misalai 23:15.) Hakika, wasu ba za su fahimci dalilin da ya sa ka zaɓi ka bauta wa Jehobah ba, kuma suna iya tunanin cewa wannan ba shawara mai kyau ba ce. Suna ma iya yi maka hamayya. Amma za ka iya sha kan waɗannan matsalolin.

Sa’ad da Wasu Suka Tuhume Ka Ko Suka Yi Maka Hamayya

10, 11. (a) Waɗanne tambayoyi ne mutane za su iya yi maka game da shawarar da ka tsai da na bauta wa Allah? (b) Menene za ka iya koya daga yadda Yesu ya amsa tambayoyi game da bauta ta gaskiya?

10 Shawarar da ka yanke na bauta wa Jehobah tana iya ba abokan makarantarka, maƙwabtanka, da kuma ’yan’uwanka mamaki. Suna iya tambayarka dalilin da ya sa ka zaɓi bin wannan tafarkin kuma su tuhume ka game da abin da ka gaskata. Yaya ya kamata ka amsa? Hakika, kana bukatar ka bincika tunaninka da yadda ka ke ji don ka iya bayyana dalilan zaɓenka. Sa’ad da ka ke amsa tambayoyi game da imaninka, misalin Yesu shi ne mafi kyau da za ka bi.

11 Sa’ad da shugabannin addinai na Yahudawa suka tuhumi Yesu game da tashin matattu, ya jawo hankalinsu zuwa ga nassi da ba su bincika ba. (Fit. 3:6; Mat. 22:23, 31-33) Sa’ad da wani marubuci ya tambaye shi wace doka ce ta fi girma, Yesu ya yi ƙaulin ayoyin Littafi Mai Tsarki da suka dace. Mutumin ya gode wa Yesu don amsar da ya ba shi. (Lev. 19:18; K. Sha 6:5; Mar. 12:28-34) Yadda Yesu ya yi amfani da Nassosi da yadda yake koyarwa ya sa “hankalin taro ya rabu biyu saboda shi” kuma ’yan hamayya suka kasa cutar da shi. (Yoh. 7:32-46) Sa’ad da ka ke amsa tambayoyi game da bangaskiyarka, ka yi amfani da Littafi Mai Tsarki kuma ka amsa “da ladabi da tsoro.” (1 Bit. 3:15) Idan ba ka san amsar wata tambaya ba, ka faɗi cewa ba ka sani ba kuma ka ce za ka yi bincike. Ka bincika batun ta wajen yin amfani da littafin nan Watch Tower Publications Index ko kuma Watchtower Library da ke cikin CD-ROM idan akwai a yarenku. Idan ka yi shiri da kyau, za ka san ‘yadda za ka amsa tambayar kowa.’—Kol. 4:6.

12. Me ya sa bai kamata mu ƙyale tsanantawa ta sa mu sanyin gwiwa ba?

12 Za ka iya fuskantar abubuwan da suka fi tambayoyi game da matsayinka da kuma imaninka. Ballantana ma, maƙiyin Allah, Shaiɗan Iblis ne yake shugabancin wannan duniya. (Ka karanta 1 Yohanna 5:19.) Ba zai dace ba ka sa rai cewa za ka sami yabo ko karɓuwa a wurin kowa da kowa, kuma kana iya fuskantar hamayya. Wasu mutane suna iya ‘zaginka,’ kuma suna iya ci gaba da yin hakan. (1 Bit. 4:4) Amma ka tuna cewa ba kai kaɗai ba ne ka taɓa fuskantar hakan. Yesu Kristi ma ya fuskanci tsanantawa. Manzo Bitrus ma ya fuskanci hamayya, kuma ya rubuta: “Ƙaunatattu, kada ku ga abin mamaki ne tsanani mai-zafin nan da ke wurinku, wanda ke auko muku domin ya auna ku, sai ka ce wani baƙon al’amari ya same ku: amma da shi ke kuna tarayya cikin azabai na Kristi sai ku yi murna.”—1 Bit. 4:12, 13.

13. Me ya sa Kiristoci za su iya yin farin ciki sa’ad da aka tsananta musu?

13 Jimre wa tsanantawa ko kuma hamayya domin kai Kirista ne dalili ne na farin ciki. Me ya sa? Domin samun amincewar duniya zai nuna cewa kana rayuwar da ta jitu da mizanan Shaiɗan ba na Allah ba. Yesu ya yi kashedi: “Kaitonku, lokacin da dukan mutane za su yabe ku! gama hakanan ubanninsu suka yi ma maƙaryatan annabci.” (Luka 6:26) Tsanantawa na nuna cewa Shaiɗan da duniyarsa suna fushi da kai domin kana bauta wa Jehobah. (Ka karanta Matta 5:11, 12.) Kuma “shan zargi sabili da sunan Kristi” abu ne na farin ciki.—1 Bit. 4:14.

14. Wane amfani ne mai kyau mutum zai iya samu idan ya kasance da aminci ga Jehobah duk da tsanantawa?

14 Sa’ad da ka riƙe amincinka ga Jehobah duk da tsanantawa, akwai aƙalla sakamako huɗu masu kyau. Ka ba da shaida domin Allah da Ɗansa. Jimrewarka da aminci na ƙarfafa ’yan’uwanka Kiristoci. Wannan yana iya motsa wasu da suka lura da hakan da ba su san Jehobah ba su biɗe shi. (Ka karanta Filibbiyawa 1:12-14.) Sa’ad da ka ga yadda Jehobah ya ƙarfafa ka ka jimre wa gwaji, za ka ƙara ƙaunarsa.

An Buɗe Maka “Kofa Mai-Faɗi”

15. Wace “kofa mai-faɗi” ce aka buɗe wa manzo Bulus?

15 Manzo Bulus ya rubuta game da hidimarsa a Afisa yana cewa: “Kofa mai-faɗi mai-yalwar aiki tana a buɗe.” (1 Kor. 16:8, 9) Kofa ce da za ta kai ga yin wa’azin bishara da almajirantarwa a cikin wannan birnin. Ta wajen yin amfani da wannan zarafin, Bulus ya taimaka wa mutane da yawa su koya game da Jehobah kuma su bauta masa.

16. Ta yaya shafaffun da suka rage suka shiga “kofa mai-faɗi” a shekara ta 1919?

16 A shekara ta 1919 Yesu Kristi mai ɗaukaka ya buɗe “kofa mai-faɗi” ga shafaffu da suka rage. (R. Yoh. 3:8) Sun bi ta ƙofar kuma suka soma wa’azin bishara da koyar da gaskiyar Littafi Mai Tsarki da himma fiye da dā. Menene sakamakon hidimarsu? A yanzu bishara ta kai iyakar duniya, kuma mutane kusan miliyan bakwai ne suke da begen samun rai madawwami a sabuwar duniya ta Allah.

17. Ta yaya za ka iya shigan “kofa mai-faɗi mai-yalwar aiki”?

17 Har yanzu “kofa mai-faɗi mai-yalwar aiki” tana buɗe ga dukan bayin Jehobah. Waɗanda suke bin ta suna samun farin ciki da gamsuwa yayin da suke yin wa’azin bishara sosai. Ku matasa bayin Jehobah, ta yaya kuke daraja gata mai tamanin da kuke da shi wanda babu na biyunsa na taimaka wa mutane su “bada gaskiya ga bisharan”? (Mar. 1:14, 15) Kun taɓa tunanin soma hidima na majagaba na kullum ko na ɗan lokaci? Gina Majami’ar Mulki, hidima a Bethel, da kuma yin wa’azi a ƙasashen waje suna cikin damar da yawancinku za su iya samu. Tun da yake wannan muguwar duniya ta Shaiɗan ta kusan ƙarewa, saka hannu a waɗannan ɓangarori na hidimar Mulki yana zama abin gaggawa a kullum. Za ka so ka shiga wannan “kofa mai-faɗi” tun da sauran lokaci?

“Ku Ɗanɗana Ku Duba, Ubangiji Nagari Ne”

18, 19. (a) Menene ya taimaka wa Dauda ya kasance da muradi mai ƙarfi na bauta wa Jehobah? (b) Menene ya nuna cewa Dauda bai taɓa nadamar bauta wa Allah ba?

18 Mai zaburar da aka hure ya gayyaci mutane su “ɗanɗana, [su] duba, Ubangiji nagari ne.” (Zab. 34:8) A lokacin da Sarki Dauda na Isra’ila ta dā yake makiyayi matashi, Jehobah ya cece shi daga harin manyan dabbobin daji. Jehobah ya taimaka masa a yaƙin da ya yi da Goliyat kuma ya cece shi daga bala’o’i masu yawa. (1 Sam. 17:32-51; Zab. 18:0-50) Saboda irin ƙauna da alherin da Allah ya nuna masa, hakan ya motsa Dauda ya rubuta cewa: “Ya Ubangiji Allahna, ayyuka masu-ban al’ajabi, waɗanda ka yi, suna dayawa, duk da tunaninka waɗanda sun nufo wajenmu: ba su lissaftuwa a gabanka.”—Zab. 40:5.

19 Dauda ya ƙaunaci Jehobah sosai kuma ya yaba masa da dukan zuciyarsa. (Ka karanta Zabura 40:8-10.) Bayan shekaru masu yawa, Dauda bai taɓa yin nadamar bauta wa Allah na gaskiya da dukan rayuwarsa ba. Bauta wa Allah da dukan zuciyarsa ita ce abu mafi tamani a gare shi, abin farin ciki wadda ba ta da na biyu. Sa’ad da ya tsufa, Dauda ya ce: “Gama kai ne begena, ya Ubangiji Yahweh: kai ne madogarata tun ina yaro. I, har lokacinda na tsufa na yi furfura, kada ka yashe ni, ya Allah.” (Zab. 71:5, 18) Dauda ya dogara ga Jehobah kuma abotarsu ta ƙara ƙarfi sosai, duk da cewa tsufa ta kama shi.

20. Me ya sa bauta wa Allah ita ce hanya mafi kyau ta yin amfani da rayuwarka?

20 Rayuwar Joshuwa, Dauda, da Timothawus sun ƙara tabbatar da cewa bauta wa Jehobah ita ce hanya mafi kyau ta yin amfani da rayuwarka. Ɗan abin duniyar da za a samu a yanzu ba komi ba ne idan aka haɗa shi da amfani na har abada da za ka samu daga ‘bauta wa Jehobah da dukan zuciyarka da dukan ranka kuma.’ (Josh. 22:5) Idan ba ka keɓe kanka ga Jehobah ba a addu’a, ka tambayi kanka, ‘Menene ke riƙe ni daga zama Mashaidin Jehobah? Idan ka riga ka yi baftisma kuma kana bauta wa Jehobah, za ka so ka daɗa farin cikinka a rayuwa? To, ka faɗaɗa hidimarka, kuma ka ci gaba da samun cin gaba a ruhaniya. Talifi na gaba zai nuna maka yadda za ka iya samun cin gaba a ruhaniya ta wajen bin misalin manzo Bulus.

Yaya Za Ka Amsa?

• Ka ba da dalilai biyu da suka sa ya kamata mu bauta wa Allah?

• Menene ya taimaka wa Timothawus ya yanke shawarar bauta wa Allah?

• Me ya sa ya kamata ka kasance da ƙarfi sa’ad da ka ke fuskantar tsanantawa?

• Waɗanne dama na hidima ne za ka iya samu?

[Hoto a shafi na 18]

Bauta wa Jehobah ita ce hanya mafi kyau a rayuwa

[Hoto a shafi na 19]

Za ka iya amsa tambayoyi game da imaninka?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba