Bauta wa Allah da ‘Zuciya da Rai Ɗaya’
YAHUDAWA da kuma shigaggu sun kewaye almajiran Yesu Kristi. Hakan ya faru ne a ranar Bikin Fentakos, kuma waɗannan baƙin sun zo Urushalima ne daga wurare masu nisa kamar ƙasar Roma da ke yamma da kuma ƙasar Fartiya da ke gabas. An ji jama’ar nan suna ta harsuna dabam-dabam. Duk da haka, yawancin almajiran Yesu da ke tattaunawa da su ’yan Galili ne. Wasu cikin baƙin da ke cike da mamaki sun yi wannan tambayar: “Ƙaƙa fa muna ji, kowane mutum da namu harshe inda aka haife mu?”—A. M. 2:8.
Manzo Bitrus ya tashi tsaye kuma ya bayyana dalilin mu’ujizar da suke gani. Nan da nan suka yi na’am da abin da ya ce. Kuma dubban mutane ne aka yi wa baftisma! (A. M. 2:41) Ko da yake ikilisiyar ta sami ƙaruwa sosai, ta ci gaba da kasancewa da haɗin kai. “Taron waɗanda suka bada gaskiya zuciyarsu da ransu kuma ɗaya ne,” in ji Luka marubucin Littafi Mai Tsarki.—A. M. 4:32.
Dubban da suka yi baftisma a ranar Fentakos ta shekera ta 33 A.Z. suna son su ɗan daɗa zama a Urushalima don su ƙara koya game da imaninsu. Amma ba su zo da shirin yin hakan ba. Saboda haka, an ɗan karɓi gudummuwar kuɗi. Wasu cikin masu bi sun sayar da dukiyoyinsu da son rai kuma suka kawo kuɗin ga manzanni don a raba wa mabukata. (A. M. 2:42-47) Waɗannan ’yan’uwan sun nuna halin ƙauna da karimci!
Kiristoci na gaskiya suna nuna irin wannan ƙauna da karimci a kowane lokaci. A yau, ikilisiyar Kirista tana ci gaba da bauta wa Jehobah da ‘zuciya da rai ɗaya.’ Kowanne Kirista na ba da lokacinsa, ƙarfinsa, da kuɗinsa wajen wa’azin bishara da kuma faɗaɗa al’amuran Mulkin Allah.—Ka duba akwatin nan “Hanyoyin da Wasu Suka Zaɓi Su ba da Gudummuwa.”
[Akwati a shafi nas 6, 7]
HANYOYIN DA WASU SUKA ZAƁI SU BA DA
GUDUMMAWA GA AIKIN WA’AZI NA DUKAN DUNIYA
Yawanci suna keɓe kuɗin da za su riƙa sakawa a cikin akwatunan da aka rubuta “Worldwide Work.”
A kowane wata, ikilisiyoyi suna aika waɗannan kuɗaɗen zuwa ofishin reshe na Shaidun Jehobah da ke kula da ƙasar da suke. Kuna iya aika gudummawa kai tsaye zuwa ofishin reshe da ke kula da ƙasarku. Idan kuna son ku aika mana cek, ku rubuta “Watch Tower” a kai don mu sami kuɗin. Kuna iya ba da gudummawar ɗan kunne da sarƙa masu tsada ko dukiyoyi. Ku rubuta ’yar gajerar wasiƙar da za ta nuna cewa waɗannan abubuwan gudummawa ne.
HANYOYIN BA DA GUDUMMAWA
Ƙari ga ba da kyautar kuɗi, akwai wasu hanyoyin ba da kyauta da za su amfane hidimar Mulki a dukan duniya. Su ne:
Inshora: Kuna iya rubuta sunan Watch Tower a matsayin wanda zai karɓi inshorar rai ko na murabus ko fansho.
Ajiyar Banki: Kuna iya ba da kuɗin da kuke da shi a banki, ko wanda kuka ajiye na ƙayyadadden lokaci (fixed deposit), ko kuma kuɗin da aka ba ku bayan kun yi murabus da kuka ajiye a banki ga Watch Tower don su yi amfani da shi, ko kuma ku ce a ba su kuɗin bayan mutuwa, bisa ga bukatun bankin.
Hannayen Jari: Ana iya ba da gudummawar hannayen jari ga Watch Tower a matsayin kyauta.
Fegi da Gida: Kuna iya yi wa Watch Tower kyautar fegin da za a iya sayarwa, idan kuma gida ne da mutum yake ciki, mutumin yana iya ci gaba da zama a ciki yayin da yake da rai. Ku gaya wa ofishin reshen da ke ƙasarku kafin ku yi kyauta da gidan ko fegin.
Wasiyya da Ajiya: Ana iya ba Watch Tower dukiya ko kuɗi a matsayin gado bayan mutuwa ta hanyar takardar da aka saka hannu a ƙarƙashin doka, ko kuma a rubuta Watch Tower a matsayin wanda zai ci amfanin ajiyar da aka yi.
Irin waɗannan hanyoyin ba da gudummawa da muka ambata suna bukatar mai yin su ya yi shiri sosai.
Don ƙarin bayani, kuna iya rubuta wasiƙa ko ku kira Ofishin Reshe na Shaidun Jehobah a adireshin da ke ƙasa ko kuwa ku tuntuɓi ofishin reshe da ke kula da ƙasarku.
Jehovah’s Witnesses
P.M.B 1090,
Benin City 300001,
Edo State, Nigeria.
Tarho: (052) 202020