‘Bari Mu Kawo Baiko ga Jehobah’
SA’AD da wani ya nuna maka alheri, yaya za ka nuna masa godiya? Ka yi la’akari da yadda shugabannin yaƙi na Isra’ila suka nuna godiya bayan da suka yi yaƙi da Midiyanawa. An yi yaƙin ne bayan da Isra’lawa suka yi zunubi da ke dangane da Baal na Peor. Allah ya sa mutanensa su yi nasara, kuma aka rarraba ganimar yaƙin tsakanin sojoji dubu goma sha biyu da sauran Isra’ilawa. Bisa ga ja-gorar Jehobah, sojojin suka ba da sashen rabonsu ga firistoci, sauran Isra’ilawa kuma suka ba da nasu ga Lawiyawa.—Lit. Lis. 31:1-5, 25-30.
Amma, shugabannin yaƙin sun so su yi fiye da hakan. “Bayinka sun lissafta jimlar mutanen yaƙi da su ke a hannunmu, ba ko ɗaya kuwa da ya saraya a cikinmu,” suka faɗa wa Musa. A matsayin hadaya ga Jehobah, suka shawarta su miƙa zinariya da kuma kayan ado dabam dabam. Adadin nauyin kayan zinariyar sun kai kilo ɗari da casa’in.—Num. 31:49-54.
A yau, haka ma mutane da yawa suna nuna godiya ga abin da Jehobah ya yi musu. Ƙari ga haka, ba bayin Jehobah da suka keɓe kai kaɗai ba ne suke nuna irin wannan godiya ba. Alal misali, ka yi la’akari da wani direban bas da yake kai da kuma dawo da wasu rukunin masu halartan taron ƙasashe da aka yi a filin wasa a birnin Bologna da ke ƙasar Italiya, a shekara ta 2009. Tun da yake shi direba mai hankali ne sosai, waɗanda suka shiga motarsa sun tsai da shawara su rubuta masa wasiƙar godiya da kyautar kuɗi tare da littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? Saboda haka direban ya ce: “Na yi farin cikin karɓan katin da littafin, amma na mayar da kuɗin saboda ina son in ba da gudummawa don ku ci gaba da aikin da kuke yi. Ko da yake ni ba Mashaidin Jehobah ba ne, ina son in ba da wannan kuɗin don na ga cewa ƙauna ce take motsa ku ku yi abubuwa.”
Sa’ad da kuke nuna godiya ga abin da Jehobah ya yi muku, hanya ɗaya da za ku nuna godiyarku ita ce ta wajen ba da gudummawa don aikin da Shaidun Jehobah suke yi a dukan duniya. (Mat. 24:14) An tsara hanyoyin da wasu suka zaɓa su ba da gudummawa a cikin akwati da ke cikin wannan talifin.
[Akwati da ke shafi na 20, 21]
HANYOYIN DA WASU SUKA ZAƁI SU BA DA
GUDUMMAWA GA AIKIN WA’AZI NA DUKAN DUNIYA
Yawanci suna keɓe kuɗin da za su riƙa sakawa a cikin akwatunan da aka rubuta “Worldwide Work.”
A kowane wata, ikilisiyoyi suna aika waɗannan kuɗaɗen zuwa ofishin reshe na Shaidun Jehobah da ke kula da ƙasar da suke. Kuna iya aika gudummawa kai tsaye zuwa ofishin reshe da ke kula da ƙasarku. Idan kuna son ku aika mana cek, ku rubuta “Watch Tower” a kai don mu sami kuɗin. Kuna iya ba da gudummawar ɗan kunne da sarƙa masu tsada ko dukiyoyi. Ku rubuta ’yar gajerar wasiƙar da za ta nuna cewa waɗannan abubuwan gudummawa ne.
HANYOYIN BA DA GUDUMMAWA
Ƙari ga ba da kyautar kuɗi, akwai wasu hanyoyin ba da kyauta da za su amfane hidimar Mulki a dukan duniya. Su ne:
Inshora: Kuna iya rubuta sunan Watch Tower a matsayin wanda zai karɓi inshorar rai ko na murabus ko fansho.
Ajiyar Banki: Kuna iya ba da kuɗin da kuke da shi a banki, ko wanda kuka ajiye na ƙayyadadden lokaci (fixed deposit), ko kuma kuɗin da aka ba ku bayan kun yi murabus da kuka ajiye a banki ga Watch Tower don su yi amfani da shi, ko kuma ku ce a ba su kuɗin bayan mutuwa, bisa ga bukatun bankin.
Hannayen Jari: Ana iya ba da gudummawar hannayen jari ga Watch Tower a matsayin kyauta.
Fegi da Gida: Kuna iya yi wa Watch Tower kyautar fegin da za a iya sayarwa, idan kuma gida ne da mutum yake ciki, mutumin yana iya ci gaba da zama a ciki yayin da yake da rai. Ku gaya wa ofishin reshen da ke ƙasarku kafin ku yi kyauta da gidan ko fegin.
Wasiyya da Ajiya: Ana iya ba Watch Tower dukiya ko kuɗi a matsayin gado bayan mutuwa ta hanyar takardar da aka saka hannu a ƙarƙashin doka, ko kuma a rubuta Watch Tower a matsayin wanda zai ci amfanin ajiyar da aka yi. Irin waɗannan hanyoyin ba da gudummawa da muka ambata suna bukatar mai yin su ya yi shiri sosai.
Don ƙarin bayani, kuna iya rubuta wasiƙa ko ku kira Ofishin Reshe na Shaidun Jehobah a adireshin da ke ƙasa ko kuwa ku tuntuɓi ofishin reshe da ke kula da ƙasarku.
Jehovah’s Witnesses
P.M.B 1090,
Benin City 300001,
Edo State, Nigeria.
Tarho: 07080662020