Kana Farin Ciki da Gatar Yin “Alheri”?
AN SAN Kiristoci na ƙarni na farko a Filibi da ba da kyauta don tallafa wa bauta ta gaskiya. Sa’ad da manzo Bulus yake rubuta hurarriyar wasiƙarsa ga waɗannan Kiristocin, ya ce: “Ina gode ma Allahna yayin da nake tuna da ku duka, kullayaumi cikin kowace addu’ata dominku duka ina yin addu’ata da farinciki, saboda tarayyarku cikin yaɗuwar bishara tun daga rana ta fari har wa yau.” (Filib. 1:3-5) Bulus ya tuna sarai sa’ad da Lidiya da iyalinta suka yi baftisma kuma ta nuna musu karimci, ta wajen nacewa don Bulus da abokan wa’azinsa su zauna a gidanta.—A. M.16:14, 15.
Ba da daɗewa ba bayan wannan lokacin, sabuwar ikilisiyar da aka kafa a Filibi ta aikawa Bulus kayayyaki sau biyu sa’ad da ya yi makonni tare da ’yan’uwansa a Tasalonika, da ke da nisa kusan mil 100 daga wurin. (Filib. 4:15, 16) ’Yan shekaru bayan hakan, sa’ad da ’yan’uwan da ke Filibi da Makidoniya suke fuskantar mawuyacin yanayi da kuma ‘talauci ainun,’ sun samu labari game da bukatun Kiristocin da ke Urushalima da ake tsananta musu kuma sun yi ɗokin taimaka musu. Bulus ya faɗa cewa lallai hakan yana “gaba da ikonsu.” Duk da haka, ya rubuta: “Da naciya mai-yawa suna roƙonmu a yarda masu wannan alheri.”—2 Kor. 8:1-4; Rom. 15:26.
Kusan shekara goma bayan Filibiyawa suka zama Kiristoci, sun ci gaba da nuna wannan halin alheri. Sa’ad da suka samu labari cewa Bulus yana kurkuku a ƙasar Roma, suka aiki Abafroditus ya yi tafiya a ƙasa da kuma ta teku mai nisan mil 800 don ya kai wa manzon kayayyaki. Hakika, Filibiyawa suna son su ba Bulus kayayyaki don ya ci gaba da ƙarfafa ’yan’uwan da kuma yin wa’azi, ko da yana cikin kurkuku.—Filib. 1:12-14; 2:25-30; 4:18.
A yau, Kiristoci na gaskiya suna ɗaukan ingancin tallafa wa aikin wa’azin Mulki da kuma almajirtarwa a matsayin gata. (Mat. 28:19, 20) Suna tallafa wa abubuwan Mulki ta ba da lokacinsu da ƙoƙarinsu da kuma kuɗaɗensu. Akwatin da ke ƙasa ya nuna wasu hanyoyin da za ka iya saka hannu wajen tallafa wa wannan aikin wa’azi.
[Akwati a shafi na 22]
Hanyoyin Da Wasu Suka Zaɓi Su Ba da
GUDUMMAWA GA AIKIN WA’AZI NA DUKAN DUNIYA
Yawanci suna keɓe kuɗin da za su riƙa sakawa a cikin akwatunan da aka rubuta “Worldwide Work.”
A kowane wata, ikilisiyoyi suna aika waɗannan kuɗaɗen zuwa ofishin reshe na Shaidun Jehobah da ke kula da ƙasar da suke. Kuna iya aika gudummawa kai tsaye zuwa ofishin reshe na Shaidun Jehobah da ke kula da ƙasarku. Idan kuna son ku aika mana cek, ku rubuta “Watch Tower” da kalmomi biyu. Kuna iya ba da gudummawar ɗan kunne da sarƙa masu tsada ko dukiyoyi. Ku rubuta ’yar gajerar wasiƙar da za ta nuna cewa waɗannan abubuwan gudummawa ne.
HANYOYIN BA DA GUDUMMAWA
Ƙari ga ba da kyautar kuɗi, akwai wasu hanyoyin ba da kyauta da za su amfane hidimar Mulki a dukan duniya. Su ne:
Inshora: Kuna iya rubuta sunan Watch Tower a matsayin wanda zai karɓi inshorar rai ko na murabus ko fansho.
Ajiyar Banki: Kuna iya ba da kuɗin da kuke da shi a banki, ko wanda kuka ajiye na ƙayyadadden lokaci (fixed deposit), ko kuma kuɗin da aka ba ku bayan kun yi murabus da kuka ajiye a banki ga Watch Tower don su yi amfani da shi, ko kuma ku ce a ba su kuɗin bayan mutuwa, bisa ga bukatun bankin.
Hannayen Jari: Ana iya ba da gudummawar hannayen jari ga Watch Tower a matsayin kyauta.
Fegi da Gida: Kuna iya yi wa Watch Tower kyautar fegin da za a iya sayarwa, idan kuma gida ne da mutum yake ciki, mutumin yana iya ci gaba da zama a ciki yayin da yake da rai. Ku gaya wa ofishin reshen da ke ƙasarku kafin ku yi kyauta da gidan ko fegin.
Wasiyya da Ajiya: Ana iya ba Watch Tower dukiya ko kuɗi a matsayin gado bayan mutuwa ta hanyar takardar da aka saka hannu a ƙarƙashin doka, ko kuma a rubuta Watch Tower a matsayin wanda zai ci amfanin ajiyar da aka yi. Irin waɗannan hanyoyin ba da gudummawa da muka ambata suna bukatar mai yin su ya yi shiri sosai.
Don ƙarin bayani, kuna iya rubuta wasiƙa ko ku kira Ofishin Reshe na Shaidun Jehobah a adireshin da ke ƙasa ko kuwa ku tuntuɓi ofishin reshe da ke kula da ƙasarku.
Jehovah’s Witnesses
P.M.B 1090,
Benin City 300001,
Edo State, Nigeria.
Tarho: 07080662020