Yalwarsu ta Biya Bukatar Wasu
A SHEKARA ta 49 a zamaninmu, Bitrus da Yaƙub da Yohanna waɗanda ana ɗaukansu “jigajigai,” sun tura manzo Bulus da Barnaba su yi wani aiki. Sun ce su riƙa kula da Kiristoci talakawa sa’ad da suke wa’azi ga al’ummai. (Gal. 2:9, 10) Ta yaya suka yi wannan aikin?
Bulus ya nuna yadda ya ɗauki wannan aikin a wasiƙarsa. Alal misali, ga abin da ya rubuta wa Kiristoci da ke Korinti: ‘Zancen tattarawan kuɗi fa domin tsarkaka, kamar yadda na yi wasici ga ekklisiyai na Galatiya, haka kuma sai ku yi. A kan rana ta fari ga bakwai kowane a cikinku shi ajiye ajiya, gwargwadon samuwa da ya ke yi, domin kada a yi ta tattarawa sa’anda na zo. Kuma sa’anda na zo, waɗanda kuka yarda da su zan aike su da wasiƙu su kai kyautarku Urushalima.”—1 Kor. 16:1-3.
A wasiƙarsa ta biyu ga Korintiyawa, Bulus ya sake gaya musu dalilin da ya sa ake tara gudummawar. Ya ce domin “yalwarku yanzu a wannan loto ta zama gudummawa ga nasu bukata.”—2 Kor. 8:12-15.
Sa’ad da Bulus ya rubuta wasiƙa zuwa ga Kiristocin da ke ƙasar Roma a shekara ta 56 a zamaninmu, Kiristoci da ke Koranti sun kusan kammala tattara gudummawarsu. Ya ce: “Tafiya na ke yi zuwa Urushalima, garin yi wa tsarkaka hidima. Gama su Makidoniya da Akaya suka ga ya yi kyau a yi wani taimako zuwa bukatar matalauta a cikin tsarkaka waɗanda ke a Urushalima.” (Rom. 15:25, 26) Bulus ya yi aikin nan da nan. Shi ya sa sa’ad da aka kama shi, ya ce wa Felix Gwamnar ƙasar Roma: “Na taho garin in kawo sadakoki wurin al’ummata, da bayebaye.”—A. M. 24:17.
Abin da Bulus ya faɗa game da Kiristocin da ke ƙasar Makidoniya ya nuna halin da Kiristoci na ƙarni na farko suke da shi. Ya ce, “Suna roƙonmu a yarda masu wannan alheri.” Manzo Bulus ya ƙarfafa Korintiyawa su bi wannan misalin. Ya ce musu: “Kowane mutum ya aika bisa yadda ya annita a zuciyarsa; ba da cicijewa ba, ba kuwa kamar ta dole ba: gama Allah yana son mai-bayarwa da daɗin rai.” Me ya sa waɗannan ikilisiyoyin suka ba da gudummawar? Ba don suna son su “biya bukatan tsarkaka kaɗai ba, amma yana yalwata kuma ta wurin godiya mai-yawa zuwa ga Allah.” (2 Kor. 8:4; 9:7, 12) Wataƙila mu ma abin da ke motsa mu mu ba da gudummawa ke nan. Babu shakka, Jehobah zai yi wa duk wanda yake da irin wannan hali na rashin son kai albarka, kuma albarkarsa tana sa mutum ya zama mawadaci.—Mis. 10:22.
[Akwati a shafi na 9]
HANYOYIN DA WASU SUKE BA DA GUDUMMAWA DON WA’AZI
Ta wajen yin koyi da mutanen da ke zamanin Bulus, a yau wasu suna “ajiya” ko kuma su keɓe kuɗi da za su riƙa sakawa a cikin akwatin da aka rubuta “Worldwide Work” (Aiki na Dukan Duniya) da ke ikilisiyarsu. (1 Kor. 16:2) A kowane wata, ikilisiyoyi suna aika wannan gudummawar zuwa ofishin reshe na Shaidun Jehobah da ke kula da ƙasarsu. Kana iya aika gudummawarka kai tsaye zuwa ofishin Shaidun Jehobah da ke ƙasarku. Idan kana son ka san sunan da Shaidun Jehobah suke amfani da shi a ƙasarku, ka tuntuɓi ofishin reshe na ƙasarku. Kana iya samun adireshin ofishin reshe a Yanar gizon www.pr418.com/contact. Ga irin gudummawar da za ka iya aikawa kai tsaye:
KYAUTA
• Ba da kyautar kuɗi ko kayan ado ko kuma wasu kaya masu amfani.
• A haɗa da wasiƙar da ke nuna cewa kuɗin ko kuma kayan kyauta ce aka bayar.
RANCE
• Ba da rancen kuɗi da za a iya mai da wa duk sa’ad da mai ba da rancen yake bukata.
• A haɗa da wasiƙar da ke nuna cewa kuɗin rance ne aka ba da.
HANYOYIN BA DA GUDUMMAWA
Ƙari ga ba da kyautar kuɗi da kaya masu amfani, akwai wasu hanyoyin ba da kyauta da za su amfane hidimar Mulki a dukan duniya. Kafin ka zaɓa wata hanyar ba da gudummawa, ka fara tuntuɓar ofishin reshe da ke kula da ƙasarku don ya gaya maka hanyar da ta dace da ƙasarku. Tun da yake dokokin ƙasashe sun bambanta, yana da muhimmanci ka fara tuntuɓar lauya kafin ka tsai da shawara a kan yadda za ka ba da gudummawa. An jera waɗannan hanyoyin a ƙasa.
Inshora: Kana iya rubuta sunan Watch Tower a matsayin wanda zai karɓi inshorar rai ko na murabus ko fansho.
Ajiyar Banki: Kana iya ba da kuɗin da kake da shi a banki, ko wanda ka ajiye na ƙayyadadden lokaci (fixed deposit), ko kuma kuɗin da aka ba ka bayan ka yi murabus da ka ajiye a banki ga Watch Tower don su yi amfani da shi. Kana kuma iya ce a ba su kuɗin bayan ka rasu, bisa ga dokokin bankin.
Hannayen Jari: Ana iya ba Watch Tower kyautar hannayen jari ko kuma a ce a ba su bayan mai shi ya rasu (Transfer on Death agreement).
Fegi da Gida: Kana iya yi wa Watch Tower kyautar fegin da za a iya sayarwa, idan kuma gida ne da mutum yake ciki, mutumin yana iya ci gaba da zama a ciki yayin da yake da rai.
Wasiyya da Ajiya: Ana iya ba Watch Tower dukiya ko kuɗi a matsayin gādo bayan mutuwa, ta hanyar rubuta takardar da aka saka hannu bisa doka, ko kuma a rubuta Watch Tower a matsayin wanda zai ci amfanin ajiyar da aka yi.
Irin waɗannan hanyoyin ba da gudummawa da muka ambata suna bukatar mai yin su ya yi shiri sosai.
Don ƙarin bayani, kana iya rubuta wasiƙa ko ka kira ofishin reshe na Shaidun Jehobah ta adireshin da ke ƙasa ko kuwa ka tuntuɓi ofishin reshe da ke kula da ƙasarku.
JEHOVAH’S WITNESSES
P.M.B 1090,
Benin City 300001,
Edo State, Nigeria.
Tarho: 07080662020