Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w15 11/15 pp. 14-15
  • Ka Rika Godiya ga Jehobah, Allah Mai Karimci

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Rika Godiya ga Jehobah, Allah Mai Karimci
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • BABU MAI KARIMCI KAMAR JEHOBAH
  • ‘Aikin Kuwa da Girma’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2016
  • Yalwarsu ta Biya Bukatar Wasu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Jehobah Yana Albarkar Masu Son Bayarwa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Ta Yaya Za Ka Iya Biyan Bukatun Wasu?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
w15 11/15 pp. 14-15
Wata mata tana saka katin ATM a cikin wata na’ura

Ka Riƙa Godiya ga Jehobah, ALLAH MAI KARIMCI

JEHOBAH ALLAH mai karimci ne. (Yaƙ. 1:17) Taurari da ke ko’ina a sararin sama da itatuwa da tsire-tsire da Allah ya halitta a duniya sun nuna cewa shi mai karimci ne.—Zab. 65:12, 13; 147:7, 8; 148:3, 4.

Marubucin zabura ya nuna godiya ga Jehobah wanda ya halicci kome kuma ya rera waƙa don ya ɗaukaka shi. Ka karanta Zabura ta 104 don kai ma ka ga yadda Jehobah ya cancanci ɗaukaka. Marubucin zabura ya ce: “Zan raira [waƙa] ga Ubangiji muddar raina. Zan raira yabo ga Allahna muddar akwai ni.” (Zab. 104:33) Babu shakka, kai ma kana da wannan burin.

BABU MAI KARIMCI KAMAR JEHOBAH

Jehobah yana so mu yi koyi da shi a nuna karimci. Ƙari ga haka, ya bayyana dalilin da ya sa ya kamata mu kasance masu bayarwa sa’ad da ya ja-goranci manzo Bulus da ruhu mai tsarki ya rubuta cewa: “Ka dokace waɗanda ke mawadata cikin wannan zamani na yanzu, kada su yi girman kai, kada su ratayi begensu bisa wadata marar-tsayawa, amma bisa Allah, wanda ke ba mu kome a yalwace mu ji daɗinsu; su yi alheri, su zama mawadata cikin kyawawan ayyuka, su kasance da niyyar bayarwa, masu son zumunta; suna ajiye wa kansu tushe mai kyau domin lokaci mai zuwa, da za su ruski rai wanda yake hakikanin rai.”—1 Tim. 6:17-19.

Sa’ad da manzo Bulus ya rubuta wasiƙarsa ta biyu zuwa ga ikilisiyar da ke Korinti, ya ƙarfafa ’yan’uwa su kasance da kyakkyawar anniya sa’ad da suke bayarwa. Bulus ya ce: “Kowane mutum ya aika bisa yadda ya annita a zuciyarsa; ba da cicijewa ba, ba kuwa kamar ta dole ba: gama Allah yana son mai-bayarwa da daɗin rai.” (2 Kor. 9:7) Bayan haka, Bulus ya ambaci waɗanda suke amfana daga halin bayarwa. Na ɗaya, masu karɓa don Allah yana biyan bukatun su ta hakan. Na biyu Allah yana yi wa masu bayarwa albarkar don karimcinsu.—2 Kor. 9:11-14.

Sa’ad da Bulus yake kammala sura 8 da 9 na wannan wasiƙarsa, ya ambaci dalilin da ya nuna cewa Allah shi ne babban mai karimci. Ya ce: “Godiya ga Allah domin kyautarsa wadda ta fi gaban magana.” (2 Kor. 9:15) Kyautar da Jehobah yake bayarwa ya haɗa da dukan alherin da ya nuna ga bayinsa ta wurin Yesu Kristi. Darajar wannan kyautar ta wuce misali.

Ta yaya za mu nuna godiya don dukan abubuwan da Jehobah da Ɗansa suka yi mana da kuma waɗanda za su yi a nan gaba? Hanya ɗaya ita ce ta ba da lokacinmu da kuzarinmu da kuma wasu dukiyarmu don a sami ci gaba a yin wa’azin bishara da kuma wasu ayyuka na ƙungiyar Jehobah, ko da gudummawar da za mu iya yi kaɗan ko da yawa.—1 Laba. 22:14; 29:3-5; Luk. 21:1-4.

Hanyoyin Da Wasu Suke Ba Da Gudummawa Don Wa’azi

A yau, kamar a zamanin manzo Bulus, mutane da yawa suna yin “ajiya” ko kuma su ajiye wani kuɗi da za su riƙa sakawa a cikin akwatunan gudummawa da ke cikin ikilisiya da aka rubuta “Aiki na Dukan Duniya.” (1 Kor. 16:2) Kowane wata, ikilisiyoyi suna tura waɗannan gudummawan zuwa ofishin Shaidun Jehobah da ke ƙasarsu. Kana iya aika gudummawarka kai tsaye zuwa ofishin Shaidun Jehobah da ke ƙasarku. Idan kana son ka san sunan da Shaidun Jehobah suke amfani da shi a ƙasarku, ka tuntuɓi ofishinsu da ke ƙasarku. Kana iya samun adireshin ofishin Shaidun Jehobah a dandalin www.pr418.com/ha. Ga irin gudummawar da za ka iya aikawa kai tsaye:

KYAUTA

  • Gudummawa ta hanyar tura kuɗi ta banki ko kuma wajen amfani da katin ATM. A wasu ofisoshin Shaidun Jehobah, ana iya yin hakan ta jw.org ko kuma wani dandalin da aka umurta a yi amfani da shi.

  • Kuɗi ko kayan ado kamar gwalagwalai ko kuma wasu kaya masu daraja. A haɗa da wasiƙar da ke nuna cewa kuɗin ko kuma kayayyakin kyauta ne.

RANCE

  • Za a iya ba da rancen kuɗi kuma ana iya mayar wa mai shi kuɗin a duk lokacin da yake bukata.

  • A haɗa da wasiƙar da ke nuna cewa kuɗin rance ne.

WASU HANYOYIN BA DA GUDUMMAWA

Ƙari ga ba da kyautar kuɗi da kaya masu amfani, akwai wasu hanyoyin ba da kyauta da za su amfane wa’azin bishara ta Mulki a dukan duniya. Kafin ka zaɓa wata hanyar ba da gudummawa, ka fara tuntuɓar ofishin Shaidun Jehobah da ke ƙasarku don neman bayani game da tsarin da ya dace a ƙasarku. Tun da yake dokokin sun dangana ga ƙasarku, yana da muhimmanci ka fara tuntuɓar lauya kafin ka tsai da shawara a kan yadda za ka ba da gudummawa. An jera waɗannan hanyoyin a ƙasa.

Inshora: Kana iya rubuta sunan “Watch Tower” a matsayin wanda zai karɓi inshorar rai ko na murabus daga aiki ko kuma fansho.

Ajiyar Banki: Kana iya ba da kuɗin da kake da shi a banki, ko wanda ka ajiye na ƙayyadadden lokaci (fixed deposit), ko kuma kuɗin da aka ba ka bayan ka yi murabus daga aiki da ka ajiye a banki ga “Watch Tower” don su yi amfani da shi. Kana kuma iya ce a ba su kuɗin bayan ka rasu, bisa ga dokokin bankin.

Hannayen Jari: Ana iya ba “Watch Tower” kyautar hannayen jari ko kuma a yi yarjejeniya cewa za a ba su bayan mai shi ya rasu (Transfer on Death).

Fegi da Gida: Kana iya yi wa “Watch Tower” kyautar fegin da za a iya sayarwa, idan kuma gida ne da mutum yake ciki, yana iya ci gaba da zama a ciki yayin da yake da rai.

Wasiyya da Ajiya: Ana iya ba “Watch Tower” dukiya ko kuɗi a matsayin gādo bayan mutuwa, ta hanyar rubuta takardar da aka saka hannu bisa doka, ko kuma a rubuta “Watch Tower” a matsayin wanda zai ci moriyar ajiyar.

Ya dace a yi shiri da kyau don ba da irin waɗannan gudummawa da aka ambata.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba