Ta Yaya Za Ka Iya Biyan Bukatun Wasu?
WANI dattijo mai suna François da ke zama a wata ƙasa da ke tasowa, ya ce: “Sa’ad da aka yi hargitsi a sakamakon wani siyasa da aka yi, dubban Shaidun Jehobah sun gudu sun bar gidajensu. An yi karancin abinci da magani kuma abubuwa sun yi tsada sosai. Bankuna sun daina aiki kuma babu kuɗi a na’urar cirar kuɗi, wato ATM, wasunsu ma sun daina aiki gaba ɗaya.”
Sai ’yan’uwa da suke ofishin reshe suka soma kai kuɗaɗe da abinci ga waɗannan ’yan’uwa da suka bar gidajensu suka koma zama a Majami’un Mulki da ke ƙasar baƙi ɗaya. Wasu rukunin ’yan adawa suka tattare hanyoyi, amma da yake sun san cewa Shaidun Jehobah ba sa saka hannu a siyasa, sukan bar motocin ofishin reshen su wuce.
François ya ce: “Wata rana da za mu wata Majami’ar Mulki, sai ’yan bindiga-daɗi suka soma harbin motarmu, amma ruwan harsashin bai taɓa mu ba. Da muka gan wani soja yana bin mu da makami a hannunsa, sai muka ja birki muka juya da wuri muka koma ofishin reshe. Amma mun gode wa Jehobah domin ba mu mutu ba. Washegari, ’yan’uwa 130 da suke wannan Majami’ar Mulkin suka bar wurin zuwa inda babu matsala. Wasun su sun zo ofishin reshen kuma mun kula da su har hargitsin ya kwanta.”
François ya daɗa da cewa: “Daga baya, ’yan’uwa daga ɓangarori dabam-dabam na ƙasar sun aika wasiƙu zuwa ofishin reshen don nuna godiya ga taimakon da aka yi musu. Kuma yadda ’yan’uwa daga wasu wurare suka taimaka musu ya sa sun daɗa dogara ga Jehobah.”
Sa’ad da bala’i ya auko wa ’yan’uwanmu maza da mata, ba zai dace mu ce musu “ku ji ɗumi, ku ƙoshi” ba. (Yaƙ. 2:15, 16) Maimakon haka, zai dace mu yi ƙoƙari mu tanadar musu da bukatunsu. Hakazalika, bayan da aka yi kashedi a ƙarni na farko cewa za a yi yunwa, sai kowane almajiran “gwargwadon abin da ya iya, suka ƙudurta su aike gudummawa ga ’yan’uwa da ke zaune cikin Yahudiya.”—A. M. 11:28-30.
Mutane suna bukatar su ji Kalmar Allah. (Mat. 5:3) Saboda haka, a matsayinmu na bayin Jehobah, muna marmarin taimaka musu su biya bukatansu. Amma ta yaya za mu iya yin hakan? Ta wajen bin umurnin da Yesu ya ba mabiyansa cewa su yi wa’azi. (Mat. 28:19, 20) Kowannenmu yana yin amfani da lokacinsa da kuzarinsa da kuma abin da yake da shi don ya bi wannan umurnin. A matsayin ƙungiya, muna amfani da wasu cikin kuɗaɗen da aka yi gudummawa don taimaka wa mutane, amma gudummawar musamman don faɗaɗa ayyukan Mulkin Allah da kuma yin wa’azi ne. Ta hakan muke nuna cewa muna ƙaunar Allah da kuma maƙwabtanmu.—Mat. 22:37-39.
Waɗanda suke tallafa wa aikin Shaidun Jehobah a dukan duniya za su iya tabbata cewa ana yin amfani da gudummawarsu a hanya mai kyau. Shin za ka iya taimaka wa ’yan’uwanka idan suna da bukata? Shin kana so ka tallafa wa aikin almajirtarwa? Idan haka ne, to “kada ka hana alheri ga waɗanda ya wajibce su, lokacin da yana cikin ikon hannunka da za ka aika.”—Mis. 3:27.