Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w16 Nuwamba pp. 19-20
  • ‘Aikin Kuwa da Girma’

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • ‘Aikin Kuwa da Girma’
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2016
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Rika Godiya ga Jehobah, Allah Mai Karimci
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
  • Jehobah Yana Albarkar Masu Son Bayarwa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Yalwarsu ta Biya Bukatar Wasu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Ta Yaya Za Ka Iya Biyan Bukatun Wasu?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2016
w16 Nuwamba pp. 19-20
Sarki Dauda yana nuna wa wani mutum zanen yadda za a gina haikalin; wani dan’uwan yana duba zanen wani gini

‘Aikin Kuwa da Girma’

LOKACI ya yi da za a yi wata babban taro mai muhimmanci a Urushalima. Sarki Dauda ya tattara dukan hakiman Isra’ila da shugabanni da dukan jarumai. Kuma sun ji daɗin sanarwar da aka yi. Jehobah ya ba wa Sulemanu, ɗan Dauda izinin yin wani babban ginin da za a keɓe don bauta wa Allah na gaskiya. Sarkin Isra’ila ne aka hure ya san yadda tsarin ginin zai kasance, kuma ya gaya wa Sulemanu yadda zai yi ginin. Dauda ya ce, “aiki kuwa da girma: gama haikalin ba domin mutum ba ne, amma domin Ubangiji Allah ne.”​—1 Laba. 28:​1, 2, 6, 11, 12; 29:1.

Bayan haka, Dauda ya yi tambaya cewa: “Wanene fa za ya bayar da yardan rai, shi cika hannunsa yau ga Ubangiji?” (1 Laba. 29:⁠5) Da a ce kana wurin, mene ne za ka yi? Za ka so ka taimaka don a yi wannan aiki mai girma? Nan da nan Isra’ilawan suka ɗauki mataki. Kuma “suka yi murna, da shi ke sun bayar da yardan ransu, da sahihiyar zuciya suka yi baiko ga Ubangiji da yardan rai.”​—1 Laba. 29:⁠9.

Ƙarnuka bayan haka, Jehobah ya kafa wani abin da ya fi haikalin nan muhimmanci. Jehobah ya kafa haikali na alama, shiri ne da ya yi don ‘yan Adam su kusace shi bisa fansar Yesu. (Ibran. 9:​11, 12) Ta yaya Jehobah yake taimaka wa mutane su sulhunta da shi a yau? Yana yin hakan ta wa’azi da muke yi. (Mat. 28:​19, 20) Saboda wannan aikin, kowace shekara miliyoyin mutane suna yin nazarin Littafi Mai Tsarki, kuma da yawa suna yin baftisma. Ƙari ga haka, ana kafa ikilisiyoyi da yawa.

Saboda irin wannan ci gaba, ana bukatar a daɗa buga littattafan da ke bayyana Littafi Mai Tsarki, da gina Majami’un Mulki da kula da su, kuma ana bukatar wajen da za a riƙa yin manyan taro. Shin ka yarda cewa wa’azin da muke yi, aiki ne mai muhimmanci kuma ana samun ci gaba sosai?​—Mat. 24:14.

Ƙaunar da muke wa Allah da maƙwabtanmu da kuma sanin muhimmancin wa’azi su ne suke sa mutanen Allah suke ba da gudummawa da yardan rai. Abin farin ciki ne mu riƙa ‘girmama Ubangiji da wadatarmu,’ kuma mu ga yadda ake amfani da shi da kyau don a yi aikin da ya fi muhimmanci a duk tarihin ‘yan Adam!​—Mis. 3:9.

Hanyoyin Da Wasu Suke Ba Da Gudummawa Don Wa’azi

Mutane da yawa suna yin “ajiya” ko kuma su ajiye wani kuɗi da za su riƙa sakawa a cikin akwatunan gudummawa da ke cikin ikilisiya da aka rubuta “Aiki na Dukan Duniya.” (1 Kor. 16:⁠2) Kowane wata, ikilisiyoyi suna tura waɗannan gudummawan zuwa ofishin Shaidun Jehobah da ke ƙasarsu. Kana iya aika gudummawarka kai tsaye zuwa ofishin Shaidun Jehobah da ke ƙasarku. Idan kana son ka san sunan da Shaidun Jehobah suke amfani da shi a ƙasarku, ka tuntuɓi ofishinsu da ke ƙasarku. Kana iya samun adireshin ofishin Shaidun Jehobah a dandalin www.pr418.com/⁠ha. Ga irin gudummawar da za ka iya aikawa kai tsaye:

KYAUTA

  • Gudummawa ta hanyar tura kuɗi ta banki ko kuma wajen amfani da katin ATM. A wasu ofisoshin Shaidun Jehobah, ana iya yin hakan ta jw.org ko kuma wani dandalin da aka umurta a yi amfani da shi.

  • Kuɗi ko kayan ado kamar gwalagwalai ko kuma wasu kaya masu daraja. A haɗa da wasiƙar da ke nuna cewa kuɗin ko kuma kayayyakin kyauta ne.

RANCE

  • Za a iya ba da rancen kuɗi kuma ana iya mayar wa mai shi a duk lokacin da yake bukata.

  • A haɗa da wasiƙar da ke nuna cewa kuɗin rance ne.

WASU HANYOYIN BA DA GUDUMMAWA

Ƙari ga ba da kyautar kuɗi da kaya masu amfani, akwai wasu hanyoyin ba da kyauta da za su amfane wa’azin bishara ta Mulki a dukan duniya. Kafin ka zaɓa wata hanyar ba da gudummawa, ka fara tuntuɓar ofishin Shaidun Jehobah da ke ƙasarku don neman bayani game da tsarin da ya dace a ƙasarku. Tun da yake dokokin sun dangana ga ƙasarku, yana da muhimmanci ka fara tuntuɓar lauya kafin ka tsai da shawara a kan yadda za ka ba da gudummawa. An jera waɗannan hanyoyin a ƙasa.

Inshora: Kana iya rubuta sunan “Watch Tower” a matsayin wanda zai karɓi inshorar rai ko na murabus daga aiki ko kuma fansho.

Ajiyar Banki: Kana iya ba da kuɗin da kake da shi a banki, ko wanda ka ajiye na ƙayyadadden lokaci (fixed deposit), ko kuma kuɗin da aka ba ka bayan ka yi murabus daga aiki da ka ajiye a banki ga “Watch Tower” don su yi amfani da shi. Kana kuma iya ce a ba su kuɗin bayan ka rasu, bisa ga dokokin bankin.

Hannayen Jari: Ana iya ba “Watch Tower” kyautar hannayen jari ko kuma a yi yarjejeniya cewa za a ba su bayan mai shi ya rasu (Transfer on Death).

Fegi da Gida: Kana iya yi wa “Watch Tower” kyautar fegin da za a iya sayarwa, idan kuma gida ne da mutum yake ciki, yana iya ci gaba da zama a ciki yayin da yake da rai.

Wasiyya da Ajiya: Ana iya ba “Watch Tower” dukiya ko kuɗi a matsayin gādo bayan mutuwa, ta hanyar rubuta takardar da aka saka hannu bisa doka, ko kuma a rubuta “Watch Tower” a matsayin wanda zai ci moriyar ajiyar.

Ya dace a yi shiri da kyau don ba da irin waɗannan gudummawa da aka ambata.

Don ƙarin bayani, ka danna “Yadda Za Ka Ba da Gudummawa don Aiki Na Dukan Duniya” da ke shafin farko a dandalin jw.org/ha ko kuma ka tuntuɓi ofishin Shaidun Jehobah da ke ƙasarku.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba