Jehobah Yana Yi wa Masu Son Bayarwa Albarka
MAHALICCINMU ya ba ’yan Adam ’yancin yin abin da suke so. Duk da haka, yana albarkar waɗanda suke amfani da ’yancinsu don su ɗaukaka bauta ta gaskiya da kuma waɗanda suke iya ƙoƙarinsu don su tsarkake sunansa kuma su yi nufinsa. Jehobah ba ya so mu yi masa biyayya don muna gudun horo ko don ana matsa mana. Maimakon haka, Jehobah yana son mutum ya bauta masa don ƙauna da kuma godiya.
Alal misali, sa’ad da Isra’ilawa suke jejin Sinai, Jehobah ya umurce su su gina wurin bauta. Ya ce: “Ku ɗauki hadaya daga wurinku ku kai wa Ubangiji: dukan wanda ya yi niyya, bari shi kawo, hadayar Ubangiji ke nan.” (Fit. 35:5) Kowane Ba’isar’ila yana iya ba da abin da zai iya bayarwa da yardar rai, ko da mene ne ko da nawa ne ake bukata don a yi nufin Allah. Shin mene ne suka yi?
‘Dukan wanda zuciyarsa ta sa shi, da dukan wanda ruhunsa’ ya motsa shi ya ba da hadaya daga ‘zuciyarsa.’ Maza da mata da yardar rai sun kawo wani abu don aikin Jehobah kamar su liwalai da ’yan kunne da zobe da zinariya da azurfa da janganci da shuɗi da shunaiya da mulufi da lilin mai taushi da gashin akuya da fatun raguna jajaye da fatun seal da itacen maje da duwatsun ado da balsam da kuma mai. Saboda haka, “kayan da ke wurinsu ya isa da za a yi dukan aiki, har ya yi yawa.”—Fit. 35:21-24, 27-29; 36:7.
Jehobah ya yi farin ciki da gudummawan mutanen amma yadda suka yi hakan da son rai don su tallafa wa bauta ta gaskiya ne ya fi faranta masa rai. Ƙari ga haka, sun ba da lokacinsu da kuzarinsu don aikin. Labarin ya ce: “Dukan mata kuma masu-hikima ga zuciya suka yi kaɗi da hannuwansu.” Hakika, “dukan mata kuma waɗanda zuciyarsu ta zuga su cikin hikima suka yi kaɗin gashin akuya.” Ƙari ga haka, Jehobah ya ba wa Bezalel ‘hikima da fahimi da ilimi da kowace irin sana’ar’ da ake bukata don yin aikin. Hakika, Allah ya ba wa Bezalel da Oholiab basira don su yi aikin da aka ce a yi.—Fit. 35:25, 26, 30-35.
Sa’ad da Jehobah ya ce wa Isra’ilawa su ba da gudummawa, ya tabbata cewa “dukan wanda ya yi niyya” zai tallafa wa bauta ta gaskiya. A sakamakon haka, Jehobah ya albarkace su da ja-gora mai kyau da farin ciki don wannan halin da suka nuna. Ta hakan, Jehobah ya nuna cewa sa’ad da ya albarkaci bayinsa da suke bayarwa da son rai, zai tanadar da masu aiki da kuma dukan abubuwan da ake bukata don a cim ma nufinsa. (Zab. 34:9) Ka tabbata cewa Jehobah zai albarkace ka don yadda kake bayarwa don a cim ma nufinsa.