Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w09 11/15 pp. 18-19
  • Bayarwa da Daɗin Rai da Dukan Zuciyarmu

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Bayarwa da Daɗin Rai da Dukan Zuciyarmu
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Makamantan Littattafai
  • Bauta wa Allah da ‘Zuciya da Rai Ɗaya’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Kana Farin Ciki da Gatar Yin “Alheri”?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • ‘Bari Mu Kawo Baiko ga Jehobah’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Yalwarsu ta Biya Bukatar Wasu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
w09 11/15 pp. 18-19

Bayarwa da Daɗin Rai da Dukan Zuciyarmu

A BATUN bayarwa, manzo Bulus ya rubuta: “Kowane mutum ya aika bisa yadda ya annita a zuciyarsa,” sai ya daɗa: “Ba da cicijewa ba, ba kuwa kamar ta dole ba: gama Allah yana son mai-bayarwa da daɗin rai.” (2 Kor. 9:7) Jehobah ba ya tilasta wa kowa ya tallafa wa bauta ta gaskiya. Yana ƙyale bayinsa su nuna ibadarsu ta wajen bayarwa da son rai da kuma daɗin rai. A cikin tarihi, mutanensa sun aikata da ƙwazo. Ga misalai uku.

Bayan Jehobah ya ja-goranci Isra’ilawa su fita daga ƙasar Masar, ya gaya musu su gina mazauni. Suna bukatar kayan aiki, sai aka gaya wa Isra’ilawa su ba da gudummawa. Sai “dukan wanda zuciyarsa ta zuga shi,” ya kawo zinariya da azurfa, lu’ulu’u, da wasu kayayyaki. Mutanen sun ba da abubuwa sosai da har aka yi sanarwa cewa su daina bayarwa.—Fit. 35:5, 21; 36:6, 7.

Bayan ƙarnuka da yawa, sa’ad da ake son a gina haikalin, mutanen Allah suna da zarafin su nuna suna tallafa wa bauta mai tsarki. Sarki Dauda da kansa ya ba da gudummawa sosai game da aikin kuma ya gaya wa wasu su ba da gudummawa. Sun yi hakan da daɗin rai. Hakika, zinariya da azurfa da suka ba da kawai sun fi dalla biliyan ɗari a kuɗi na yanzu! Mutanen sun yi farin ciki don sun ba da gudummawa da son rai ga Jehobah.—1 Laba. 29:3-9; 2 Laba. 5:1.

Mabiyan Yesu Kristi na farko su ma sun nuna halin bayarwa da daɗin rai. A ranar Fentakos na shekara ta 33 A.Z., an yi wa mutane wajen dubu uku baftisma, da yawa cikinsu ba sa zama a Urushalima. Don a taimaka wa talakawa su kasance a birnin su ƙara koya game da sabon imaninsu, an ɗan karɓi gudummawar kuɗi. ’Yan’uwan sun sayar da dukiyoyinsu kuma suka kai wa manzannin kuɗin don a taimaka wa mabukata. Babu shakka, Jehobah ya yi farin ciki da ya lura da irin wannan nuni na bangaskiya da ƙauna!—A. M. 2:41-47.

A yau Kiristoci sun ci gaba da tallafa wa bauta ta gaskiya ta wajen ba da lokacinsu, ƙarfinsu, da kuɗinsu da daɗin rai. Akwati na gaba ya nuna wasu hanyoyi da za ka yi hakan.

[Akwati da ke shafi na 18]

Hanyoyin Da Wasu Suka Zaɓi Su Ba da

GUDUMMAWA GA AIKIN WA’AZI NA DUKAN DUNIYA

Yawanci suna keɓe kuɗin da za su riƙa sakawa a cikin akwatunan da aka rubuta “Worldwide Work.”

A kowane wata, ikilisiyoyi suna aika waɗannan kuɗaɗen zuwa ofishin reshe na Shaidun Jehobah da ke kula da ƙasar da suke. Kuna iya aika gudummawa kai tsaye zuwa ofishin reshe da ke kula da ƙasarku. Idan kuna son ku aika mana cek, ku rubuta “Watch Tower” a kai don mu sami kuɗin. Kuna iya ba da gudummawar ’yan kunne da sarƙa masu tsada ko dukiyoyi. Ku rubuta ’yar gajerar wasiƙar da za ta nuna cewa waɗannan abubuwan gudummawa ne.

HANYOYIN BA DA GUDUMMAWA

Ƙari ga ba da kyautar kuɗi, akwai wasu hanyoyin ba da kyauta da za su amfane hidimar Mulki a dukan duniya. Su ne:

Inshora: Kuna iya rubuta sunan Watch Tower a matsayin wanda zai karɓi inshorar rai ko na murabus ko fansho.

Ajiyar Banki: Kuna iya ba da kuɗin da kuke da shi a banki, ko wanda kuka ajiye na ƙayyadadden lokaci (fixed deposit), ko kuma kuɗin da aka ba ku bayan kun yi murabus da kuka ajiye a banki ga Watch Tower don su yi amfani da shi, ko kuma ku ce a ba su kuɗin bayan mutuwa, bisa ga bukatun bankin.

Hannayen Jari: Ana iya ba da gudummawar hannayen jari ga Watch Tower a matsayin kyauta.

Fegi da Gida: Kuna iya yi wa Watch Tower kyautar fegin da za a iya sayarwa, idan kuma gida ne da mutum yake ciki, mutumin yana iya ci gaba da zama a ciki yayin da yake da rai. Ku gaya wa ofishin reshen da ke ƙasarku kafin ku yi kyauta da gidan ko fegin.

Wasiyya da Ajiya: Ana iya ba Watch Tower dukiya ko kuɗi a matsayin gado bayan mutuwa ta hanyar takardar da aka saka hannu a ƙarƙashin doka, ko kuma a rubuta Watch Tower a matsayin wanda zai ci amfanin ajiyar da aka yi.

Irin waɗannan hanyoyin ba da gudummawa da muka ambata suna bukatar mai yin su ya yi shiri sosai.

Don ƙarin bayani, kuna iya rubuta wasiƙa ko ku kira Ofishin Reshe na Shaidun Jehobah a adireshin da ke ƙasa ko kuwa ku tuntuɓi ofishin reshe da ke kula da ƙasarku.

Jehovah’s Witnesses

P.M.B 1090,

Benin City 300001,

Edo State, Nigeria.

Tarho: 07080662020

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba