Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w17 Nuwamba pp. 18-19
  • “Mai-Alheri Za Ya Sami Albarka”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • “Mai-Alheri Za Ya Sami Albarka”
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2017
  • Makamantan Littattafai
  • ‘Aikin Kuwa da Girma’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2016
  • Ka Rika Godiya ga Jehobah, Allah Mai Karimci
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
  • Yalwarsu ta Biya Bukatar Wasu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Jehobah Yana Albarkar Masu Son Bayarwa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2017
w17 Nuwamba pp. 18-19
Hannatu ta kawo Sama’ila mazauni

“Mai-Alheri Za Ya Sami Albarka”

BAYIN ALLAH a dā sun ba da hadaya kuma yin haka yana da muhimmanci sosai. Isra’ilawa sun ba da hadayar dabbobi, kuma an san Kiristoci da ba da “hadaya ta yabo.” Amma akwai wasu hadayu ma da ke faranta wa Allah rai. (Ibran. 13:​15, 16) Waɗannan hadayun suna sa mutane farin ciki kuma suna sa su samu albarka sosai, kamar yadda misalan da za mu gani suka nuna.

Wata baiwar Allah mai suna Hannatu tana so ta haihu, amma ba ta iya yin hakan ba. Sai ta yi wa Jehobah addu’a kuma ta yi alkawari cewa idan ta haifi ɗa, za ta “ba da shi ga Ubangiji muddar ransa.” (1 Sam. 1:​10, 11) Da shigewar lokaci, Hannatu ta yi juna biyu kuma ta haifi ɗa, ta sa masa suna Sama’ila. Bayan da Hannatu ta yaye Sama’ila, sai ta kai shi mazauni don ta cika alkawarin da ta yi. Jehobah ya albarkaci Hannatu don abin da ta yi. Kuma ta ƙara haifan yara biyar, ban da haka ma, Sama’ila ya zama annabi da kuma marubucin wasu littattafai a Littafi Mai Tsarki.​—1 Sam. 2:21.

Kamar abin da Hannatu da Sama’ila suka yi, Kiristoci a yau suna da damar yin amfani da rayuwarsu don su yi wa Mahaliccinsu hidima. Ban da haka ma, Yesu ya yi alkawarin cewa za mu sami albarka sosai a duk wata sadaukarwa da muka yi a bautarmu ga Jehobah.​—Mar. 10:​28-30.

A ƙarni na farko, akwai wata mata mai suna Dokas da mutane suka san ta da “ayyukan nagarta da bayebayen” da take yi don ta taimaka ma wasu. Amma abin tausayi shi ne, “ta yi ciwo, ta mutu” kuma hakan ya sa ikilisiyar da take baƙin ciki sosai. Da ’yan’uwan suka ji cewa Bitrus yana yankinsu, sai suka kirawo shi. Babu shakka, sun yi farin ciki sosai da Bitrus ya zo ya ta da Dokas, kuma shi ne manzo na farko da ya ta da wani daga mutuwa. (A. M. 9:​36-41) Hakika, Allah bai manta da ayyukan da Dokas ta yi ba. (Ibran. 6:10) Kuma an rubuta labarin alherin da ta yi a Littafi Mai Tsarki don bayin Allah su yi koyi da halinta mai kyau.

Manzo Bulus ma ya kafa misali mai kyau na ba da lokacinsa da kuma taimaka wa mutane. Sa’ad da yake rubuta wa ’yan’uwan da ke Korinti wasiƙa ya ce: “Ni ma da farin ciki sarai na yarda in batar har kuwa a batar da ni sabili da rayukanku.” (2 Kor. 12:15) Bulus ya fahimci cewa yin sadaukarwa don wasu yana sa mutum farin ciki kuma yana sa Jehobah ya yi mana albarka. Ƙari ga haka, zai amince da shi.​—A. M. 20:​24, 35.

Babu shakka, idan muna amfani da lokacinmu don mu tallafa wa ƙungiyar Jehobah ko kuma taimaka wa ’yan’uwanmu, hakan yana faranta wa Jehobah rai. Ƙari ga abin da aka ambata, akwai wasu hanyoyin da za mu tallafa ma wa’azin da ake yi game da Mulkin Allah? E! Ban da ayyukan da muke yi, za mu iya nuna godiya ta wajen ba da gudummawa. Ana amfani da gudummawar ne don a tallafa wa ’yan’uwan da ke wa’azi a wata ƙasa da kuma wasu da ke hidima ta cikakken lokaci na musamman. Ban da haka ma, ana amfani da gudummawar don fassara littattafai da bidiyoyi da taimaka wa ’yan’uwa da bala’i ya auko musu. Ƙari ga haka, ana yin amfani da shi don a gina Majami’un Mulki da kuma kula da su. Muna bukatar mu kasance da tabbacin cewa “mai-alheri za ya sami albarka.” Ƙari ga haka, ba da gudummawa yana nuna cewa muna daraja Jehobah sosai.​—Mis. 3:9; 22:9.

Hanyoyin Da Wasu Suke Ba Da Gudummawa Don Wa’azi

Kamar yadda yake a zamanin manzo Bulus, mutane da yawa suna “ajiye” kuɗi da za su riƙa sakawa a cikin akwatunan gudummawa da ke cikin ikilisiya da aka rubuta “Aiki na Dukan Duniya.” (1 Kor. 16:2) A kowane wata, ikilisiyoyi suna tura waɗannan gudummawan zuwa ofishin Shaidun Jehobah da ke ƙasarsu. Kana iya aika gudummawarka kai tsaye zuwa ofishin Shaidun Jehobah da ke ƙasarku. Idan kana son ka san sunan da Shaidun Jehobah suke amfani da shi a ƙasarku, ka tuntuɓi ofishinsu da ke ƙasarku. Kana iya samun adireshin ofishin Shaidun Jehobah a dandalin www.pr418.com/ha. Bisa ga bukatun ƙasarku, ga irin gudummawar da za ka iya aikawa kai tsaye:

KYAUTA

  • Gudummawa ta hanyar tura kuɗi ta banki ko kuma wajen amfani da katin ATM. A wasu ofisoshin Shaidun Jehobah, ana iya yin hakan ta jw.org ko kuma wani dandalin da aka ce a yi amfani da shi.

  • Kuɗi ko kayan ado kamar gwalagwalai ko kuma wasu kaya masu daraja. Ka haɗa da wasiƙar da ke nuna cewa kuɗin ko kuma kayayyakin ka ba da su kyauta ne.

RANCE

  • Za a iya ba da rancen kuɗi kuma ana iya mayar wa mai shi a duk lokacin da yake bukata.

  • A haɗa da wasiƙar da ke nuna cewa kuɗin rance ne.

WASU HANYOYIN BA DA GUDUMMAWA

Ƙari ga ba da kyautar kuɗi da kaya masu amfani, akwai wasu hanyoyin ba da kyauta don a tallafa ma wa’azin bishara ta Mulki a dukan duniya. Kafin ka zaɓa wata hanyar ba da gudummawa, ka fara tuntuɓar ofishin Shaidun Jehobah da ke ƙasarku don neman bayani game da tsarin da ya dace a ƙasarku. Tun da yake dokokin sun dangana ga ƙasarku, yana da muhimmanci ka fara tuntuɓar lauya kafin ka tsai da shawara a kan yadda za ka ba da gudummawa. An jera waɗannan hanyoyin a ƙasa.

Inshora da Fensho: Kana iya rubuta cewa wani rukunin da Shaidun Jehobah suke amfani da shi da hukuma ta yi wa rajista ne zai karɓi inshorar rai ko kuma fensho.

Ajiyar Banki: Kana iya ce a ba wani rukunin da Shaidun Jehobah suke amfani da shi da hukuma ta yi wa rajista ajiyarka a banki bayan ka rasu, bisa ga dokokin bankin.

Hannayen Jari: Ana iya ba ma wani rukunin da Shaidun Jehobah suke amfani da shi da hukuma ta yi wa rajista kyautar hannayen jari ko kuma a yi yarjejeniya cewa za a ba su bayan mai shi ya rasu.

Fegi da Gida Kana iya ba ma wani rukunin da Shaidun Jehobah suke amfani da shi da hukuma ta yi wa rajista kyautar fegin da za a iya sayarwa, idan kuma gida ne da mutum yake ciki, yana iya ci gaba da zama a ciki yayin da yake da rai.

Wasiyya da Ajiya Ana iya ba ma wani rukunin da Shaidun Jehobah suke amfani da shi da hukuma ta yi wa rajista dukiya ko kuɗi ta hanyar rubuta takardar da aka saka hannu bisa doka, ko kuma a nuna cewa ƙungiyar ce za ta gāji ajiyar. Wataƙila hakan zai taimaka a rage kuɗin haraji da ake biya.

Zai dace a yi shiri da kyau don ba da irin waɗannan gudummawa da aka ambata. Don a taimaka ma waɗanda suke so su ba da gudummawa don aikin da Shaidun Jehobah suke yi a faɗin duniya, an wallafa wata ƙasida mai jigo Charitable Planning to Benefit Kingdom Service Worldwide a Turanci da Sfanisanci. An wallafa wannan ƙasidar don a ba da ƙarin bayani a kan hanyoyi dabam-dabam da mutum zai iya ba da gudummawa yanzu ko kuma a nan gaba, kamar ta hanya gādo bayan rasuwa. Wataƙila bayanin da ke cikin wannan ƙasidar bai shafi yankin da kake ba domin dokokin haraji ko kuma wasu dokoki da ake bi a ƙasar. Ta wurin yin amfani da waɗannan hanyoyin ba da gudummawa, mutane da yawa sun taimaka wa ƙungiyarmu ko kuma ayyukanmu na ba da agaji a dukan duniya. Ƙari ga haka, wannan ya taimaka a rage kuɗin harajin da gwamnati ta ce su biya. Idan kuna da wannan ƙasidar a ƙasarku, za ka iya samu guda ɗaya daga wurin sakataren ikilisiyarku.

Don ƙarin bayani, ka danna “Ka Ba da Gudummawa don Aikinmu a Dukan Duniya” a ƙarƙashin kowane shafi a dandalin jw.org/ha ko kuma ka tuntuɓi ofishin Shaidun Jehobah da ke ƙasarku.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba