Abin da Za a Ce Game da Mujallun
Janairu-Maris
“Aure zai iya zama ƙalubale, amma yana daɗa tsanani sa’ad da ɗaya daga cikin ma’auratan yana da ciwo mai tsanani. Kana tsammani cewa zai iya yiwu a jimre wa irin wannan yanayin kuwa? [Ka bari ya ba da amsa.] Ka lura da Nassin da irin waɗannan ma’auratan za su iya yin tunani akai. [Karanta Farawa 2:24.] Wannan talifin da ya soma daga shafi na 16 ya tattauna abin da zai iya taimaki waɗannan ma’auratan su jimre wa yanayin.”
Janairu
Karanta Ayyukan Manzanni 17:31a. Sai ka ce: “Ga mutane da yawa, zancen Ranar Shari’a yana tsorata su. Yaya kake ji? [Ka bari ya ba da amsa.] Littafi Mai Tsarki ya koyar cewa Ranar Shari’a za ta kawo albarka da yawa zuwa duniya. Wannan mujallar ta ba da bayani.” Ka gabatar da talifin da ya soma daga shafi na 10.
Janairu-Maris
“Kana tsammani cewa wata rana Allah zai kawar da dukan wahala a duniya kuwa? [Ka bari ya ba da amsa.] Ka lura da wannan alkawari na Littafi Mai Tsarki wanda ya ba mu bege. [Karanta nassi ɗaya da ke cikin akwatin da ke shafi na 7.] Wannan mujallar ta nuna abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da lokaci da kuma yadda Allah zai kawar da dukan wahala.”
Fabrairu
“Kashe aure gama gari ne a yau. Kana tsammani cewa yawancin ma’aurata suna yin tunani sosai kafin su kashe aurensu kuwa? [Ka bari ya ba da amsa. Sai ka karanta Misalai 14:15.] Wannan mujallar ta bayyana abubuwa huɗu da ya kamata ma’aurata su yi la’akari da shi sa’ad da suke yanka shawarar kashe aurensu.”