Abin da Za a Ce Game da Mujallun
Janairu-Maris
“Wataƙila ka san wani da salon rayuwarsa bai jitu da mizanan Littafi Mai Tsarki ba. Mene ne kake gani zai iya taimaka masa ya yi canje-canje? [Ka bari ya ba da amsa.] Ka lura da abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa a waɗannan ayoyin. [Karanta Kolosiyawa 3: 9, 10.] Wannan talifin da ya soma a shafi na 18 ya tattauna yadda Littafi Mai Tsarki ya canja rayuwar wasu mutane.”
Janairu
“Wasu sun gaskata cewa imani na addini ya dangana ga yadda mutum yake ji fiye da yin tunanin kirki. Mene ne ra’ayinka? [Ka bari ya ba da amsa.] Littafi Mai Tsarki ya ce bai kamata a riƙa bin imani na addini haka kawai ba. [Karanta 1 Yohanna 4:1.] Talifin da ya soma a shafi na 28 ya bayyana yadda za mu tabbata cewa imaninmu yana bisa tunanin kirki.”
Janairu-Maris
“Kana tunanin cewa mala’iku suna son su san abubuwan da muke yi ne? [Ka bari ya ba da amsa.] Littafi Mai Tsarki ya yi wannan kalami mai kyau. [Karanta Luka 15:10.] Wannan talifin ya tattauna abin da Yesu ya faɗa game da yadda halittu na ruhu suke shafanmu.” Ka gabatar da talifin da ya soma a shafi na 24.
Fabrairu
“Kamar dai mutane da yawa suna ƙara son sani game da mayu, da kuma bokaye. Kana ganin cewa sa hannu cikin sihiri ba shi da lahani ne? [Ka bari ya ba da amsa.] Ka ga wannan kashedin da Allah ya ba Isra’ila ta dā. [Karanta Kubawar Shari’a 18:10-12.] Wannan mujallar ta nuna abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa game da sihiri.”