DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | ZABURA 38-44
Jehobah Yana Taimaka wa Marasa Lafiya
Amintattu suna da tabbaci cewa Jehobah zai taimake su sa’ad da suke cikin matsala
41:1-4
Dauda ya yi ciwo mai tsanani
Dauda ya taimaki matalauta
Dauda bai sa rai cewa za a warkar da shi ta hanyar mu’ujiza ba, amma ya dogara ga Jehobah don ya ƙarfafa shi, ya ba shi hikima kuma ya taimaka masa
Jehobah ya ɗauki Dauda a matsayin mutumi mai aminci