DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
Yadda Dokar Musa Ta Nuna Cewa Jehobah Ya Damu da Talakawa
Isra’ilawa sun taimaka wa talakawa da waɗanda ba su da gādo (M.Sh 14:28, 29; it-2-E 1110 sakin layi na 3)
A ƙarshen kowace shekara ta bakwai, Isra’ilawa suna “yafe” bashin da suke bin wani (M.Sh 15:1-3; it-2-E 833)
Idan Ba’isra’ile ya sayar da kansa zuwa bauta, a shekara ta bakwai, maigidansa zai ’yantar da shi kuma ya yi masa kyauta (M.Sh 15:12-14; it-2-E 978, sakin layi na 6)
KA TAMBAYI KANKA, ‘A waɗanne hanyoyi ne zan nuna cewa na damu da Kiristocin da ke bukatar taimako?’