DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
Ku Nemi Mafaka a Wurin Jehobah, Allah Madawwami
Jehobah yana so mu kasance da dabi’a mai kyau (M.Sh 33:26; it-2-E 51)
Jehobah yana amfani da ikonsa don ya taimaka mana (M.Sh 33:27; w11 10/15 26 sakin layi na 18)
Kamar Musa, ya kamata mu kasance da tabbaci cewa Jehobah zai cece mu (M.Sh 33:29; w11 9/15 19 sakin layi na 16)
Jehobah zai taimaka mana sa’ad da muke fuskantar matsaloli. Hakan ya haɗa da lokacin da muke rashin lafiya, ko baƙin ciki, ko idan mutum ya yi zunubi amma ya tuba.