DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
Ka Kāre Gadonka
Kaleb ya kāre gadonsa ta wurin korin maƙiyansa (Yos 15:14; w04 6/1 7 sakin layi na 8)
Ba dukan Isra’ilawa ba ne suka kāre gadonsu daga wurin mutane da ba sa bauta wa Jehobah (Yos 16:10; it-1-E 848)
Jehobah ya taimaka wa mutane da suke so su kāre gadonsu (M.Sh 20:1-4; Yos 17:17, 18; it-1-E 402 sakin layi na 3)
Jehobah ya ba dukan Kiristoci gadon rai na har abada. Don mu kāre gadonmu, wajibi ne mu guji faɗa cikin jaraba ta wajen nazarin Littafi Mai Tsarki da halartan taro da yin wa’azi da kuma addu’a.
KA TAMBAYI KANKA, ‘Ina kāre gadona kuwa?’