Yakubu yana yi wa yaransa annabci
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
Jehobah Ya Raba Ƙasar Yadda Ya Dace
Jehobah ya ba da umurni a jefa ƙuri’a, wataƙila domin kowace zuriya ta sami nata rabon gadon (Yos 18:10; it-1-E 359 sakin layi na 1)
Jehobah ya tabbata cewa annabcin da Yakubu ya yi sa’ad da ya kusan mutuwa ya cika (Yos 19:1; it-1-E 1200 sakin layi na 1)
Jehobah ya bar mutanen su zaɓi yadda girma gadon kowace ƙabila za ta kasance (Yos 19:9; it-1-E 359 sakin layi na 2)
An raba ƙasar yadda ƙabilun ba za su yi kishin juna ko kuma su yi fada ba. Ta yaya hakan ya ba mu tabbaci cewa Jehobah zai tsara abubuwa yadda ya dace a sabuwar duniya?