Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • mwb21 Nuwamba p. 15
  • Ka Koya wa Dalibanka Yadda Za Su Rika Nazari da Kansu

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Koya wa Dalibanka Yadda Za Su Rika Nazari da Kansu
  • Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2021
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Taimaka wa Dalibanka Su Zama Aminan Jehobah
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2022
  • Ka Taimaka wa Dalibanka Su Daina Halayen da Jehobah Ba Ya So
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2022
  • Yin Tambayoyi
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2021
  • Ka Ratsa Zukatan Mutane
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2021
Dubi Ƙari
Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2021
mwb21 Nuwamba p. 15

KA YI WA’AZI DA KWAZO | YADDA ZA KA DAƊA JIN DAƊIN WA’AZI

Ka Koya Wa Ɗalibanka Yadda Za Su Riƙa Nazari da Kansu

Don ka taimaka wa ɗalibanka su san Jehobah kuma su manyanta, wajibi ne su ƙara koyan wasu abubuwa. (Mt 5:3; Ibr 5:12–6:2) Wajibi ne su koyi yadda za su riƙa nazari da kansu.

Tun da farko ka nuna wa ɗalibanka yadda za su riƙa shiri kafin ku yi nazari, kuma ka ƙarfafa su su yi hakan. (mwb18.03 6) Ka ƙarfafa su su yi addu’a kafin su soma nazari da kansu. Ka taimaka musu su san yadda ake amfani da waya a nazari. Ka bayyana musu yadda za su ga sabbin abubuwa a dandalin jw.org da kuma shirye-shiryen JW. Ka ci gaba da koya musu yadda za su riƙa karanta Littafi Mai Tsarki kullum, da yin shiri don taro da kuma yin bincike don su sami amsoshin tambayoyinsu. Ka taimaka musu su riƙa yin tunani a kan abin da suke koya.

KU KALLI BIDIYON NAN KU TAIMAKA WA ƊALIBANKU SU RIƘA NAZARI DA KANSU, SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:

  • Hoto daga bidiyon “Ku Taimaka Wa Dalibanku Su Rika Nazari da Kansu.” Rose ta ce ta tuna abubuwan da suka ratsa zuciyarta.

    Ta yaya Anita ta taimaka wa Rose ta san cewa yin nazari ba kawai sanin amsar tambayoyi ba ne?

  • Hoto daga bidiyon “Ku Taimaka Wa Dalibanku Su Rika Nazari da Kansu.” Anita ta taimaka wa Rose ta sami amsa a cikin wani nassi.

    Mene ne ya taimaka wa Rose ta amince cewa ya dace da Jehobah ya hana yin lalata?

  • Hoto daga bidiyon “Ku Taimaka Wa Dalibanku Su Rika Nazari da Kansu.” Rose tana bimbini a kan wani nassi yayin da ta zauna kusa da saurayinta.

    Ka koya wa ɗalibanka yadda za su riƙa nazari da kansu don abin da suke koya ya ratsa zuciyarsu

    Mene ne Rose ta fahimta game da muhimmancin yin tunani a kan abin da take nazarinsa?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba