DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
“Ki Ɗauko Ɗanki”
Wata mata daga Shunem ta kula da Elisha sosai (2Sar 4:8-10)
Jehobah ya albarkace ta kuma ta haifi ɗa (2Sar 4:16, 17; w17.12 4 sakin layi na 7)
Jehobah ya sa Elisha ya ta da ɗanta da ya mutu (2Sar 4:32-37; w17.12 4 sakin layi na 8)
Kana fama da baƙin ciki don ’yarka ko ɗanka ya rasu? Jehobah ya san yadda da kake ji. Nan ba da daɗewa ba, zai ta da wani naka da ya rasu. (Ayu 14:14, 15) Babu shakka ranar za ta zama rana ta musamman!