WAƘA TA 5
Ayyukan Allah Suna da Ban Al’ajabi
Hoto
(Zabura 139)
1. Jehobah Allahnmu mai iko,
Kana sane da duk ayyukana.
Kana ganin kome a zuciyata,
Furucina, halayena,
duk ka san su.
Ka ga sa’ad da nake ciki,
Kafin ma a san za a haife ni.
Fasalina duk a gabanka suke.
Ina yabo da kuma son
ayyukanka.
Hikimarka tana da ban mamaki,
Ina farin cikin sanin hakan.
Idan na ɓoye a inda ba haske,
Duk da haka Jehobah zai gan ni.
Jehobah a ina zan ɓoye
da ba za ka iya gani na ba?
Ko na shiga Kabari ko a sama,
ko cikin duhu ko teku,
za ka gan ni.
(Ka kuma duba Zab. 66:3; 94:19; Irm. 17:10.)