Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w13 9/1 pp. 10-13
  • Littafi Mai Tsarki Yana Gyara Rayuwar Mutane

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Littafi Mai Tsarki Yana Gyara Rayuwar Mutane
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Makamantan Littattafai
  • Wadanda Ba Sa Cin Nama​—Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce?
    Karin Batutuwa
  • Littafi Mai Tsarki Yana Gyara Rayuwar Mutane
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Littafi Mai Tsarki Yana Gyara Rayuwar Mutane
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Littafi Mai Tsarki Yana Canja Rayuka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
w13 9/1 pp. 10-13

LITTAFI MAI TSARKI YANA GYARA RAYUWAR MUTANE

“Na Daina Ɗauka Cewa Zan Iya Gyara Yanayin Duniya”

Jukka Sylgren ne ya ba da labarin

  • SHEKARAR HAIHUWA: 1966

  • ƘASAR HAIHUWA: FINLAND

  • TARIHI: MAI NEMAN SAUYI

RAYUWATA A DĀ:

Na soma ƙaunar halittun Allah tun ina yaro. Sau da yawa, iyalinmu sukan fita shan iska a inda akwai itatuwa masu kyan gani da kuma tafkuna da ke kewaye da garinmu, wato, Jyväskylä, a Central Finland. Da yake ni mai son dabbobi ne, sa’ad da nake yaro na so in riƙa wasa da duk wani kule ko kare da na gani! Sa’ad da nake girma, na lura da yadda mutane suke wulaƙanta dabbobi kuma hakan ya ɓata min rai sosai. Da shigewar lokaci na shiga wata ƙungiyar kāre hakkin dabbobi, kuma a nan ne na haɗu da mutane masu ra’ayi ɗaya da ni.

Mun yi zanga-zanga don kāre hakkin dabbobi, kuma mun yi adawa da shaguna da ake sayar da fātun dabbobi da kuma ɗakunan bincike da ke amfani da dabbobi wajen gwaje-gwaje, kuma mun yaɗa bayanai ga mutane. Har ma muka kafa wata sabuwar ƙungiya don kāre hakkin dabbobi. Da yake mukan ɗauki matakai masu tsanani don mu cim ma burinmu, mun riƙa samun matsala da hukuma. Sau da yawa ’yan sanda sun kama ni kuma sun kai ni kotu.

Ƙari ga yadda nake damuwa da dabbobi, wasu matsaloli da ke faruwa a duniya ma sun dame ni sosai. Saboda haka, da sannu-sannu, na shiga ƙungiyoyin kāre hakki da yawa, kamar su Amnesty International da kuma Greenpeace. Na yi hidima kuma na ba da kaina gaba ɗaya ga ƙungiyoyin nan. Na yi yaƙin neman hakkin matalauta da waɗanda suke ƙarancin abinci da kuma waɗanda ake takura musu.

Amma, a hankali na gano cewa ba zan iya canja duniya ba. Ko da yake waɗannan ƙungiyoyin sun ɗan yi gyare-gyare a wasu fannoni, amma sun kasa magance manyan matsalolin da ke addabar mutane. Kamar dai mugunta ta mamaye duniya gaba ɗaya kuma babu wanda ya damu da ɗaukan mataki a kai. A lokacin ne na gano cewa tusa ba ta hura wuta.

YADDA LITTAFI MAI TSARKI YA CANJA RAYUWATA:

Irin baƙin ciki da na ji domin kasawata ya sa na soma tunani sosai game da Allah da kuma Littafi Mai Tsarki. Kafin wannan lokacin, Shaidun Jehobah sun taɓa yin nazarin Littafi Mai Tsarki da ni. Ko da yake na so yadda Shaidun suka kula da ni kuma suka yi mini alheri, ban shirya gyara halayena ba. Amma, yanzu kiɗar ganga ta canja.

Na soma karanta Littafi Mai Tsarki da nake da shi kuma hakan ya sa na sami kwanciyar hankali sosai. Na lura da ayoyi da yawa a cikin Littafi Mai Tsarki da suke koya mana yadda za mu kula da dabbobi. Alal misali, littafin Misalai 12:10 ya ce: “Mutumin kirki yakan lura da dabbobinsa.” (Littafi Mai Tsarki) Na kuma fahimci cewa ba Allah ne yake haddasa matsalolin da muke fama da su a duniya ba. Amma matsalolinmu suna daɗa muni ne domin yawancin mutane sun ƙi bin ja-gorarsa. Sanin cewa Jehobah yana da ƙauna da tsawon jimrewa ya burge ni sosai.—Zabura 103:8-14.

A wannan lokacin, na sami wata mujalla da ɗayan shafin na ɗauke da bayani a kan yadda zan iya samun littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?, kuma na aika takardar zuwa ofishin reshe na Shaidun Jehobah. Ba da daɗewa ba, wasu ma’aurata Shaidun Jehobah suka zo gidana kuma suka gaya min cewa za su iya yin nazarin Littafi Mai Tsarki da ni. Na yi na’am da hakan kuma na soma halartan taro a Majami’ar Mulki. Hakan ya sa na soma jin daɗin abin da nake koya daga Littafi Mai Tsarki.

Littafi Mai Tsarki ya taimaka mini in yi canji sosai. Na daina maye da kuma shan taba. Na daina baƙar magana kuma na soma ado mai kyau. Na daidaita ra’ayina game da hukuma. (Romawa 13:1) Ko da yake a dā ina yin lalata kamar yadda mutum yake shan ruwa, amma yanzu na daina.

Gyara mafi wuya da na yi ita ce kasancewa da ra’ayi da ya dace game da ƙungiyoyi masu kāre hakki. Hakan bai kasance mini da sauƙi ba. Da farko, na ɗauka cewa yin murabus yana nufin cewa na ci amanar waɗannan ƙungiyoyin ne. Amma daga baya, na fahimci cewa Mulkin Allah ne kawai zai iya magance matsalolin duniya. Hakan ya sa na yi iyakacin ƙoƙarina wajen yin wa’azi da kuma koya wa mutane game da Mulkin Allah.—Matta 6:33.

YADDA NA AMFANA:

A matsayin mai kāre hakkin ’yan Adam da dabbobi nakan raba mutane zuwa kashi biyu, wato, masu kirki da marasa kirki, kuma ina shirye in yaƙi waɗanda nake ganin ba su da kirki. Amma yanzu, Littafi Mai Tsarki ya taimaka mini in daina ƙiyayya. A maimakon haka, ina ƙoƙari in yi ƙaunar dukan mutane kamar yadda ya kamata Kiristoci su yi. (Matta 5:44) Ƙari ga wasu abubuwa da nake yi, ina ƙoƙarin nuna wannan ƙaunar ta wajen yin bisharar Mulkin Allah. Ina farin cikin ganin yadda wannan aikin alheri yana taimaka wa mutane su kasance da zaman lafiya da juna da bege da kuma farin ciki.

Yanzu na bar kome a hannun Jehobah kuma hakan ya sa na sami kwanciyar hankali. Na tabbata cewa Mahaliccinmu ba zai bari a wulaƙanta ’yan Adam da dabbobi har abada ba, kuma ba zai bari a halaka wannan duniya ba. Akasin haka, zai yi amfani da Mulkinsa don ya gyara dukan abubuwan da ’yan Adam suka lalata a duniya. (Ishaya 11:1-9) Sanin wannan gaskiyar da kuma taimaka wa mutane su amince da ita yana sa ni farin ciki sosai. Yanzu na daina ɗauka cewa zan iya gyara yanayin duniya.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba