Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w01 11/1 pp. 20-25
  • Jehovah Allah Ne Mai Tsawon Jimrewa

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Jehovah Allah Ne Mai Tsawon Jimrewa
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Daidai Yake da Muhimmin Hali na Allah
  • Tsawon Jimrewa na Jehovah Kafin Rigyawa
  • Tsawon Jimrewa Mai Kyau ga Isra’ila
  • Tsawon Jimrewa na Jehovah Bai Ƙare Ba
  • Tsawon Jimrewa Domin Sunansa
  • Tsawon Jimrewa na Jehovah Yana Kawo Ceto
  • ‘Ku Yafa Wa Kanku Tsawon Jimrewa’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Abin da Muka Koya Daga Ƙyale Mugunta da Allah Ya Yi
    Ka Bauta wa Allah Maƙadaici na Gaskiya
  • Za Ka Ci Gaba Da Yin “Tafiya Bisa Ga Ruhu”?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • Kana Barin Ruhun Allah Ya Yi Maka Ja-gora Kuwa?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
w01 11/1 pp. 20-25

Jehovah Allah Ne Mai Tsawon Jimrewa

“Ubangiji, Allah ne cike da juyayi, mai-alheri kuma, mai-jinkirin fushi, mai-yalwar jinƙai.”—FITOWA 34:6.

1, 2. (a) Su wa a dā suka amfana daga tsawon jimrewa na Jehovah? (b) Menene kalmar nan “tsawon jimrewa” ke nufi?

MUTANE a zamanin Nuhu, Isra’ilawa da suka yi gantali cikin daji tare da Musa, Yahudawa a lokacin da Yesu yake duniya—dukansu sun rayu cikin yanayi dabam dabam. Amma duka sun amfana daga hali mai kyau na Jehovah—tsawon jimrewa. Ga wasu, ya kasance cetonsu. Tsawon jimrewa na Jehovah zai iya sa mu tsira mu ma.

2 Menene tsawon jimrewa? A wane lokaci Jehovah yake nuna shi, kuma me ya sa? An ba da ma’anar “tsawon jimrewa” cewa “haƙuri ne cikin jimiri game da mugunta ko ɓacin rai, da ya haɗa da ƙin fid da rai don gyara dangantakar da take ɓacewa.” Saboda haka, wannan hali yana da wata manufa. Yana la’akari ne musamman da wanda yake jawo wani yanayin jayayya. Kasancewa da tsawon jimrewa ba ya nufin yin na’am da mugunta. Yayin da aka cim ma manufar tsawon jimrewa ko kuma idan ba a bukatar a ci gaba da jimrewa da yanayin, sai tsawon jimrewa ya ƙare.

3. Menene manufar tsawon jimrewa na Jehovah, kuma yaya iyakarsa yake?

3 Ko da yake mutane suna da tsawon jimrewa, Jehovah ne misali mafi girma na wannan hali. Tun lokacin da zunubi ya ɓata dangantakar Jehovah da halittunsa mutane, Mahaliccinmu ya nuna jimrewa kuma ya yi tanadin hanyar da mutane da suka tuba za su iya gyara dangantakarsu da shi. (2 Bitrus 3:9; 1 Yohanna 4:10) Amma idan tsawon jimrewarsa ya cim ma manufarsa, Allah zai yi gāba da masu yin zunubi da gangan, ya kawo ƙarshen wannan mugun zamani.—2 Bitrus 3:7.

Daidai Yake da Muhimmin Hali na Allah

4. (a) Yaya aka bayyana ma’anar tsawon jimrewa a Nassosi na Ibrananci? (Duba hasiya.) (b) Yaya annabi Nahum ya kwatanta Jehovah, kuma menene wannan ya bayyana game da tsawon jimrewa na Jehovah?

4 A cikin Nassosin Ibrananci, tsawon jimrewa ya bayyana a kalmomi biyu na Ibrananci da a zahiri suna nufin “tsawon hanci” kuma an fassara shi “jinkirin fushi” cikin New World Translation.a Game da tsawon jimrewa na Allah, annabi Nahum ya ce: “Ubangiji mai-jinkirin fushi ne, mai-girma ne cikin iko, ba kuwa za shi kuɓutadda masu-laifi ba ko kaɗan.” (Nahum 1:3) Abin da ya sa ke nan tsawon jimrewa na Jehovah ba kumamanci ba ne kuma yana da iyaka. Gaskiyar cewa Allah mai iko duka yana jinkirin fushi kuma mai girma ne yana nuna cewa tsawon jimrewarsa sakamakon kamewa mai manufa ne. Yana da ikon ya hukunta, amma yakan ƙi yin haka nan da nan domin ya ba wa mai laifin zarafin yin gyara. (Ezekiel 18:31, 32) Saboda haka, tsawon jimrewa na Jehovah nuna ƙaunarsa ce kuma yana nuna hikimarsa a yadda yake amfani da ikonsa.

5. A wace hanya ce tsawon jimrewa na Jehovah yake jituwa da shari’arsa?

5 Tsawon jimrewa na Jehovah ya jitu da shari’arsa da kuma adalci. Ya bayyana kansa ga Musa cewa shi “Allah ne cike da juyayi, mai-alheri kuma, mai-jinkirin fushi [ko “tsawon jimrewa”], mai-yalwar jinƙai da gaskiya.” (Fitowa 34:6) Wasu shekaru daga baya, Musa ya rera waƙar yabo ga Jehovah: “Dukan tafarkunsa shari’a ne: Shi Allah mai-aminci ne, mara-mugunta, kuma, mai-adalci ne shi mai-gaskiya.” (Kubawar Shari’a 32:4) Hakika, jinƙai, tsawon jimrewa, shari’a, da adalcin Jehovah suna aiki tare cikin jituwa.

Tsawon Jimrewa na Jehovah Kafin Rigyawa

6. Wane tabbaci na tsawon jimrewa mai girma ne Jehovah ya nuna wajen ’ya’yan Adamu da Hauwa’u?

6 Tawayen da Adamu da Hauwa’u suka yi a Adnin ya ƙarar da dangantakarsu mai tamani gabaki ɗaya da Mahaliccinsu mai ƙauna, Jehovah. (Farawa 3:8-13, 23, 24) Wannan warewa ya shafi ’ya’yansu, waɗanda suka gāji zunubi, ajizanci, da kuma mutuwa. (Romawa 5:17-19) Ko da yake mata da miji na farko sun yi zunubi ne da gangan, Jehovah ya ƙyale su su haifi ’ya’ya. Daga baya, ya yi tanadin hanyar da ’ya’yan Adamu da Hauwa’u za su sulhunta da shi. (Yohanna 3:16, 36) Manzo Bulus ya bayyana: “Allah yana shaidar ƙaunatasa garemu, da shi ke, tun muna masu-zunubi tukuna, Kristi ya mutu sabili da mu. Balle fa yanzu, baratattu ne ta wurin jininsa, za mu tsira daga fushin Allah ta wurinsa. Gama idan tun muna maƙiya muka sulhuntu da Allah ta wurin mutuwar Ɗansa, balle, sulhuntattu, za mu tsira ta wurin ransa.”—Romawa 5:8-10.

7. Yaya Jehovah ya yi tsawon jimrewa kafin Rigyawan, kuma me ya sa halakar tsarar da take kafin Rigyawa daidai take?

7 An ga tsawon jimrewa na Jehovah a zamanin Nuhu. Fiye da ƙarni guda kafin Rigyawa, “Allah ya duba duniya, ga ta kuwa ɓatacciya ce; gama dukan masu-rai sun ɓata tafarkinsu a duniya.” (Farawa 6:12) Amma, Jehovah ya yi tsawon jimrewa wajen mutane na ɗan lokaci. Ya ce: “Ruhuna ba za ya riƙa ja da mutum har abada ba, gama shi kuma nama ne: amma kwanakin ransa shekara ɗari da ashirin za su zama.” (Farawa 6:3) Shekara 120 sun ba Nuhu mai aminci zarafi ya yi iyali—sai aka gaya masa umurnin Allah—ya gina jirgi kuma ya faɗakar da tsararsa game da Rigyawa da ke zuwa. Manzo Bitrus ya rubuta: “Haƙurin Allah [hali da ke kama da tsawon jimrewa] yana jinkiri a zamanin Nuhu, tun ana shirin jirgi, inda mutane kima, watau masu-rai takwas, suka tsira ta wurin ruwa.” (1 Bitrus 3:20) Hakika, waɗanda ba sa cikin iyalin Nuhu “ba su sani ba” game da wa’azin da yake yi. (Matta 24:38, 39) Amma ta sa Nuhu ya gina jirgin ya zama “mai-shelan adalci” ƙila na shekaru da yawa, Jehovah ya ba wa tsara ta zamanin Nuhu zarafi su tuba daga hanyoyinsu na mugunta kuma su juya su bauta masa. (2 Bitrus 2:5; Ibraniyawa 11:7) Yadda aka halaka muguwar tsarar nan, daidai take.

Tsawon Jimrewa Mai Kyau ga Isra’ila

8. Ta yaya Jehovah ya nuna wa al’ummar Isra’ila tsawon jimrewa?

8 Tsawon jimrewa na Jehovah ga Isra’ila ya wuce shekara 120. Duk cikin shekaru fiye da 1,500 na tarihinsu na mutanen da Allah ya zaɓa, lokatai kalilan ne kawai da Isra’ilawa ba su gwada tsawon jimrewa na Allah ba ƙwarai. Makonni ne kawai bayan da aka cece su ta hanya mai ban al’ajabi daga ƙasar Masar, suka juya zuwa bautar gumaka, suka nuna rashin biyayya ƙwarai ga Mai Cetonsu. (Fitowa 32:4; Zabura 106:21) A shekaru da yawa da suka biyo baya, Isra’ilawan suka yi gunaguni game da abinci da Jehovah ya ba su cikin hamada, suka yi gunaguni game da Musa da Haruna, suka yi wa Jehovah baƙar magana, kuma suka yi fasikanci da arna, har ma suka bauta wa Ba’al. (Litafin Lissafi 11:4-6; 14:2-4; 21:5; 25:1-3; 1 Korinthiyawa 10:6-11) Da Jehovah ya halaka mutanensa, da zai dace, amma ya nuna tsawon jimrewa.—Litafin Lissafi 14:11-21.

9. Yaya Jehovah ya kasance Allah mai tsawon jimrewa a lokacin Alƙalai da kuma a lokacin sarakuna?

9 A lokatai na Alƙalai, sau da yawa Isra’ilawa suke juyawa ga bautar gumaka. Yayin da suka yi haka, Jehovah yakan yashe su ga magabtansu. Amma yayin da suka tuba kuma suka roƙe shi, yana nuna tsawon jimrewarsa kuma ya naɗa alƙalai su cece su. (Alƙalawa 2:17, 18) A dogon lokaci na sarakuna, sarakuna kalilan ne suka yi wa Jehovah cikakkiyar ibada. Har a ƙarƙashin sarakuna masu aminci ma, sau da yawa mutanen sukan haɗa bauta ta gaskiya da ta ƙarya. Yayin da Jehovah ya ta da annabawa su yi gargaɗi saboda da rashin aminci, sai mutanen suka fi son su saurari lalatattun firistoci da annabawan ƙarya. (Irmiya 5:31; 25:4-7) Hakika, Isra’ilawan sun tsananta wa annabawan Jehovah masu aminci har ma sun kashe wasu cikinsu. (2 Labarbaru 24:20, 21; Ayukan Manzanni 7:51, 52) Duk da haka, Jehovah ya ci gaba da nuna tsawon jimrewa.—2 Labarbaru 36:15.

Tsawon Jimrewa na Jehovah Bai Ƙare Ba

10. A wane lokaci ne tsawon jimrewa na Jehovah ya kai ƙarshensa?

10 Amma, tarihi ya nuna cewa tsawon jimrewa na Allah yana da iyaka. A shekara ta 740 K.Z., ya ƙyale Assuriyawa su ci sarautar ƙabila goma ta Isra’ila kuma su kwashi mazaunansu zuwa bauta. (2 Sarakuna 17:5, 6) A ƙarshen ƙarnin da ya biyo baya, ya ƙyale Babiloniyawa suka faɗa wa sarautar ƙabila biyu na Yahuda kuma suka halaka Urushalima da haikalinta.—2 Labarbaru 36:16-19.

11. Ta yaya Jehovah ya kasance da tsawon jimrewa ko a lokacin da yake zartar da hukunci ma?

11 Har lokacin da yake zartar da hukuncinsa a kan Isra’ila da Yahuda ma, Jehovah bai manta ba ya kasance da tsawon jimrewa. Ta wurin annabi Irmiya, Jehovah ya annabta komo da zaɓaɓɓun mutanensa. Ya ce: “Bayan shekara saba’in sun cika domin Babila, zan ziyarce ku, in cika maganata mai-alheri gareku, ina komo da ku a wurin nan. Zan samu gareku, . . . in dawo da ku daga bautarku, in tattaro ku daga cikin dukan al’ummai, daga dukan wurare kuma inda na kore ku.”—Irmiya 29:10, 14.

12. Ta yaya komowar raguwar Yahudawa zuwa Yahuda ya zama ta ja-gorar Allah game da zuwan Almasihu?

12 Raguwar Yahudawa da suke bauta sun kuwa dawo zuwa Yahuda kuma suka sake fara bauta ta Jehovah a haikalin da aka sake ginawa a Urushalima. A cika nufe-nufen Jehovah, waɗannan raguwar za su zama kamar ‘raɓa daga Jehovah,’ da ke kawo wartsakewa da kuma ni’ima. Za su kuma kasance da gaba gaɗi da ƙarfi kamar “zaki a cikin namomin jeji.” (Mikah 5:7, 8) Wataƙila furcin nan sun cika a lokatan Makabi lokacin da Yahudawa ƙarƙashin iyalin Makabi suka kori magabtansu daga Ƙasar Alkawari kuma suka sake keɓe haikalin, wanda aka ƙazantar. Da haka, aka tsare ƙasar da kuma haikali don wasu raguwa masu aminci su marabci Ɗan Allah yayin da ya bayyana Almasihu.—Daniel 9:25; Luka 1:13-17, 67-79; 3:15, 21, 22.

13. Bayan da Yahudawan suka kashe Ɗansa, ta yaya Jehovah ya ci gaba da nuna musu tsawon jimrewa?

13 Har bayan da Yahudawa suka kashe Ɗansa, Jehovah ya ci gaba da nuna musu tsawon jimrewa ya ƙara musu shekara uku da rabi, yana ba su zarafi su kasance cikin zuriya ta ruhaniya na Ibrahim. (Daniel 9:27)b Kafin kuma bayan shekara ta 36 A.Z., wasu Yahudawa suka amince da wannan kira, da haka, kamar yadda Bulus ya faɗa a gaba, “ringi bisa ga zaɓen alheri.”—Romawa 11:5.

14. (a) A shekara ta 36 A.Z., ga wa aka miƙa wa gatar zama sashen zuriyar Ibrahim ta ruhaniya? (b) Ta yaya Bulus ya furta yadda yake ji game da hanyar da Jehovah yake zaɓan waɗanda ke na Isra’ila ta ruhaniya?

14 A shekara ta 36 A.Z., aka miƙa gatar zama zuriyar Ibrahim ta ruhaniya a lokaci na farko ga waɗanda suke Yahudawa ko shigaggu. Duk wanda yake son ya zama mai karɓan alherin Jehovah da tsawon jimrewa yana iya samu. (Galatiyawa 3:26-29; Afisawa 2:4-7) A nuna godiya ga hikima da kuma manufar tsawon jimrewa na Jehovah na jinƙai, wanda ta wurinsa ya samu cikakken adadin waɗanda aka kira su cika Isra’ila ta ruhaniya, Bulus ya furta da mamaki: “Ya zurfin wadata na hikimar Allah duk da saninsa! Ina misalin wuyan binciken shari’unsa, al’amuransa kuma sun fi gaban a bi sawu!”—Romawa 11:25, 26, 33; Galatiyawa 6:15, 16.

Tsawon Jimrewa Domin Sunansa

15. Menene dalili na musamman don tsawon jimrewa na Allah, kuma wace mahawara take bukatar lokaci a warware ta?

15 Me ya sa Jehovah yake nuna tsawon jimrewa? Musamman domin ya ɗaukaka sunansa mai tsarki kuma ya kunita ikonsa na mallaka. (1 Samu’ila 12:20-22) Mahawarar nan da Shaiɗan ya tayar game da hanyar da Jehovah yake amfani da Ikonsa na mallaka tana bukatar lokaci domin a warware ta sarai a gaban dukan halitta. (Ayuba 1:9-11; 42:2, 5, 6) Shi ya sa, yayin da ake zalunta mutanensa a ƙasar Masar, Jehovah ya gaya wa Fir’auna: “Saboda wannan na tsayadda kai, domin in gwada maka ikona, a sanarda sunana kuma cikin dukan duniya.”—Fitowa 9:16.

16. (a) Ta yaya tsawon jimrewa na Jehovah ya sa ya yiwu a shirya jama’a domin sunansa? (b) Ta yaya za a tsarkake sunan Jehovah kuma a kunita ikonsa na mallaka?

16 An ɗauko kalmomin Fir’auna lokacin da manzo Bulus ya yi bayanin matsayin tsawon jimrewa na Allah a ɗaukaka Sunansa mai tsarki. Sai kuma Bulus ya rubuta: “Ƙaƙa fa, idan Allah, da nufin ya gwada fushinsa, ya sanarda ikonsa kuma, da haƙuri mai-yawa ya jimre da tukwane na fushi shiryayyu ga halaka: domin kuma ya sanarda wadatar ɗaukakarsa bisa tukwane na jinƙai, waɗanda ya rigaya ya shirya su zuwa ɗaukaka, watau mu ne, waɗanda ya kira kuma, ba daga cikin Yahudawa kaɗai ba, amma daga cikin Al’ummai kuma? Kamar yadda ya faɗi cikin Hosea, Wannan wadda ba al’ummata ba ce, zan kira ta al’ummata.” (Romawa 9:17, 22-25) Saboda Jehovah ya yi tsawon jimrewa, ya ɗauko daga cikin al’ummai “wata jama’a . . . domin sunansa.” (Ayukan Manzanni 15:14) A ƙarƙashin Shugabansu, Yesu Kristi, waɗannan ‘tsarkakku’ za su gāji Mulkin da Jehovah zai yi amfani da shi ya tsarkake Sunansa mai girma kuma ya kunita Ikonsa na mallaka.—Daniel 2:44; 7:13, 14, 27; Ru’ya ta Yohanna 4:9-11; 5:9, 10.

Tsawon Jimrewa na Jehovah Yana Kawo Ceto

17, 18. (a) Ta yin menene zai zama muna sukār Jehovah ba da saninmu ba game da tsawon jimrewarsa? (b) Yaya aka ƙarfafa mu mu ji game da tsawon jimrewa na Jehovah?

17 Daga lokacin da mutum ya faɗā cikin zunubi zuwa yanzu, Jehovah ya nuna shi Allah ne mai tsawon jimrewa. Tsawon jimrewarsa kafin Rigyawan ya ba da lokaci don a faɗakar kuma don a iya samun ceto. Amma da haƙurinsa ya kai ƙarshensa, sai Rigyawar ta zo. Haka ma a yau, Jehovah yana tsawon jimrewa sosai, kuma wannan yana daɗewa fiye da yadda wasu suka yi tsammani. Amma hakan ba dalilin da zai sa a yi sanyin jiki ba ne. Yin haka zai zama kamar muna sukār Allah ne cewa me ya sa yake tsawon jimrewa. Bulus ya yi tambaya: “Kana rena wadatar alherinsa da haƙurinsa da tsawon jimrewarsa, ba ka sani ba alherin Allah yana jawo ka zuwa tuba?”—Romawa 2:4.

18 Babu wani cikinmu da zai sani sarai yawan yadda muke bukatar tsawon jimrewar Allah don mu iya samun tagomashinsa mu samu ceto. Bulus ya yi mana gargaɗi mu “yi aikin ceton[mu] da tsoro da rawan jiki.” (Filibbiyawa 2:12) Manzo Bitrus ya rubuta wa ’yan’uwa Kirista: “Ubangiji ba mai-jinkiri ba ne ga zancen alkawarinsa, yadda waɗansu mutane su ke aza jinkiri; amma mai-haƙuri ne zuwa gareku, ba shi nufin kowa da halaka ba, amma duka su kai ga tuba.”—2 Bitrus 3:9, tafiyar tsutsa tamu ce.

19. A wace hanya za mu iya yin amfani da tsawon jimrewa na Jehovah?

19 Saboda haka, kada mu yi rashin haƙuri game da yadda Jehovah yake bi da al’amura. Maimakon haka, bari mu bi gargaɗin Bitrus da ya ce mu “maida jimrewar Ubangijinmu ceto.” Ceton wa? Namu, da kuma na waɗansu da har ila suke bukatar jin “bishara kuwa ta mulki.” (2 Bitrus 3:15; Matta 24:14) Wannan zai taimake mu mu daraja yalwar tsawon jimrewa na Jehovah kuma ya motsa mu mu kasance da tsawon jimrewa a yadda muke bi da wasu.

[Hasiya]

a A Ibrananci, kalmar nan “hanci” (ʼaph) sau da yawa ana amfani da ita a alamance a nuna fushi. Haka yake domin mugun numfashi da mutum yake yi idan ya yi fushi.

b Don ƙarin bayani a kan annabcin nan, duba littafin nan Pay Attention to Daniel’s Prophecy!, shafuffuka 191-194, da Shaidun Jehovah suka buga.

Za Ka Iya Bayyanawa?

• Menene kalmar nan “tsawon jimrewa” ke nufi cikin Littafi Mai Tsarki?

• Yaya ne Jehovah ya yi tsawon jimrewarsa kafin Rigyawan, da bayan da Babila suka kwashe su ganima, da kuma a ƙarni na farko A.Z.?

• Domin waɗanne muhimman dalilai ne Jehovah ya nuna tsawon jimrewa?

• Yaya ya kamata mu ɗauki tsawon jimrewa na Jehovah?

[Hoto a shafi na 21]

Tsawon jimrewa na Jehovah kafin Rigyawan ya ba mutane isashen zarafin tuba

[Hoto a shafi na 22]

Bayan faɗuwar Babila, Yahudawa sun amfana daga tsawon jimrewa na Jehovah

[Hoto a shafi na 23]

A ƙarni na farko, Yahudawa duk da waɗanda ba Yahudawa ba sun amfana daga tsawon jimrewa na Jehovah

[Hotuna a shafi na 24]

Kiristoci a yau ma suna amfani da kyau da tsawon jimrewa na Jehovah

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba