‘Kada Ka Ji Tsoro Ni Zan Taimake Ka’
YESU ya gargaɗi mabiyansa: “Shaiɗan yana shiri ya jefa waɗansu daga cikinku a kurkuku, domin a gwada ku.” Amma, kafin ya ba da wannan gargaɗin, Yesu ya ce: “Kada ka ji tsoron wahala da za ka sha.” Tun da yake Shaiɗan ya ci gaba da yin amfani da barazanar saka mu a kurkuku domin ya sa a daina wa’azin Mulki, zai yiwu wasu gwamnatoci su tsananta wa Kiristoci na gaskiya. (R. Yoh. 2:10; 12:17) Saboda haka, menene zai taimaka mana mu kasance a shirye domin dabarun Shaiɗan kuma kada mu ji “tsoro” kamar yadda Yesu ya ƙarfafa mu?
Hakika, akwai lokacin da yawancinmu muke ɗan jin tsoro. Duk da haka, Kalmar Allah ta tabbatar da mu cewa da taimakon Jehobah, za mu guji ƙyale tsoro ya sha kanmu. Ta yaya? Hanya ɗaya da Jehobah yake taimaka mana mu yi shiri domin hamayya ita ce sanin dabarun da Shaiɗan da mabiyansa suke amfani da su. (2 Kor. 2:11) Don tabbatar da gaskiyar hakan, bari mu bincika wani abu da ya faru a lokacin da aka rubuta Littafi Mai Tsarki. Za mu kuma duba wasu misalan ’yan’uwa masu bi masu aminci na zamani waɗanda suka “yi tsayayya da dabarun Shaiɗan.”—Afis. 6:11-13.
Sarki Mai Tsoron Allah ya Fuskanci Mugun Sarki
A ƙarni na takwas K.Z., mugun Sarkin Assuriya, Sennakerib, ya ci nasarori da yawa bisa al’ummai masu yawa. Da yake waɗannan nasarorin sun shiga kansa, sai ya mai da hankalinsa ga mutanen Jehobah da babban birninsu, Urushalima, inda sarki Hezekiya mai tsoron Allah yake sarauta. (2 Sar. 18:1-3, 13) Babu shakka, Shaiɗan yana amfani da wannan damar, yana zuga Sennakerib don ya cim ma manufofinsa, domin a kawar da bauta ta gaskiya daga doron duniya.—Far. 3:15.
Sennakerib ya aika tawagarsa zuwa Urushalima yana cewa su ba da kansu. Rabshakeh yana cikin tawagar, kuma shi ne kakakin sarkin.a (2 Sar. 18:17) Muradin Rabshakeh shi ne ya sa Yahudawa su yi sanyin gwiwa kuma su ba da kansu ba tare da yin yaƙi ba. Waɗanne dabaru ne Rabshakeh ya yi amfani da su don ya tsorata Yahudawa?
Sun Kasance da Aminci Duk da Kaɗaita
Rabshakeh ya gaya wa wakilan Hezekiah: “In ji babban sarki, sarkin Assyria, Menene wannan ƙarfinka da ka ke dogara gareshi haka nan? Ga shi, kana dogara ga karan wannan gora, rarraunan gora ke nan, Masar; abin da mutum ko ya dogara gareshi, ya shiga hannunsa, ya soke shi.” (2 Sar. 18:19, 21) Tuhumar Rabshakeh ƙarya ce, gama Hezekiya bai yi kawance da Masar ba. Duk da haka, tuhumar ta nanata abin da Rabshakeh yake son Yahudawa su tuna sarai: ‘Babu wanda zai taimake ku. Kuna a ware.’
A kwanakin nan, masu hamayya da bauta ta gaskiya suna yin amfani da barazanar kaɗaici domin su sa Kiristoci na gaskiya su tsorata. Wata ’yar’uwa Kirista da aka saka a kurkuku domin bangaskiyarta kuma aka ware ta daga ’yan’uwa masu bi shekaru da yawa, ta faɗa abin da ya taimake ta don kada tsoro ya sha kanta. Ta ce: “Addu’a ta taimaka mini in kusaci Jehobah . . . Na tuna tabbacin da ke Ishaya 66:2, cewa Allah yana kula da ‘talaka mai-karyayyen ruhu.’ Hakan yana ƙarfafa ni sosai a kowane lokaci.” Hakazalika, wani ɗan’uwa da ya yi shekaru yana tsare shi kaɗai ya ce: “Na fahimci cewa ƙaramin ɗakin kurkuku zai iya zama sararin samaniya idan mutum yana da dangantaka na kud da kud da Allah.” Hakika, kasancewa da dangantaka na kud da kud da Jehobah ya ba waɗannan Kiristoci biyu ƙarfin da suke bukata don su jimre da kaɗaici. (Zab. 9:9, 10) Masu tsananta musu suna iya ware su daga iyali, abokai, da kuma ’yan’uwa masu bi, amma Shaidu da aka ɗaure sun san cewa masu hamayya da su ba za su iya ware su daga Jehobah ba.—Rom. 8:35-39.
Saboda haka, yana da muhimmanci mu yi amfani da kowane zarafi da muke da shi don mu ƙarfafa dangantakarmu da Jehobah! (Yaƙ. 4:8) Ya kamata mu riƙa tambayar kanmu a kai a kai: ‘Na san Jehobah sosai kuwa? Kalmominsa suna shafan yadda nake tsai da shawarwari, ƙanana da manya a rayuwata na yau da kullum?’ (Luk 16:10) Idan muka ƙoƙarta sosai don mu ci gaba da riƙe dangantakarmu na kud da kud da Allah, ba mu da wani dalilin jin tsoro. Annabi Irmiya da yake magana a madadin Yahudawa talakawa, ya ce: “Daga cikin zurfin ɗakin duhu na kira sunanka, ya Ubangiji, . . . A ran da na yi kiranka kā guso: ka ce, Kada ka ji tsoro.”—Mak. 3:55-57.
Ƙoƙarin Sa Su Yin Shakka Bai Yi Nasara Ba
Rabshakeh ya yi amfani da tunanin ruɗu don ya sa mutanen yin shakka. Ya ce: “Ko ba shi [Jehobah] ba ne wanda Hezekiah ya kawasda masujadansa da bagadansa, . . . Ubangiji ne ya ce mani, Je ka, ka yi yaƙi da wannan ƙasa, ka hallaka ta.” (2 Sar. 18:22, 25) Da haka, Rabshakeh yana cewa Jehobah ba zai yi yaƙi don mutanensa ba domin yana fushi da su. Amma hakan ba gaskiya ba ne. Jehobah yana farin ciki da Hezekiah da kuma Yahudawan da suka komo ga bauta ta gaskiya.—2 Sar. 18:3-7.
A yau, masu hamayya suna iya faɗin gaskiya sama-sama don mu yarda da su, amma da dabara suna haɗa wannan gaskiyar da ƙarya da zaton cewa za su sa mu yi shakka. Alal misali, a wasu lokatai an gaya wa ’yan’uwa maza da mata da aka ɗaure a kurkuku cewa ɗan’uwan da yake ja-gora a ƙasarsu ya karya imaninsa, saboda haka zai dace su ma su yi hakan kuma su yi watsi da imaninsu. Amma, irin wannan tunanin ba ya sa Kiristoci masu fahimi shakka.
Ka yi la’akari da abin da ya faru da wata ’yar’uwa Kirista a lokacin Yaƙin Duniya na biyu. Sa’ad da take kurkuku, an nuna mata wani kalami da ya nuna cewa wani ɗan’uwa mai gata ya daina bin imaninsa. Mai tuhumarta ya tambaye ta ko ta gaskata da wannan Mashaidin. ’Yar’uwar ta amsa, “Shi ajizi ne.” Ta daɗa cewa muddin yana bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki, Allah ya yi amfani da shi. “Amma tun da kalamansa sun bijire daga Littafi Mai Tsarki, shi ba ɗan’uwa na ba ne.” Cikin hikima wannan ’yar’uwar mai aminci ta bi gargaɗin da ke cikin Littafi Mai Tsarki: “Kada ku dogara ga sarakuna, ko kuwa ɗan adam, wanda babu taimako gareshi.”—Zab. 146:3.
Samun cikakken sani na Kalmar Allah da kuma yin amfani da gargaɗinsa zai taimaka mana mu guji tunanin ruɗu da zai iya raunana ƙudurinmu na jimrewa. (Afis. 4:13, 14; Ibran. 6:19) Saboda haka, don mu kasance a shirye domin yin tunani mai kyau sa’ad da muke fuskantar matsi, muna bukatan mu mai da hankali sosai ga karanta Littafi Mai Tsarki a kullum da kuma nazari na kanmu. (Ibran. 4:12) Hakika, yanzu ne lokacin zurfafa saninmu da kuma ƙarfafa bangaskiyarmu. Wani ɗan’uwa da ya jimre tsari na kaɗaici na shekaru da yawa ya ce: “Zan so in ƙarfafa kowa ya fahimci muhimmancin dukan abinci na ruhaniya da ake ba mu, domin ba mu san yadda hakan zai amfane mu a nan gaba ba.” Hakika, idan muna yin nazarin Kalmar Allah sosai da kuma littattafan da rukunin bawan nan suke tanadinsa a yau, sa’ad da muka fuskanci matsaloli masu tsanani a rayuwa, ruhu mai tsarki “zai tuna [mana]” abin da muka koya.—Yoh. 14:26.
An Kāre Su a Lokacin Razana
Rabshakeh ya yi ƙoƙarin ya razanar da Yahudawa. “Ina roƙonka, ka yi wa’adin caca da ubangijina sarkin Assyria,” in ji shi, “in ba ka dawakai alfin, idan kai wajen naka ka sa masu mahaya. Ya’ya fa za ka iya juyar da fuskar jarumi guda ɗaya daga cikin mafi-ƙanƙantan bayi na ubangijina.” (2 Sar. 18:23, 24) Bisa ra’ayin ’yan adam, babu yadda Hezekiah da mutanensa za su yi nasara a kan runduna mai ƙarfi na Assuriya.
Masu hamayya a yau suna iya bayyana kamar suna da ƙarfi sosai, musamman sa’ad da Gwamnati take goyon bayansu. Abin da ya faru ke nan da ’yan Nazi masu hamayya a lokacin Yaƙin Duniya na biyu. Sun yi ƙoƙarin su tsoratar da bayin Allah da yawa. Ɗaya daga cikin ’yan’uwanmu, da ya yi shekaru da yawa a fursuna, ya kwatanta yadda aka yi masa barazana. Akwai lokacin da wani hafsa ya tambaye shi: “Ka ga yadda aka kashe ƙaninka? Wane darassi ka koya daga wannan?” Amsarsa ita ce: “‘Ni mashaidin Jehobah ne kuma zan ci gaba da zama hakan.” ‘Sai hafsan ya yi masa barazana, ‘Saura kai ke nan za mu kashe.” Duk da haka, ɗan’uwanmu ya yi tsayin daka, kuma magabcin ya daina yin ƙoƙari ya tsoratar da shi. Menene ya taimaka masa ya kasance da aminci sa’ad da yake fuskantar barazana? Ya amsa: “Na dogara ga sunan Jehobah.”—Mis. 18:10.
Ta wajen kasancewa da cikakkiyar bangaskiya ga Jehobah, muna ɗaukan garkuwa mai girma da ke tsare mu daga dukan abubuwan da Shaiɗan yake amfani da su don ya yi mana lahani a ruhaniya. (Afis. 6:16) Shi ya sa yake da kyau mu gaya wa Jehobah cikin addu’a ya taimaka mana mu ƙarfafa bangaskiyarmu. (Luk 17:5) Muna bukatan kuma mu yi amfani sosai da tanadin da rukunin bawan nan suka yi don mu ƙarfafa bangaskiyarmu. Sa’ad da muke fuskantar barazana, muna samun ƙarfafa sa’ad da muka tuna tabbacin da Jehobah ya ba annabi Ezekiel, wanda ya faɗi saƙo ga mutane masu taurin kai. Jehobah ya gaya masa: “Na ƙarfafa fuskarka daidai kamar tasu: na taurare kanka kuma har da za ya iya tsayayya da nasu. Na sa kanka ya yi ƙarfi kamar dutse, har ma ya fi dutsen ƙanƙara ƙarfi.” (Ezek. 3:8, 9) Idan da bukata, Jehobah zai taimaka mana mu yi ƙarfi kamar dutse kamar yadda Ezekiel ya yi ƙarfi.
Tsayayya wa Gwaje-Gwaje
Masu hamayya sun gano cewa idan ba su yi nasara ba a dukan dabarun da suka yi amfani da su, gwajin ba da lada a wani lokaci zai sa mutum ya yi rashin aminci. Rabshakeh ya yi amfani da wannan dabarar. Ya gaya wa waɗanda suke Urushalima: “In ji sarkin Assyria, Ku yi amana da ni, ku fito zuwa wurina . . . Har in zo in ɗauke ku, in kai ku wata ƙasa makwatanciyar taku, ƙasa mai-hatsi da ruwan anab, ƙasar gurasa da gonakin anab, ƙasa mai-itatuwan zaitun, mai-zuma kuma, domin ku rayu, kada ku mutu.” (2 Sar. 18:31, 32) Tunanin cin gurasa da shan ruwan inabi zai kasance abin marmari ga waɗanda suke cikin garun birnin da aka kewaye!
Akwai lokaci da aka yi amfani da wannan don a raunana ƙudurin wani mai wa’azi a ƙasar waje da yake kurkuku. An gaya masa cewa za a kai shi wani “gida mai kyau” da ke cikin wani “lambu mai kyau” har tsawon watanni shida don ya yi tunani. Amma, ɗan’uwan ya kasance a faɗake a ruhaniya kuma bai yasar da ƙa’idodinsa na Kirista ba. Menene ya taimake shi? Ya bayyana daga baya: “Na ɗauki Mulkin a matsayin bege na ainihi. . . . Domin ina da cikakken sani game da mulkin Allah, na tabbata da hakan, kuma ban taɓa yin shakka ba ko na ɗan lokaci, hakan ya sa suka kasa rinjayana in yi rashin aminci.”
Mun gaskata da Mulkin Allah kuwa? Uban iyali Ibrahim, manzo Bulus, da Yesu sun jimre gwaje-gwaje masu wuya domin sun gaskata da Mulkin. (Filib. 3:13, 14; Ibran. 11:8-10; 12:2) Idan muka ci gaba da saka Mulkin farko a rayuwarmu kuma muka sa madawwamin ladarsa a zuciya, mu ma za mu iya tsayayya wa gwaji na samun sauƙi na ɗan lokaci daga gwaji.—2 Kor. 4:16-18.
Jehobah Ba Zai Yasar da Mu Ba
Duk da ƙoƙarin da Rabshakeh ya yi don ya tsoratar da Yahudawa, Hezekiah da talakawansa sun dogara sosai ga Jehobah. (2 Sar. 19:15, 19; Isha. 37:5-7) Jehobah ya amsa addu’o’insu na taimako ta wajen aika mala’ika guda ya halaka runduna 185,000 a cikin dare ɗaya a sansanin Assuriyawa. Washegari, cike da kunya, Sennakerib ya hanzarta zuwa babban birninsa, Nineba, da rundunarsa kaɗan da suka rage.—2 Sar. 19:35, 36.
Babu shakka, Jehobah bai yasar da waɗanda suka dogara da shi ba. Misalai na zamani na ’yan’uwanmu da suka yi tsayin daka sa’ad da suke fuskantar gwaji sun nuna cewa Jehobah ba ya yasar da mutanensa a yau. Saboda haka, da dalili mai kyau Ubanmu na Samaniya ya tabbatar da mu cewa: “Ni Ubangiji Allahnka zan riƙe hannun damanka, in ce maka, kada ka ji tsoro, ni taimake ka.”—Isha. 41:13.
[Hasiya]
a “Rabshakeh” laƙabi ne na sanannen ma’aikaci a gwamnatin Assuriya. Ba a faɗi sunan mutumin ba a cikin labarin.
[Bayanin da ke shafi na 13]
Jehobah da kansa ya tabbatar wa bayinsa fiye da sau 30 a cikin Kalmarsa cewa: “Kada ka ji tsoro”
[Hoton da ke shafi na 12]
Ta yaya ne dabarun Rabshakeh suka yi daidai da waɗanda magabtan mutanen Allah suka yi amfani da su a yau?
[Hotuna da ke shafi na 15]
Dangantaka na kud da kud da Jehobah yana taimaka mana mu kasance da aminci sa’ad da muke fuskantar gwaji