Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu
Saꞌad da Dauda ya rubuta kalmomin da ke Zabura 61:8 cewa zai rera yabon sunan Allah “har abada,” yana nufin cewa yana ganin ba zai taɓa mutuwa ba ne?
Aꞌa. Abin da Dauda ya rubuta gaskiya ne.
Ka yi laꞌakari da abin da ya rubuta a ayar nan da kuma wasu ayoyi. Ya ce: “Zan rera yabon Sunanka har abada, yayin da nake cika rantsuwata kowace rana.” “Ya Ubangiji Allahna, zan yabe ka da dukan zuciyata, zan ɗaukaka Sunanka har abada.” “Zan yabi Sunanka har abada abadin.”—Zab. 61:8; 86:12; 145:1, 2.
Dauda bai rubuta kalmomin nan domin yana tunanin cewa ba zai mutu ba. Ya san cewa ꞌyan Adam za su mutu domin sun yi zunubi, kuma Dauda ya amince cewa shi mai zunubi ne. (Far. 3:3, 17-19; Zab. 51:4, 5) Ya kuma san cewa amintattun mutane kamar Ibrahim da Ishaku da kuma Yakub ma sun riga sun mutu. Saboda haka, Dauda ya san cewa shi ma zai mutu. (Zab. 37:25; 39:4) Amma kalmomin da ya rubuta a Zabura 61:8 sun nuna cewa yana so ya yabi Allah har abada, wato har iyakacin rayuwarsa.—2 Sam. 7:12.
A wasu lokuta, Dauda ya yi rubutu a kan abubuwan da ya fuskanta a rayuwarsa ne, kamar yadda muka gani a Zabura 18, 51, da 52. A Zabura 23, Dauda wanda shi ma makiyayi ne, ya kwatanta Jehobah a matsayin makiyayi wanda yake yi masa ja-goranci, yake ƙarfafa shi kuma yake kāre shi. Hakan ya sa Dauda ya so ya bauta ma Allah a ‘dukan kwanakin ransa.’—Zab. 23:6.
Ka tuna cewa Jehobah ne ya sa Dauda ya rubuta dukan abubuwan da ya rubuta. Abubuwan da ya rubuta sun ƙunshi abubuwan da za su faru a nan gaba. Alal misali, a Zabura 110, Dauda ya yi rubutu a kan lokacin da Ubangijinsa ya zauna a hannun damar Allah a sama kuma ya karɓi iko. Mene ne zai yi da ikon? Zai hallaka maƙiyan Allah kuma ya “yanke wa alꞌummai shariꞌa” a duniya. Dauda kakan-kakannin Almasihu ne wanda zai yi sarauta daga sama, kuma zai zama ‘firist na har abada.’ (Zab. 110:1-6) Yesu ya ce annabcin da aka yi a Zabura 110 game da shi ne, kuma zai sake cika a nan gaba.—Mat. 22:41-45.
Jehobah ne ya sa Dauda ya yi rubutu a kan abin da ke faruwa a lokacinsa, da abin da zai faru a nan gaba a lokacin da za a tā da shi kuma ya yabe Jehobah har abada. Hakika, abin da aka rubuta a Zabura 37:10, 11, 29 ya shafi lokacin da aka rubuta su da kuma abin da zai faru a nan gaba. Abubuwa da aka ambata a ayoyin nan sun faru a a ƙasar Israꞌila ta dā kuma za su sake faruwa a lokacin da Allah zai cika alkawuransa a gaba.—Ka duba sakin layi na 8 a talifin nan “Za Ka Kasance Tare da Ni a Aljanna” a wannan fitowar.
Zabura 61:8 da ma wasu ayoyi sun nuna cewa Dauda ya so ya yabe Jehobah a zamanin Israꞌilawa har iyakacin rayuwarsa. Kuma sun nuna abin da Dauda zai iya yi a nan gaba, lokacin da Jehobah zai tā da shi daga mutuwa.