Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w08 8/15 p. 29
  • Ka Tuna?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Tuna?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Makamantan Littattafai
  • Yadda Aka Tsara Hukumar Mulki
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Su Waye ne Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah?
    Tambayoyin da Ake Yawan Yi
  • Ku Rika “Girmama Irin Waɗannan Mutane”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
  • Magance Matsaloli
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
w08 8/15 p. 29

Ka Tuna?

Ka yi farin cikin karanta fitowar Hasumiyar Tsaro na kwanan nan? Ka ga ko za ka iya amsar waɗannan tambayoyin:

• Waɗanne ƙalubale masu tsanani ne wasu Kiristoci suke fuskanta bayan sun yi aure, kuma menene ya kamata su yi ƙoƙari su yi?

Wasu Kiristoci za su ga cewa ba su jitu da abokin aurensu ba. Da yake sun san cewa ba a amince da kisan aure da ba bisa Nassi ba, suna bukatar su yi ƙoƙari su riƙe aurensu.—4/15, shafi na 17.

• Waɗanne ƙalubale ne Kirista da yake inda ake kula da tsofaffi yake fuskanta?

Wataƙila bai san ikilisiyar da ke inda yake ba. Yawanci mutanen da ke wajen suna iya kasancewa da imani dabam dabam, kuma suna iya sa shi ya soma sa hannu cikin ayyukan addini. Ya kamata dangi da Kiristoci ne da kuma waɗanda suke cikin ikilisiya su san abin da ke faruwa kuma su ba da taimako da kulawa.—4/15, shafuffuka 25-27.

• Waɗanne matakai huɗu ne za su taimaki ma’aurata su magance matsalolinsu?

Ku keɓe lokacin da za ku tattauna batun. (M. Wa. 3:1, 7) Ku faɗi gaskiyar yadda kuke ji kuma ku yi hakan cikin ladabi. (Afis. 4:25) Ka saurari matarka kuma ka yi la’akari da yadda take ji. (Mat. 7:12) Ku tattauna yadda za ku magance matsalar, kuma ku haɗa hannu don cim ma hakan. (M. Wa. 4:9, 10)—5/1, shafuffuka 10-12.

• Sa’ad da Yesu ya aririce mu mu yi addu’a a gafarta mana basussuwanmu, waɗanne basusuwa yake nufi?

Matta 6:12 da Luka 11:4, sun nuna sarai cewa Yesu ba ya nufin bashin kuɗi. Yana nufin zunubai. Muna bukatar mu yi koyi da Allah ta wajen kasancewa a shirye mu gafarta wa mutane.—5/15, shafi na 9.

• A waɗanne kwamiti ne Hukumar Mulki suke hidima a ciki?

Kwamitin Mai Kula; Kwamitin Ma’aikata; Kwamitin Buga Littattafai; Kwamitin Hidima; Kwamitin Koyarwa; Kwamitin Rubuce-Rubuce.—5/15, shafi na 29.

• Ta yaya muka san cewa Rigyawa na zamanin Nuhu ta shafi dukan duniya?

Yesu ya gaskata cewa Rigyawar ta faru kuma ta shafi dukan duniya. Gargadin da ke cikin Littafi Mai Tsarki sun nuna cewa Rigyawar ta faru da gaske.—6/1, shafi na 8.

• Halin da aka kwatanta a Romawa 1:24-32 yana nuni ga Yahudawa ko kuwa ’yan Al’umma?

Kwatancin yana iya dacewa da kowannensu, amma ainihi manzo Bulus yana maganar Isra’ilawa ta dā ne da suka ƙi bin Dokar Allah. Sun san dokokin Allah, duk da haka ba su bi su ba.—6/15, shafi na 29.

• Me ya sa yin abubuwa da za mu iya zai iya ƙara farin cikinmu?

Idan muka yi ƙoƙarin cim ma makasudan da suka fi ƙarfinmu, muna saka kanmu cikin matsi da bai dace ba. Duk da haka, bai kamata mu ƙasƙantar da kanmu ba, ta wajen rage hidimarmu don kasawarmu.—7/15, shafi na 29.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba