Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w14 5/15 pp. 21-25
  • Jehobah Allah Ne Mai Tsari

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Jehobah Allah Ne Mai Tsari
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • YADDA ALLAH YA TSARA MUTANENSA A DĀ
  • YADDA JEHOBAH YA TSARA KIRISTOCI A ƘARNI NA FARKO
  • MUTANE DA YAWA SUN HALAKA, AMMA BAYIN ALLAH SUN TSIRA
  • Kana Bin Ƙungiyar Jehobah Sau da Kafa Kuwa?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Ina Ya Kamata Ka Kasance Sa’ad da Ƙarshe Ya Zo?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Jehobah Yana Yi wa Kungiyarsa Ja-goranci
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2020
  • Me Ya Sa Allah Yake da Ƙungiya?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
w14 5/15 pp. 21-25

Jehobah Allah Ne Mai Tsari

“Allah ba Allah na yamutsai ba ne, amma na kwanciyar rai ne.”—1 KOR. 14:33.

MECE CE AMSARKA?

  • Ta yaya Jehobah ya tsara halittu na ruhu da kuma na zahiri da ke sama?

  • Me ya sa Jehobah ya ceci Nuhu da Rahab?

  • Ta yaya labaran Isra’ila ta dā da kuma Kiristoci na ƙarni na farko suka nuna cewa Jehobah Allah ne mai tsari?

1, 2. (a) Waye ne Allah ya fara halitta, kuma ta yaya ya yi amfani da shi? (b) Me ya nuna cewa mala’iku suna da tsari sosai?

JEHOBAH, Mahaliccin dukan abu yana yin abubuwa bisa tsari. Abin da ya fara halitta shi ne Ɗansa Yesu. Littafi Mai Tsarki ya kira Yesu “Kalma” domin shi ne babban wakilin Allah. Littafi Mai Tsarki ya ce: “A cikin farko akwai Kalma, Kalman kuwa tare da Allah ne.” Ya yi wa Allah hidima a sama na shekaru aru-aru. Littafi Mai Tsarki ya ƙara da cewa: “Ta wurinsa [Kalmar] aka yi dukan abu; ba a yi komi ba cikin abin da an yi, sai ta wurinsa.” Fiye da shekaru 2,000 da suka shige, Allah ya aiko da Kalmar nan wato, Yesu Kristi zuwa duniya a matsayin kamiltaccen mutum. Kuma Yesu ya yi dukan abin da Ubansa ya gaya masa ya yi.—Yoh. 1:1-3, 14.

2 Yesu ya yi wa Allah hidima da aminci a matsayin “gwanin mai-aiki” kafin ya zo duniya. (Mis. 8:30) Allah ya yi amfani da Yesu ne wajen halittar miliyoyin mala’iku a sama. (Kol. 1:16) Littafi Mai Tsarki ya gaya mana yadda Allah ya tsara mala’ikunsa. Ya ce: “Dubban dubbai kuma suna yi masa hidima: zambar goma kuma so zambar goma suna tsaye a gabansa.” (Dan. 7:10) Hakika, Littafi Mai Tsarki ya kwatanta yadda Jehobah ya tsara mala’iku a matsayin ‘runduna.’—Zab. 103:21.

3. Taurari nawa ne muke da su, kuma yaya aka tsara su?

3 A lokacin da Allah ya halicci sararin sama, ya yi taurari masu yawan gaske. Su nawa ke nan? Wata jarida mai suna Chronicle, da ake bugawa a birnin Houston, a jihar Texas, ya ce masana kimiyya sun yi bincike kwanan nan kuma suna ganin akwai taurari da duniyoyi tiriliyan uku sau biliyan ɗari a sararin sama, ma’ana suna da yawan gaske. An tsara taurari dami-dami kuma kowane dami na ɗauke da taurari biliyoyi ko kuma tiriliyoyi. An tsara yawancin dami-damin taurari cikin wasu dami-dami masu girma sosai.

4. Ta yaya muka sani cewa Allah ya tsara mutanensa a nan duniya?

4 An tsara mala’iku da kuma taurari da ke sama da kyau sosai. (Isha. 40:26) Saboda haka, muna da tabbaci cewa Jehobah ya tsara bayinsa da ke duniya ma. Allah yana son su ci gaba da bin wannan tsarin. Hakan yana da muhimmanci don yana da babban aiki da yake so su yi masa. Jehobah ya tsara bayinsa a shekaru da yawa don su iya bauta masa da aminci. Kuma muna da misalai da yawa da suka nuna cewa Allah yana tare da su kuma shi “ba Allah na yamutsai ba ne, amma na kwanciyar rai ne.”—Karanta 1 Korintiyawa 14:33, 40.

YADDA ALLAH YA TSARA MUTANENSA A DĀ

5. Ta yaya aka rugurguje nufin Allah ga duniya?

5 A lokacin da Allah ya halicci mutane na farko, ya gaya musu: “Ku yalwata da ’ya’ya, ku riɓu, ku mamaye duniya, ku mallake ta; ku yi mulkin kifaye na teku, da tsuntsaye na sarari, da kowane abu mai-rai wanda ke rarrafe a ƙasa.” (Far. 1:28) Allah ya so mutane su yalwata da ’ya’ya bisa tsari don su cika duniya kuma su mai da ita Aljanna. Adamu da Hawwa’u sun rugurguje wannan tsarin sa’ad da suka yi zunubi. (Far. 3:1-6) Da sannu-sannu, “Ubangiji ya ga muguntar mutum ta yi yawa cikin duniya, kuma kowacce shawara ta tunanin zuciyarsa mugunta ce kaɗai kullayaumi.” A sakamakon haka, “duniya kuwa ta ɓāci a gaban Allah, duniya kuma ta cika da zalunci.” Saboda haka, Allah ya ce zai halaka miyagun mutane da rigyawa.—Far. 6:5, 11-13, 17.

6, 7. (a) Me ya sa Jehobah ya ceci Nuhu? (Ka duba hoto na farko.) (b) Me ya faru da mutane marasa bangaskiya na zamanin Nuhu?

6 Amma “Nuhu ya sami tagomashi a gaban Ubangiji” domin shi “mutum mai-adalci ne” kuma “mara-aibi ne cikin tsararakinsa.” Nuhu ya yi “tafiya tare da Allah,” saboda haka, Jehobah ya umurce shi ya gina babban jirgi. (Far. 6:8, 9, 14-16) An tsara jirgin a hanyar da zai kasance a saman ruwa don kada mutane da kuma dabbobi da ke cikinsa su mutu. Nuhu ya yi dukan abin da Allah ya gaya masa ya yi. Da ya shigar da dabbobi cikin jirgi, sai “Ubangiji kuma ya rufe” ƙofar jirgin.—Far. 7:5, 16.

7 Jehobah ya “shafe kowane abu mai-rai wanda ke a fuskar ƙasa” sa’ad da aka yi rigyawa a shekara ta 2370 kafin zamaninmu, amma Nuhu da iyalinsa ne kaɗai suka tsira daga rigyawar. (Far. 7:23) Kowa da ke raye a yau ya fito daga zuriyar Nuhu ne. Amma dukan mutane marasa bangaskiya da ba su shiga cikin jirgin ba sun halaka, don sun ƙi su saurari Nuhu “mai-shelan adalci.”—2 Bit. 2:5.

8. Mene ne ya nuna cewa Isra’ilawa suna da tsari sosai sa’ad da Jehobah ya umurce su su shiga Ƙasar Alkawari?

8 Sama da ƙarnuka takwas bayan Rigyawar, Allah ya shirya mutanensa a matsayin al’umma. Yadda Allah ya tsara su ya shafi dukan fannonin rayuwarsu, musamman ma yadda ya kamata su bauta masa. Alal misali, ya naɗa wasu daga cikin firistoci da Lawiyawa. Ƙari ga haka, ya shirya wasu mata su yi “hidima a bakin ƙofar tent na taruwa.” (Fit. 38:8) Amma, sa’ad da Jehobah ya umurci mutanen su shiga Kan’ana, wannan tsarar ta yi rashin biyayya kuma ya gaya musu: “Ba za ku shiga ƙasa wadda na rantse zan ba ku ita, ku zauna a ciki, sai Kaleb ɗan Jephunneh, da Joshua ɗan Nun kaɗai” don sun kawo rahoto mai kyau da suka dawo daga leƙen Ƙasar Alkawari. (Lit. Lis. 14:30, 37, 38) Daga baya, Musa ya bi umurnin Allah kuma ya naɗa Joshua a matsayin wanda zai maye gurbinsa. (Lit. Lis. 27:18-23) Sa’ad da Joshua yake so ya ja-goranci Isra’ilawa su shiga cikin Kan’ana, Jehobah ya ce masa: “Ka ƙarfafa; ka yi ƙarfin zuciya kuma; kada ka tsorata, kada ka yi fargaba kuma: gama Ubangiji Allahnka yana tare da kai dukan inda ka nufa.”—Josh. 1:9.

9. Yaya Rahab ta ɗauki Jehobah da mutanensa?

9 Hakika, Jehobah ya kasance da Joshua duk inda ya je. Alal misali, ka yi la’akari da abin da ya faru sa’ad da Isra’ilawa suka ya da zango kusa da birnin Jericho da ke ƙasar Kan’ana. A shekara ta 1473 kafin zamaninmu, Joshua ya aika mutane biyu su leƙa asirin Jericho, kuma suka sauka a gidan wata karuwa mai suna Rahab. Sarkin ya aika a kamo waɗannan masu leƙen asirin birnin, amma Rahab ta ɓoye su a cikin rufin gidanta. Sai ta ce musu: “Na sani Ubangiji ya rigaya ya ba ku ƙasar. . . . Gama mun ji yadda Ubangiji ya shanyar da ruwan Jan Teku a gabanku . . . , da abin da kuka yi wa sarakuna biyu ɗin nan na Amoriyawa.” Ta ƙara da cewa: “Gama Ubangiji Allahnku, shi ne Allah cikin sama a bisa, da duniya a ƙasa.” (Josh. 2:9-11) Da yake Rahab ta goyi bayan mutanen Allah a lokacin, Allah ya cece ta da iyalinta sa’ad da aka ci Jericho da yaƙi. (Josh. 6:25) Rahab ta ba da gaskiya kuma ta girmama Jehobah da mutanensa.

YADDA JEHOBAH YA TSARA KIRISTOCI A ƘARNI NA FARKO

10. Mene ne Yesu ya gaya wa shugabannin Yahudawa na zamaninsa, kuma me ya sa ya yi wannan furucin?

10 A lokacin da Joshua yake ja-gorar Isra’ilawa, sun ci biranen ƙasar Kan’ana kuma sun mamaye ƙasar gaba ɗaya. Amma mene ne ya faru daga baya? A shekaru da yawa da suka biyo baya, Isra’ilawa suka yi ta karya dokokin Allah. Sa’ad da Jehobah ya aiko da Ɗansa zuwa duniya, karya dokokin Allah ya riga ya shiga jinin Isra’ilawa har suka ƙi su saurari Yesu. Saboda haka, Yesu ya ce da su masu “kisan annabawa.” (Karanta Matta 23:37, 38.) Allah ya yi watsi da shugabannin Yahudawa don rashin bangaskiyarsu. Shi ya sa Yesu ya gaya musu: “Za a amshe Mulkin Allah daga hannunku, za a bayar ga al’umma mai-fitowa da ’ya’yansa.”—Mat. 21:43.

11, 12. (a) Me ya nuna cewa Jehobah ya daina harka da al’ummar Isra’ila kuma ya albarkaci wata ƙungiya a ƙarni na farko? (b) Wannan sabuwar ƙungiyar ta ƙunshi su waye ne?

11 A ƙarni na farko a zamaninmu, Jehobah ya yasar da al’ummar Isra’ila don rashin bangaskiyarsu. Duk da haka, ya tsara mutane masu bangaskiya da suka bi Kristi da kuma koyarwarsa. Jehobah ya daina harka da al’ummar Isra’ila kuma ya albarkaci wannan sabuwar ƙungiyar. Ta yaya aka samu wannan ƙungiyar? A shekara ta 33 a zamaninmu, almajiran Yesu guda 120 sun taru a Urushalima, “farat ɗaya sai aka ji wani amo daga sama, kamar na busowar gawurtacciyar iska, ya cika duk gidan. Sai waɗansu harsuna kamar na wuta suka bayyana a gare su, suna rarrabuwa, suna sassauka a kan kowannensu. Sai duk, aka cika su da Ruhu Mai Tsarki, suka kuma fara magana da waɗansu harsuna dabam dabam, gwargwadon yadda Ruhun ya yi musu baiwar yin magana.” (A. M. 2:1-4, Littafi Mai Tsarki) Wannan abin al’ajabin da ya faru ya nuna cewa tabbas, Jehobah yana tare da wannan sabuwar ƙungiyar da ta ƙunshi almajiran Kristi.

12 A wannan ranar, wajen mutane 3,000 ne suka soma tarayya da ƙungiyar Jehobah a matsayin mabiyan Yesu. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ubangiji kuma yana tattarawa yau da gobe waɗanda a ke cetonsu.” (A. M. 2:41, 47) Almajiran Yesu sun yi nasara sosai a aikin wa’azi kuma Littafi Mai Tsarki ya ce: “Maganar Allah kuwa ta yawaita; yawan masu-bi kuma cikin Urushalima ya riɓanɓanya ƙwarai.” Har ma “babban taro kuma na malamai suka yi biyayya ga imanin.” (A. M. 6:7) Mutane da yawa masu zuciyar kirki suka amince da koyarwar Yesu da wannan sabuwar ƙungiyar take wa’azinsa. Daga baya Jehobah ya nuna goyon bayansa ga ikilisiyar Kirista sa’ad da ’yan “alummai” suka soma ba da gaskiya.—Karanta Ayyukan Manzanni 10:44, 45.

13. Mene ne aikin sabuwar ƙungiyar Allah?

13 A bayyane yake cewa Allah ya ba wa mabiyan Yesu wani aiki na musamman. Sa’ad da Yesu yake duniya, ya kafa wa mabiyansa misali. Bayan da aka yi masa baftisma, Yesu ya soma wa’azi game da “Mulkin sama.” (Mat. 4:17) Ya kuma umurci mabiyansa su yi hakan. Ya ce musu: “Za ku zama shaiduna kuma cikin Urushalima da cikin dukan Yahudiya da Samariya, har kuma iyakan duniya.” (A. M. 1:8) Waɗannan mabiyan Yesu sun fahimci abin da ya kamata su yi. Alal misali, a Antakiya na Bisidiya, Bulus da Barnaba sun faɗa wa Yahudawa masu hamayya da gaba gaɗi cewa: “Ku, ya wajaba a fara yi wa Maganar Allah, amma da ya ke kun ture ta, kun nuna ba ku cancanci samun rai madawwami ba, to, za mu juya ga al’ummai. Domin haka Ubangiji ya umarce mu, ya ce, ‘Na sa ka haske ga al’ummai, Don ka zama sanadin ceto, har ya zuwa iyakar duniya.’” (A. M. 13:14, 45-47) Tun ƙarni na farko, sashen ƙungiyar Jehobah da ke duniya tana sanar da mutane game da wannan tanadi da Jehobah ya yi don mu sami ceto.

MUTANE DA YAWA SUN HALAKA, AMMA BAYIN ALLAH SUN TSIRA

14. Me ya faru da Urushalima a ƙarni na farko, amma su wane ne suka tsira?

14 Yawancin Yahudawa ba su karɓi bishara ba kuma sun halaka don Yesu ya ce wa mabiyansa: “Sa’anda kuka ga Urushalima tana kewaye da dāgar yaƙi, sa’annan ku sani rushewarta ta kusa. Sa’an nan waɗanda ke cikin Yahudiya su gudu zuwa duwatsu; waɗanda suke cikin tsakiyarta su fita waje; waɗanda ke cikin ƙauyuka kada su shigo ciki.” (Luk 21:20, 21) Abin da Yesu ya yi annabcinsa ya faru. Cestius Gallus ya ja-goranci wani Rundunan Romawa su kewaye Urushalima saboda wani tawaye da Yahudawa suka yi a shekara ta 66 a zamaninmu. Waɗannan rundunan suka janye ba zato ba tsammani. Sai mabiyan Yesu suka sami zarafin barin Urushalima da kuma Yahudiya. Wani ɗan tarihi mai suna Eusebius ya ce mabiyan Yesu da yawa sun tsere zuwa hayin Kogin Urdun a birnin Pella a ƙasar Perea. A shekara ta 70 a zamaninmu, rundunan Romawa da janar Titus ya ja-gora sun dawo kuma suka halaka Urushalima. Amma, Kiristoci masu aminci sun tsira don sun bi umurnin Yesu.

15. Me ya sa mutane da yawa suka zama Kiristoci?

15 Duk da cewa Kiristoci na ƙarni farko sun fuskanci wahala da tsanantawa da kuma wasu gwaje-gwaje, mutane da yawa sun ba da gaskiya kuma suka zama Kiristoci. (A. M. 11:19-21; 19:1, 19, 20) Me ya sa hakan ya faru? Don Allah yana tare da wannan ikilisiyar Kirista na ƙarni na farko.—Mis. 10:22.

16. Mene ne kowane Kirista yake bukatar yi don ya kasance da dangantaka mai kyau da Jehobah?

16 Kowane Kirista a lokacin ya yi ƙwazo don ya kasance da dangantaka mai kyau da Jehobah. Nazarin Littafi Mai Tsarki da halartan taro a kai a kai da kuma wa’azin Mulkin da ƙwazo sun kasance da muhimmanci. Irin waɗannan ayyukan sun ƙarfafa dangantakarsu da Jehobah, sun sa sun kasance da haɗin kai a lokacin kuma hakan ma yake a yau. Ikilisiyoyi suna da tsari kuma suna amfana daga ƙwazon dattawa da bayi masu hidima masu son taimaka wa ’yan’uwansu. (Filib. 1:1; 1 Bit. 5:1-4) Kuma suna jin daɗin dattawa masu kula masu ziyara da suke kamar Bulus sa’ad da ya ziyarci ikilisiyoyi! (A. M. 15:36, 40, 41) Muna farin ciki sosai sa’ad da muka yi tunanin yadda bautarmu a yau take kamar na Kiristoci na ƙarni na farko. Ƙari ga haka, muna godiya ga Jehobah a kan yadda ya tsara bayinsa a dā da kuma a yau!a

17. Mene ne za a tattauna a talifi na gaba?

17 Muna rayuwa ne a kwanaki na ƙarshe kuma nan ba da daɗewa ba, za a halaka zamanin Shaiɗan. Duk da haka, sashen ƙungiyar Jehobah da ke duniya yana ci gaba sosai fiye da dā. Shin kana yin biyayya ga abin da ƙungiyar Jehobah take faɗa kuwa don ka ƙarfafa dangantakarka da Allah? Talifi na gaba zai tattauna yadda za mu yi hakan.

a Ka duba talifofin nan: “Kiristoci Suna Bauta Cikin Ruhu Da Gaskiya” da kuma “Sun Ci Gaba Da Tafiya Cikin Gaskiya” da ke cikin Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Agusta 2002. Don ƙarin bayani game da sashen ƙungiyar Jehobah da ke duniya a yau, ka duba ƙasidar nan Su Wane Ne Suke Yin Nufin Jehobah a Yau?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba