Gabatarwa
Don Soma Nazarin Littafi Mai Tsarki a Asabar ta Farko a Watan Afrilu
“Mutane da yawa suna ganin Shaiɗan ne sanadiyyar mugunta a duniya. Amma sukan yi tunani: ‘Daga ina ne Iblis ya fito? Allah ne ya halicce shi?’ Mene ne ra’ayinka? [Ka bari ya ba da amsa.] Ka ji abin da nan ya faɗa.” Ka nuna masa talifin da ke bangon baya na Hasumiyar Tsaro na Maris-Afrilu 2013. Ku tattauna sakin layi na ɗaya da Nassin da aka rubuta a wurin. Ka ba mutumin mujallun, kuma ka gaya masa za ka dawo don ku tattauna tambaya da ke biye.
Hasumiyar Tsaro Maris-Afrilu
“Addinai da yawa sun gaskata cewa idan mutum ya mutu yana ci gaba da rayuwa a wani wuri. Kana ji za mu iya sake ganin ’yan’uwanmu da suka mutu kuwa? [Ka bari ya ba da amsa.] Ka lura da abin da Ɗan Allah ya faɗa da zai taimaka mana mu gaskata da begen tashin matattu. [Ka karanta Matta 22:31, 32.] Talifin da ke shafi na 7 a wannan mujallar ya bayyana wannan Nassin a hanyar da za ta taimaka mana mu kasance da bege.”
Awake! Afrilu
“Nuna zalunci a cikin iyali matsala ce da ta zama ruwan dare a duniya. Wasu sun ce al’ada da irin iyalin da mutum ya fito a ciki da kuma mugun nishaɗi ne sanadin hakan. Wane dalili ne ainihi kake ganin yana sa mutane su yi zalunci a cikin iyali? [Ka bari ya ba da amsa.] Littafi Mai Tsarki ya nuna irin dangantaka da ya kamata ya kasance tsakanin miji da matarsa. [Ka karanta Afisawa 5:33.] Wannan mujallar ta tattauna yadda bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki ya taimaka wa wasu iyalai su sake kasancewa da farin ciki.”