Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • km 1/12 p. 4
  • Gabatarwa

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Gabatarwa
  • Hidimarmu Ta Mulki—2012
  • Makamantan Littattafai
  • Gabatarwa
    Hidimarmu Ta Mulki—2013
  • Gabatarwa
    Hidimarmu Ta Mulki—2014
  • Abin da Za a Ce Game da Mujallun
    Hidimarmu Ta Mulki—2011
  • Gabatarwa
    Hidimarmu Ta Mulki—2011
Dubi Ƙari
Hidimarmu Ta Mulki—2012
km 1/12 p. 4

Gabatarwa

Don Soma Nazarin Littafi Mai Tsarki a Asabar ta Farko a Watan Fabrairu

“A waɗannan kwanaki na ƙarshe, kowannenmu yana fuskantar ƙalubale da ke sa iyalai alhini. Mene ne kake tsammani zai iya sa rayuwar iyalinmu ta kasance da farin ciki?” Ka bari ya ba da amsa. Sai ka ba mai-gidan Hasumiyar Tsaro ta Janairu-Maris, kuma ku tattauna batun da ke ƙarƙashin ƙaramin jigon da ke shafi na 10 da 11. Ka karanta aƙalla ɗaya cikin nassin da aka yi ƙaulinsa. Ka ba da mujallar, kuma ka shirya yadda za ka koma ziyara wurinsa don ku tattauna ɗaya cikin tambayoyin.

Hasumiyar Tsaro Janairu-Maris

“Babu shakka, za ka yarda cewa babu abin da aka ƙera a banza, amma kowanne yana da manufa. Ka taɓa tunani ko, ‘Mene ne Ma’anar Rai?’ [Ka bari ya ba da amsa.] Abin farin ciki ne cewa Allah bai bar mu a cikin duhu ba. [Karanta Mai-Wa’azi 12:13.] Wannan talifin ya bayyana abin da ya sa ya kamata mu yi rayuwar da ta jitu da wannan manufar da ya sa aka halicce mu da kuma yadda za mu amfana don yin hakan.” Ka gabatar da talifin da ke shafi na 28.

Awake! Fabrairu

“Mutane da yawa a yau suna more tattaunawa a dandalin yin hira na Intane. Kana tsammani cewa waɗannan hanyoyin sadarwa suna ɗauke da haɗarurruka? [Ka bari ya ba da amsa.] Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da ƙa’idodi da za su taimaka mana mu guji faɗawa cikin matsala sa’ad da muke amfani da wannan dandalin. [Ka buɗe shafuffuka na 6 zuwa 9, kuma ka tattauna ɗaya cikin tambayoyi da aka yi da kuma nassi guda da aka rubuta.] Wannan mujallar za ta taimaka maka ka san haɗarurrukan da ke cikin wannan dandalin da kuma yadda za ka guji faɗawa cikinsu.”

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba